HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 21-25

“Kin dai ji ko? Ko kuma address din gidan nasu zan
baki?”

 

“A ah.” Tace a sanyaye tana mikewa. Cigaba da aikin
gabansa yayi dan be ga dalilin da zai saka ta tada hankalin ta ba, bayan sun
riga sun aurawa Bashir din basu da ikon bibiyar in da duk zai kaita.

 

***Zuwa yamma masarautar ta cika sosai, duk wanda Ammi ta
gayyato sun hallara, yan mata ne kyawawa masu aji suka fi yawa sai manya
tsirari wanda Ammi ta barsu sai ranar nadin dan kar ya zama an takure mutum,
Ba’a dau lokaci aka shiga gabatar abinda ya tara su, saboda a ranar su Mamma
suke so su wuce. Tsarin daban ne da duk wani taro da akayi na bikin, Muhammad
da be niyyar attending ba, amma ganin abinda ya faru ya sakashi shiryawa cikin
shigar da yasan zai burge Iman dinshi, wanda be san iya adadin yan matan da
suka sake faller masa ba a ranar. Yana zaune kusa da ita daf ya dan karkace
yana fuskantar ta, yana mata magana k’asa-kasa, tana jin sa sarai amma ta fuske
dan ta gama gane shi so yake suyi abin da zata sha kunya dan taga kamar shi be
san kunya ba sam. Daga nesa ba zaka gane yanayin da suke ciki ba, zaka dauka
yanayin zaman nasa na mulki ne, sai ka matso sosai zaka gane kan abun. Shigar
da Laila tayi a wajen ta kusan fin ta Iman din, babu laifi Allah ya hore mata
kyau ba kad’an ba, dan sanda ta shigo wajen sai da gaban Iman ya fadi ganin
uwar kwalliyar da taci kamar wata dawisu, kai tsaye wajensu ta nufo tana tafiya
tana karkada kowanne lungu da sako na jikin ta, kamar bishiyar da iskar rani ke
kadawa haka ta dinga karkada jikin ta har ta karaso wajen fuskar ta a washe ta
matsa daidai saitin Capt Muhammad ta rankwafo tana nunawa camera man sign din
ya dauke su.

  Da ido Muhammad yayi masa alamar idan ya dauki hoton sai
dai wani bashi ba, sum-sum ya bar wajen hakan ya bata wa Laila rai tace

 

“Capt wanne irin wulakanci ne wannan?”

 

“Baby kinga waccar da ta shigo yanzu?” Yayi kamar be
ji ba, ya matsa jikin Iman din yana nuna mata wata,

 

“Kanwar Ammi ce, itace Aunty Fatima.”

 

“Ok wadda ka bani labarin ta ko!?”

 

“Yea ita.”

 

“Allah sarki, she’s nice.”

 

“Sosai.” Sai ya sake kai fuskar sa jikin ta sosai

 

“Baby perf din nan akwai kamshi, i just love it, yayi
dadi.”

 

“Thanks dear.” Tace tana smiling

 

Bakin ciki ne ya tuke Laila, tayi saurin barin wajen kafin
zuciyar ta, ta buga. Tana barin wajen sukayi wa juna murmushi.

 

A gajiye suka koma cikin gidan bayan an gama taron, su Mamma sun
jima da tafiya dan haka part din Ammi aka maida ita, daga nan Ammi ta saka
mutane da yawa suka yi mata rakiya zuwa nata part din da ta riga ta tare tun a
jiya ba tare da Ammin ta sani ba, sai gobe za’a rakata wajen Bubu idan ta huta
shi ma baya nan yau sai goben zai dawo.

   Masu kula da bangaren da duk wani abu da ya shafe
ta Ammi ta nuna mata, suna isa kuwa suka shigar da kayan su dakunan su dake
bayan part din suka shigo suka fara aikin gyara shashen, suka gama suka saka
masa turaren wuta sannan aka jere musu abinciccika masu rai da lafiya. Sai da
suka tabbatar babu wani abu da zata bukata sannan sukayi mata sallama suka
tafi.

   A gajiye take sosai amma kuma dole tayi wanka dan
sosai Mamma ta jaddada mata muhimmanci wanka da gyara jiki, cire kayan jikin ta
tayi, ta zari towel daya ta daura ta nufi toilet din, wanka tayi ta hado da
alwala ta fito tana sharce kanta. Wayarta ce tayi kara ta dauka tana dubawa,
Mommy ce ke kiranta, tunda aka fara bikin basuyi magana ba, sai dai ta jisu da
Mamma suna yi, zama tayi tana daga wayar dadi na cikata

 

“Mummy barka da dare.”

 

“Iman… Kuna lafiya?”

 

“Lafiya lou mummy, dama yanzu nake so nazo na kira.”

 

“Ko? Toh gashi na kira ni ai, ya sabon waje?”

 

“Alhamdulillah.”

 

“Mamma ta sanar dani duk yadda abubuwan suka kasance, nasan
kuma duk abinda ya kamata ki sani ta sanar dake, dan haka ita rayuwar aure yar
hakuri ce, sannan duba da irin gidan da kika samu kanki, sai kinyi hakuri kin
kuma zama me lura sosai.”

 

“In Sha Allah mummy.”

 

“Yawwa, ki kula sosai da mijinki da duk abinda kika san
yana so, karki ga tarin ma’aikata ki sakar musu kula da mijinki, duk wani abu
da ya danganci mijinki ki taske kiyi shine hanyar samun ladan ki, kuma hanyar
aljannar ki.”

 

” In Sha Allah Mummy, nagode sosai.”

 

“Ki ajiye kunya ki kula da mijinki sosai, banda sanyin jiki
da lalaci.”

 

A kunyace tace

 

“Toh mummy.”

 

Turo kofar akayi, yana sanye da 3quarter wando babu riga a jikin
sa, saurin dauke kanta tayi tana amsawa mummy bayanin da tayi mata akan wasu
magunguna da ta saka mata a bag dinta. Gabanta yazo ya tsaya k’yam yana karewa
cinyoyin ta dake bayyane saboda kankantar towel din. Tsugunawa yayi a gabanta
ya saka hannu ya shafa saman cinyar ta ta, tayi saurin janye su tana jan
numfashi,

 

“Kina ji na Iman?” Mummy tace jin kamar attention
dinta ya tafi wani wajen.

 

“Am.. am ina ji Mummy.”

 

Ta amsa a firgice ganin ya kai hannu jikin towel din ya janye,
da sauri ta saki wayar bayan ta danne power button din, ta mike tana rik’e
towel din. Idonsa a shanye yake kallon ta

 

“Zanyi wanka.”

 

Yace yana shigar da idonsa cikin nata, kasa matsawa tayi daga
wajen, sai jan towel din take a dole sai ya sauka ya rufe bayanta. Bata taba
jawowa zai shigo a lokacin ba, ta yi tunanin ma ya tafi, sai ganin shi tayi.
Dariya ta bashi,yadda ta hakikance a dole sai ta saukar da towel din.

 

“Zanyi wanka.” Ya sake maimaitawa yana folding hannun
sa, kamar ta dora hannu a ka tayi ta kurma ihu ta shiga takawa zuwa toilet din
tana cigaba da jan towel din. Ji tayi an rungume ta, ta baya ya dora kansa a
saman kafadarta.

 

“Me kunya, kunyar me kike ji?”

 

“Ba komai.”

 

“Shine kike ta jan towel din bayan halal dina ne, sai a
barni na more kallon kayana ko?”

 

“Uhum”.

 

” Emana. ” Ya sake tura kansa wuyan nata sosai,yana
jujjuya kan, hakan ya haifar mata da kasala, ta dinga kokarin zamewa amma ya
hanata, a dole ta kyaleshi yayi budurin sa. Sai da ya tabbatar da tayi laushi
sosai sannan ya jata zuwa toilet din. Mamakin rashin kunyar sa take, shi ko a
jikin sa babu abinda ya dame shi, ita kuwa kamar ta shide idan ta kalleshi a
hakan sa, da k’yar ta samu ya barta bayan ya kara tattabe ta, ta samu ta fito
ta barshi a ciki, a gurguje ta shirya ta saka kaya ta tada sallah ko da ya fito
tana sallah sai kawai ya shirya shima ya fita falo dan cikin sa ya fara kiran
yunwa. Zaman jiranta ya dinga yi jin shiru bata fito ba ya leko ya kirata, dan
baya so a kara kwana be bata labarin komai ba, a kalla hakan zai saka ta sake
yarda dashi ta kuma taimaka masa dan ita kadai ce ta fara ganin Laila sanda ta
shigo part din. Tsattsakurar abincin tayi tace ta goshi dan da gaske tsoro take
ji, tsoron kar yace zai sake yi mata irin abinda yayi mata jiya, ba zata iya
dauka ba, shiyasa tana gama ci ta sulale ta gudu ta kwanta ta kudundune a dole
tayi bacci. Sai da ya gama komai sannan ya biyo ta dakin ya yaye abinda ta
rufan yana shigewa jikinta.

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button