HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 21-25

“Waye!”

 

Yadda yayi maganar ya saka ta sake tabbatar da komai yayi
daidai, basu yi mata shirme ko shiririta ba. Karasawa tayi jikin gadon, ta kai
hannu ta taba shi ta hasken bedside lamp da ke kunne, take kallon sa, idon sa
yayi masifar komawa ciki yana lumshe su tamkar wanda yake shirin yin bacci irin
baccin da yafi karfin sa yake neman kai shi k’asa.

 

“Waye?” Ya sake maimaitawa da k’yar kansa da yake juya
masa ya shiga kai masa sakon mayen kamshin da yaji ya karad’e dakin,kamshin da
ya dauke shi zuwa wata duniya ta daban, a take yaji komai ya hargitse masa, ya
mike da k’yar yana duban ta cikin ido, gaba daya komai ya chanja masa,ta juye
masa Iman dinsa gaba daya. Hannu ya kai zai taba ta, ta saka karbi ta tura shi
baya ya fad’a saman gadon!

 

***Text message ne ya shigo wayar ta, ta bud’e da sauri tana
fatan ya kasance daga shi, kamar yadda tayi tsammani, shi din ne kuwa,

 

_”A rako ki shashe na.”_

 

Haka kawai sakon ya kunsa, kifa wayar tayi tunanin yadda zata
fara fadawa Mamma yace a rakota bangaren sa. Da kunya sosai bata kuma jin zata
iya,shiru tayi tana wassafa abun a ranta, zuciyar ta na ce mata kawai ta kira
mamma ta fad’a mata ai ba wani abu bane, wata zuciyar kuma na ce mata a ah. Ta
na nan zaune har aka dau tsahon wani lokaci, sakon ya sake shigowa irin na dazu
a karo na biyu, sai dai banbancin lokaci. Amaani ta kira suna zaune suna cin
snacks da juice, ta bata wayar tace ta kaiwa Mamma. Sai ta kifa kanta tana jin
nauyin Mamma. Tana jin sanda Mamman tazo kanta, tana sababi

 

“Yanzu haka ake gaya miki anayi Iman? Mijinki yana kiranki
tun dazu kika yi shiru. Kunyar me? Zamani ya chanja kinji? Tashi maza ki gyara
jikin ki, ga masu kula dake nan da yawa daya sai ta rakaki, tashi maza kina
kara bata lokaci.”

 

Tashi tayi kunya na nukurkusar ta,ta dinga sunne kai taki yarda
su hada ido da Mamman, tana kallon ta, ta fito mata da wasu kayan tace ta
sauya, sannan ta kawo mata wani abu a cup da madara ta bata ta shanye, ta
faffesa mata turarurruka masu kamshi sannan suka fito in da yan matan ke zaune,
da sauri suka tashi su biyu, suka sakata a tsakiya suka nufin bangaren Moh din
da yake da dan tazara da wanda aka sauke su.

   Babu kowa a kofar, kai tsaye ta shiga su kuma
suka samu waje daga wajen suna jiran ta dan tace musu ba jimawa zatayi ba, babu
kowa a falon babu motsin komai, dakin farko ta bud’e da sallamar ta, baya ciki,
sallama take amma ba da karfi sosai ba, a tunanin ta ko ya shiga toilet ta
zauna jiran shi, shiru shiru babu alamar sa, ta kasa kunne ko zata ji karar
ruwa a toilet sai taji kamar shesshekar kuka, sake kasa kunnen tayi sosai ta
tabbatar da abinda taji, sai ta fara tunanin aina take ji, dakin da yake
karshen falon ta kalla, babu alamun haske a ciki amma kuma tabbas da ga nan ne
sound din yake fitowa. Tashi tayi ta nufi dakin tana taraddadin abinda zata
tarar. A hankali ta tura kofar, ta leka da kanta kafin ta shiga da jikin ta
gaba daya, tana gama shiga wutar dakin ta kawo, kwakwalwarta ta dauke kamar
yadda ake dauke wutar nepa, idanun ta suka sauka akan Moh yayi ruf da ciki a
saman gado yana bacci cikin kwanciyar hankali, boxer ne kawai ajikin sa dgaa
shi babu komai. Da sauri ta maida kallon ta kan matar dake zaune a kasan tiles
din dakin, kanta babu dankwali gashin kan nata da ya hargitse ya barbazu har
zuwa saman fuskar ta, shigar jikin ta kawai ta kalla tayi saurin dauke kanta
tana kokarin barin dakin, sai dai bata kai ga barin wajen ba dan ko taku biyu
batayi ba, taji sanarwa shigowar Maimartaba, bayan sanarwa ne taji shigowar sa.

   Karuwar kukan Laila ya sake sakata cikin yanayin
da ta shiga, har Maimartaba ya karaso bakin dakin tana tsaye kamar an dasa ta,
bata san me zatayi ba. kallon ta yayi kafin ya maida kallon sa cikin dakin,
yayi musu kallo daya wani abu me dacin gaske yana tokare shi a goshi. Juyawa
yayi sai a lokacin kwakwalwarta ta kai mata sakon waye wanda ya shigo din, da
sauri ta zube a wajen ta gaishe shi cikin muryar ta da take rawa sosai.

   Be amsa mata ba, sai daga mata kai da yayi ya
juya ya fice yan rakiyar sa suka bi bayan sa cikin tunanin dalilin zuwan Bubun
shashen Moh.

    Kasa daga kafarta tayi daga wajen, ta jingina da
bangon dakin tana karanto duk addu’ar da tazo bakin ta, ji tayi kamar ana mata
magana, ta dago tana kallon cikin dakin

 

“Amarya! Kinyi farin gani ko?”

 

Me zata ce? Shiru tayi tana maida idonta ta rufe shi ruf tana
kokarin ajiye abinda ta gani din da kuma abinda zuciyar ta take haska mata waje
daya.

 

“Anya? Anya kuwa? Muhammad? Me ya faru? Me yake shirin
faruwa? Wacece wannan din?”

 

“Karki wahalar da kanki tunanin wacece ni, sunana Laila,
gimbiya Lailah.”

 

Yawu me karfi ta hadiye, ta hau kokarin daidaita kanta waje
daya, shigowa taji an sake yi, ta daga idonta da sauri wannan karon wata babbar
mata ce ta shigo a hargitse, tayi saurin yin kan wadda ta kira sunan ta da
Laila tana rik’e ta, tana kallon yadda Lailan ta cigaba da rusa kuka kamar
Allah ya Aiko ta, matar na bata baki jikin ta na rawa sosai. Daga ta tayi da
sauri, ta yafa mata mayafi ta rik’e hannun ta, suka zo daidai in da Iman din
take tsaye, matar tayi mata wani mugun kallo, ita kuma Laila tayi mata
murmushin da ta tsaya mata a rai. Fita sukayi tayi saurin zuwa ta sakawa kofar
key, ta dawo ta durkusa a k’asan falon ta shiga kuka, kukan da take ta kokarin
rikewa dan bata son su ga weakness dinta, dama chan ita mutum ce me taurin
zuciya da wuya kaga weakness dinta, shiyasa yanzun ma ta daure har suka fita.

   Sai da tayi kuka sosai sannan ta tashi ta share
hawayenta, a kalla zata so taji ta bakin shi, kar ta yi judging dinsa da abinda
ko a musulunci babu hujja, dan bata gansu suna aikata wani abu mara kyau ba.
Duk da ta na kokarin karfafa jikinta da zuciyar ta akan ta bari taji komai,
amma kuma jiki da zuciyar ta ta sunyi sanyi, sanyin da take jin kamar komai ya
kare mata, kasan zuciyar ta tana jin zafin sa, tana jin haushin sa amma kuma
bata da damar yanke masa hukunci.

   A yan awannin da tayi a cikin gidan nasu ta
fuskanci akwai wani Babban al’amari da ya shafi Moh dinta. Tana jin kamar gadar
zare aka hada masa har ma da ita. A nutse take duk da abin ya kadata, dan babu
matar da zata ga wata mace a dakin mijinta cikin yanayin da taga Laila ba tare
da taji komai ba, sai dai ta yarda da addu’a dan haka ta dage sosai har ta soma
jin nutsuwa na saukar mata.

   Bata san dadewar da tayi a wajen ba, taji kamar
motsi a dakin, ta tashi ta dubo cikin rashin sa’a ta cire takalmin ta, ta taka
glass din da yake fashe a wajen, kara tayi hakan ya farkar da Moh gaba daya, ya
mike da sauri kansa yayi wani irin sarawa da be taba jin irin sa ba, jiri yaji yana
neman kayar dashi yayi saurin komawa ya zauna yana dafe kan, bayan kamar sakan
goma ya mike a hankali ya fito.

   A durkushe ya ganta tana rik’e kafarta da har ta
fara jini, da sauri ya karaso ya durkusa a gabanta yana kama kafar

 

“Me ya same ki? Me kika taka.”

 

Kokarin janye kafarta tayi, ya sake kama kafar ya rik’e yana
kallon kafar cikin tausayawa.

 

“Cika min kafata.”

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button