HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 21-25

***Motoci ne guda uku suka dauke su zuwa airport din daga su Mamma
sai wasu yan uwan Abba su uku shikenan wanda zasu adamawar, shima saboda bikin
da zasuyi ne suma badan haka ba da babu me zuwa. a lokacin Moh sun dade da isa
suna zaune dasu Musaddik ana hira a wani kebantaccen wuri.

   Zuwan su da aka dan suka dauki hanya babu wani
bata lokaci. Ita kadai ce a wajenta, babu kowa a saman duk suna k’asa sai ita
kadai kwal har ta dinga tunanin dalilin da ya saka aka kawo ta nan din ba
abarta wajen su Mamma ba. Kamshin turaren sa ne ya amsa mata tunanin ta, ya
karaso ya zauna kusa da ita yana kashe mata ido. Kayan jikin sa ta kalla wanda
suka kasance na sarauta, sai takalmin kafarsa da akayi da fatar zaki yayi kyau
sosai shigar gidan sarauta, babu hula akan sa ya rik’e ta hannun sa, sumar sa
ta fulani ta sha gyara ya fito a bafulatanin sa sosai.

   Shi din ma shigar ta yake kallo, yana kuma yaba
yadda komai ta saka sai yaga ya karbe ta yayi dai-dai da ita.

 

“Ba magana?” Yace bayan ya gama kallon nata

 

Mirgina kanta tayi gefe tayi masa murmushi tace

 

“Sannu da zuwa toh.”

 

“Yawwa.”

 

Yace yana jingina da kujerar jirgin sosai, be sake magana ba sai
dai yanayin sa ya nuna mata kamar akwai damuwa, tasan yadda yake mata dan haka
yau din sai taga kamar bashi ba, bata sani ba ko sarautar ce ta motsa. Satar
kallon sa ta dinga yi sai taga ya kulle idon sa yayi kamar me bacci. Duk sai
taji ta takura ta kuma damu, taba shi tayi kad’an, ya motsa amma be bude idon
nasa ba, sai kamo hannun ta da yayi ya sakalo shi ta tsakanin nasa hannun ya
harde su waje daya, kusan rabin jikin ta ya sauka a nasa, bata sake attempting
komai ba har zuwa sanda suka iso jirgin ya sauka suka fito still hannun sa na
sarke da nasa.

 

 

  

***Kafarta a mike take tana sauraron bayanin da take mata, ko
motsi batayi ba, kamar bata jin me take cewa har ta kai karshen bayanin tayi
shiru tana kallon ta. Sai da ta dauki lokaci me tsawo kafin ta gyara zama, ta
bud’e hannun ta, ta mik’a mata shi, jikinta na rawa ta ciro kwalbar da take
nannade a gefen zanin ta, ta saka mata a cikin tafin hannun ta. Jujjuya shi
tayi tayi a hannun nata tamkar me son gano wani abu.

 

“Turare ne ranki ya dade, a jiki kawai ake shafa shi bayan
haka babu wani abu.”

 

“Kin tabbatar da abinda kika ce?”

 

“Allah ya taimake ki, yadda nayi miki bayanin haka yake,
yace kar ayi wasa dashi, sannan kuma kar ayi sakacin da za’a samu
matsala.”

 

“Rik’e.” Ta mika mata, da sauri ta karba tana damke wa
a hannun ta sosai.

 

” Kin tabbata babu wani abu da ya faru tsakanin su?”

 

” Na tabbatar, sai da ya nuna min komai kafin ya bani, yau
zasu iso sai kiyi kokari kafin su tare a sabon bangaren su dan naji rad’e
rad’in bikin ba zai dau kwanakin da aka tsara ba, bisa umarnin Sarki.”

 

Murmushi tayi me kyau, ta dawo ta zauna bayan ta ciro wata
karamar riga ta karata a jikin ta,sai kuma ta ajiye tana mikar da hannun ta
baya.

 

” Kinyi kokari, kina da kyauta me tsoka idan har na samu
biyan bukata.”

 

” An riga ma an samu gimbiya, ki kwantar da hankalin
ki.”

 

“Tukunna dai.”

 

” Me yayi saura? Yan awoyi ya rage miki ki samu abinda kike
so gimbiya ta.”

 

Jikin tagar dakin ta karasa, ta daga labulayen tana kallon
harabar gidan da yadda hadiman gidan ke kaiwa da komowa a tsakanin bangaren Moh
din da na Ammi, tasan duk shirin tarbar bakin ake, hankalin kowa ya riga ya
koma chan dan haka zatayi amfani da damar ta isa bangaren Moh ta yi zaman jiran
dawowar shi!

 

 

Rano💕

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

 

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*

_SO DA ZUCIYA_

 

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

 

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

 

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

 

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

 

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

 

*_Zaku tura kudin a_*

 

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

 

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

 

08184017082

 

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

 

09134848107

 

 

 

1/31/22, 19:14 – Buhainat: Halin Girma

      22

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

**********

Tamkar rana haka harabar masarautar take, komai an shirya shi an
tsara saboda shirin tarbar su. Tafiya sukayi doguwa a ciki kafin su kai wajen
manyan gine-ginen cikin masarautar.

   Ba mota daya suka shigo daga airport din dashi
ba, shiyasa ma bata ganshi ha a sanda suke fitowa daga mota. Cikin rakiyar
hadiman shashen Ammi da na gidan ma baki daya suka isa babban falon nata, da
aka kawata shi matuka ana jiran isowar su. Kamar yadda suka samu tarba ta
musamman a Kano haka aka karbe su anan dinma. Hakan ya kara bawa su Mamma
nutsuwa da tunanin irin yadda Iman din zata samu kanta a gida irin wannan wanda
yake cike da abubuwan da ba lallai ta iya dauka ba.

   Bayan sun huta an gabatar musu da abinci ne Ammi
ta saka aka rakasu masaukin su, wanda aka ware musu tun kafin isowar su. A
gajiya kowa yake dan haka suna zuwa kowa ya mike aka shiga maida maganar yadda
aka karbe su da irin sa’ar da Iman din tayi.

   Tana jin su bata tanka ba, hankalin ta ya tafi
sosai wajensa tana son jin yadda yake dan ta tabbata da akwai wani abu da ya
rage masa walwala.

 

***Tun isowar su ta samu labari wanda dama abinda take jira
kenan, ta shirya tsaf babu Kuma abinda zai hanata aiwatar da abinda tayi niyya
shiyasa ma bata bari Kilishi ta sani ba balle har ta hanata.

   Shigar sa shashen nasa bayan ya bar wajen Bubu
hadimar ta, ta sanar mata wanda dama ta saka ta ne ta saka ido tana ganin ya
shiga ta fad’a mata.

   Tashi tayi tana gyara gashin kanta da ta saka
ribbon din tayi sako-sako dashi, ta daura babbar Alkyabba akan kayan da suke
jikin ta da ya kasance karamar riga ce mara hannu iyakar ta guiwa kawai, sai
dogon wando a k’asan da ta saka saboda yadda zai zama ko ina na jikinta ya
rufe.

   Turaren da yake cikin Jakarta ta ciro, ta dunkule
shi a hannun ta, ta fita ta kofar bayan cikin rakiyar amintacciyar hadimar ta.
Tafiyar dake tsakanin bangaren Moh din da nasu da akwai tazara dan haka yasa
suka bi ta baya har suka isa. Idon ta, ta daga ta dubi bangaren bedroom dinsa
amma sai taga dakin babu haske sai sauran dakunan. Zagayo wa sukayi zuwa gaban
ginin masu kula da kofar suka tashi ganin ta, da ido sukayi magana da daya, ya
girgiza mata kai alamar eh sannan yace

 

“Yarima na jiranki gimbiya Lailah.”

 

Jin haka ya saka dayan saurin bud’e mata kofar, ta kutsa kanta
ciki kai tsaye tana jin kamar anyi an gama ta samu cikar burin ta.

   Tafiya ta ke a cikin falon tana kallon komai,
yadda aka sauya komai kamar ba part din da take shigowa a duk sanda ta ga dama
ba, babban hoton da ke manne a jikin bangon dakin ta kurawa ido tana matsawa
gaban sa. Iman ce a jiki, ita da Moh ranar da aka daura aure, sunyi masifar
kyau kamar kayi musu magana su amsa. Wani bakin ciki ne yazo ya tokare mata a
makoshi, taji kamar tayi wurgi da hoton ya tarwatse a wajen amma sai ta daure,
ta maida hannun ta baya tana nufar bedroom din nasa in da tasan zata same shi.

   Kafin ta karasa ta hango glass cup a k’asa a
farfashe, ta durkusa ta dauki ragowar tana kaiwa hancin ta, murmushi tayi tana
da yakinin komai ya zama daidai, everything is in order kamar yadda ta tsara.
Hakan ya saka ta wucewa Kai tsaye ta murda kofar dakin ta kutsa kanta ciki tana
zare alkyabbar da take jikin ta, ta zame a wajen ta fadi.

   Muryar sa da ta soma bacewa yayi kokarin cewa

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button