HALIN GIRMA 19

Da k’yar ta taimaka mata ta fito ta shirya har lokacin kuka take, kaya kawai ta saka sai turare babu batun powder ko makeup. Lullube mata fuska Aunty Maimuna tayi suka fito, kai tsaye aka wuce da ita wajen Abba. Su uku ne a dakin daga shi sai Abba kabiru sai Abba (Babba) nasiha suka soma mata, me shiga ciki akan rayuwar da zata shiga sabuwa, yawanci magana daya ce hakuri wanda Zeenat din ta kasa fahimtar su, bata gane me suke cewa balle ta san a wanne mazauni zata ajiye maganganun nasu ba, har suka gama bata fuskanci komai ba, hankalin ta ma baki daya baya wajen su ta tafi tunanin kalar rayuwar da zata fara a gidan Bashir din. Sadakin ta Abba ya dauko a aljihun ta ya mik’a mata
“Gashi zeenatu,Allah ubangiji yayi miki albarka ya baku zaman lafiya.”
K’asa karba tayi, ta fashe da kukan da take ta rikewa, mikewa Abba yayi ya fice daga dakin zuciyar sa na tabuwa, yana jin kamar ya dawo da hannun agogo baya a lokaci da ya dinga nunawa Zeenat din illar abinda take shirin aikatawa.
Abba Kabiru ne ya karbi kudin a hannu Abba yace
“Barshi Yaya, bari wani cikin yaran nan sai yaje ya saka mata shi a account, idan yaso bayan komai ya lafa sai ta ciro tayi amfani da abinta.”
“Hakan ma yayi, shikenan zeenatu kudin ki za’a saka miki shi a account kinji? Ki daina kuka.”
Tashi tayi da k’yar tana gid’a kai kamar gadangaruwa ta fita, daga nan ne kuma kowa ya firfita dan zuwa kai ta gidan Ango Bashir. Sai dai duk mutane suka gama shiga mota sannan aka fito da ita aka sakata a mota, tana kuka Mama na yi haka aka tura ta a motar. Dangin Bashir din sukayi ta mamakin abinda yake faruwa dan kowa ya ga kukan yasan ba kawai na rabuwa bane akwai wani abu daban.
Shiru kake ji a motar babu motsin kowa kamar ba ma mutane a ciki. Wata Yayar su Abba ce da Aunty Maimuna suka sakata a tsakiya, hannun ta na damke ana Aunty Maimuna tana cigaba da kukan ta a ciki ciki. Har suka karaso bata daina kukan ba. Sauran jama’ar motar ne suka fiffito, kowa tayi cirko cirko suna jiran a nuna musu gidan Zeenat.
***Text message ne ya shigo wayar Bashir din, ya duba yana sauri sauri dan yana so yaga Moh kafin tafiyar da zai yi,
_”Ina jiran ka kaida kanwar tawa a gida, na saka an gyara muku daya daga cikin dakunan nan. Sai kunzo.” _
Gaban sa ne yayi mummunar faduwa, yayi sakale rik’e da wayar yana tunanin mafita, be shi da niyyar hada Zeenat da Hajiya Layuza gida daya, amma kuma be isa ya ki kai ta ba dan komai zai iya faruwa. Kiran ganin sa Ghali yayi ya tabbatar da sun karasa, yace idan kafa ta dauke ya kirashi ya sanar masa. Yana kashewa yayi mata reply da an gama hajjaju sannan ya saka wayar a aljihu ya fita yana sauri
Yadda dakunan suke kananu ya saka gidan ya chunkushe, kowa so yake yaga abinda zai samu na dorarwa a gaba, masu bud’e kitchen masu bud’e toilet har da masu bud’e rijiya dan tabbatar wa.
Aunty Maimuna ce tace kowa ya fita za’a koma gida saboda zuwa kai Iman, mutane suka hau saurin fita dan kowa ta kama motar da taxo amma suna fita suka ga wayam babu ko mota daya duk sun gudu,. Nan fa waje ya rude kowa ya hau tofa albarkacin bakin sa, yan uwan Mama suka shiga tashin hankali dan babu abinda yafi ciwo a debo mata a kawo su gidan amarya a watsar dasu, komawa cikin sukayi aka tilastawa Zeenat kiran Bashir din, be daga ba har aka gaji da kiran sa suka hakura suka fita, aka fara tunanin yadda za’a yi kowa ya koma gida.. saukin ta ma dama duk cikn garin ne dan tuni wasu ma sun dade da tafiya sun tari napep. Wanda suka rage ne dole su Aunty Maimuna suka san yadda sukayi kowa ta samu abin hawa. Sai yada habaici da bakar magana suke musamman yan uwan Abba da Mama ta bata wa rai tun a farkon fara bikin.
Sanda suka gama dawowa gida magriba ta kawo kai, a lokacin ne kuma motocin masarauta suke jere kansu a cikin layin wanda ya kasance tun daga farkon layin har karshen sa. Motar da za’a dau amarya daban take ta gaji da haduwa, anyi decorating dinta tayi kyau.
Gashi nan na biya bashin na ranar Friday.
#Rano????
*_ZAFAFA BIYAR 2022????_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*????????????
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*????????
09134848107
[ad_2]