HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 21-25

Tace ba tare da tasan me yasa ba, kawai ganin sa ya sakata jin
haushin sa. Kin cika mata kafar yayi, sai ma daukar ta da yayi gaba daya duk da
yadda yake jin sa babu kwari, ya ajiye a gefen gadon ya dauko first aid box din
sa yazo ya durkusa a gabanta ya gyara mata kafar Allah ya taimaka kwalbar bata
shige ba.

 

“Yaushe kika zo nan? Ya akayi nayi bacci? Me ya faru aina
aka samu kwalba a wajen nan har kika taka? Ina masu kula da wajen?”

 

Ya jero mata tambayoyin cikin son tuna wani abu, da Ido kawai
yake bin sa kamar me son karantar sa, sai dai bata ga komai ba sai tsantar
gaskiyar sa a yadda yake maganar. Janye kafarta tayi ta mikar da ita a saman
gadon, ya dawo ssman gadon ya zauna yana jan kafar ya dora akan cinyar sa.

 

“Bacci ne ya dauke ni bayan na sha juice daga nan kuma
bansan me ya faru ba, kin dade kina jirana? Da baki tashe ni ba?”

 

“Bana so na katse maka barci ne.” Tace ganin duk ya
damu, ajiyar zuciya ya sauke yana matsowa ya gyara mata kafar yadda zata ji
dadi, ya mannu a jikinta.

 

” Kiyi hakuri, kaina ne naji yana min ciwo sosai shine
kawai nazo na dan huta bansan zanyi bacci ba.”

 

” Ba komai.”

 

Tace tana rufe idon ta

 

” Bacci?”

 

” Umm.”

 

Tace a gajarce dan bata son doguwar magana tana son tattara
bayanan da ta samu ta hade su waje daya kafin wayewar gari.

 

Tashi yayi ya fita bayan ya maida rigar sa,  ya hau k’wala
kiran ma’aikatan wajen, da sauri ya shigo yana raba ido, masifa ya fara yi masa
akan dalilin barin kwalba a hanya, hakuri yayi ta bashi yayi saurin gyara wajen
sannan ya fita.

   Ji yayi duk jikin sa yana masa ciwo, chan k’asan
zuciyar sa kuma wani irin feeling ne da be san dalili ba, ji yake kamar idan
har be samu abinda yake so ba zai iya rasa ransa, yana wanka yana tunani har ya
kammala ya fito daure da towel iya ka guiwar sa, kallon in da take kwance yayi,
ta dunkule waje daya kamar me jin sanyi.

   Kaya ya saka sannan yayi sallah ya duba wayar sa
yaga misscalls da yawa, ganin dare yayi ya saka shi ajiye wayar ya hawo gadon
yana juyo da ita tana kallon shi. Hawaye ya gani a saman kuncin ta, ya saka
hannu cikin mamaki yace

 

“Kuka?”

 

Kamar wadda take jiran kiris ta shiga rera shi sai dai babu
sauti, rikicewa yayi ya hau tambayar ta menene, bata amsa masa ba, ta cigaba da
kukan ta wanda ita kanta bata san me yake sake tunzura ta take kukan ba, da
farko ta zata zata iya daurewa sai daga baya ta gane duk dauriyar ta wannan ya
wuce in da take tunani, kishin mijinta ne ya sakata kuka. Magiya ya cigaba da
yi mata akan ta fad’a masa dalilin kukan ta amma taki, rungume ta yayi a
jikinsa yana lallashin ta amma kamar kara ingizata yake, ya rasa yadda zai, ga
wani irin abu da yake jin yana taso masa. Kasa daurewa yayi ya hade bakin su
waje daya, da karfi tayi kokarin turashi ta amma ta kasa!

 

 

 

Rano💕

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

 

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*

_SO DA ZUCIYA_

 

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

 

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

 

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

 

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

 

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

 

*_Zaku tura kudin a_*

 

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

 

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

 

08184017082

 

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

 

09134848107

 

 

1/31/22, 19:15 – Buhainat: Halin Girma

      23

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

*******

A hankali ya shiga bin ko ina na jikinta yana aika mata da
sakonnin shi, kukan da take na taba shi, yana jin har cikin kansa, sai dai ba
zai iya controlling kansa ba, abinda yake ji yafi karfin ikon sa, ba kuma zai
iya tsere masa ba.

   Da fari ta dauka babu wani abu da zai mata sai
son ganin ya rarrashe ta, amma daga baya sai taga abin yana chanja salo.
Jikinta ne ya hau rawa ta ko ina, ta sauya akalar kukan nata zuwa magiya da
rokon sa, baya jin ta, idan ma yaji ta baya tunanin zai iya yi mata abinda take
so din.

   Juyo ta yayi ta zama a saman sa, ya sake hautsina
ta zuwa kasansa , ya ajiye mata dukkan karfin sa, ji tayi kamar numfashin ta na
janye wa daga jikin ta, ta dinga jansa tana kuka tana kiran sunan sa, yadda
yake kissing dinta kamar mayaunwacin zaki ya sake tsorata ta,shi kansa jikin sa
rawa yake,ga wani karfi da yake ji ya zo masa wanda be taba jin irin shi ba.
Kayan jikin ta ya shiga janyewa yana wurgi dasu ta kowanne angle, har yayi
nasarar rabata da komai. Idanun sa da suka rine sosai ya zuba mata yana kallon
ta, wani abu yana kaiwa da komowa a tsakanin wuyansa.

 

“I’m so sorry.”

 

Ya furta mata da k’yar kafin ya shiga aiwatar da abinda yayi niyya.

 

   Sama sama yake jin ta, cikin muryar da ta shige
ciki saboda kukan da ta sha,  kamar mafarki haka yake jin abun, juyowa
yayi da k’yar ya dune ta, tana kwance agefen sa taci kuka har ta gode Allah.

 

“Subhanallah!”

 

Ya furta yana tashi, abinda ya faru ya shiga dawo masa akai, ya
akayi haka? Bayan yayi ma kansa alkawarin zama so gentle, yadda yasan ba zai
bata wahala sosai ba, what has gotten in to him? Me yayi mata?

  Rik’e ta yayi yana kokarin daidaita kansa ya samu damar
kwantar mata da hankali

 

“I’m so sorry dan Allah, dan Allah kiyi hakuri ki yafe min,
bansan me ya hau kai na ba, this is not me, bani bane ba.”

 

Bata da karfin da zata kwaci kanta, sai kawai ta lafe a jikin sa
tana jan numfashi. Kanta ya dinga shafawa a hankali a hankali, yana jin wani
irin son ta, na saka shigar sa. Idan har abinda kwakwalwar sa ta dawo mata
dashi gaskiya ne, toh lallai sai yaci uban Lailah, dole ne yayi mata abinda ko
a hanya ta hadu dashi ba zata nuna ta sanshi ba.

  Idonsa a rufe yana tariyo abinda ya faru, tabbas ya
ganta a tsaye a kansa, lokacin da baccin da be san na menene ba dauke shi da
sauri. Tunanin sa ne ya koma baya, zuwa sanda ya shigo ya tarar da juice akan
table din da ake ajiye masa, a gajiya yace amma ya tsaya ya sha daga nan ne ya
fara jin wani abu me karfin gask yana taso masa, sai wani irin bacci me nauyi
da be taba jin irin sa ba.

 

“Desire pills?”

 

Ya furta yana kokarin tashi, k’ara tayi mara sauti ya tuna tana
jikin shi, yayi saurin komawa ya zauna yana sake gyara ta.

 

” I’m sorry.”

 

Ya saka hannu ya goge mata hawayen da suke sauka a fuskar ta.
Tsawon minti talatin yana a haka yana tunanin abubuwan da suka faru a daren,
tabbas koma menene an shirya masa abu ne, be san ya akayi ya bada kafa ba, har
aka yi galaba akansa. Tashi yayi bayan ya gyara mata kwanciya, ya shiga toilet
ya gyara jikin sa, sannan ya fito, ya taimaka mata, ta tashi tana ciccijewa sai
dai taki yarda su hada ido, ta hade fuska sosai a dole haushin sa take ji,
haushi biyu ne suka hadu waje daya, ta kasa manta abinda ya faru farko da na
karshen.

  Toilet din ta shiga sai taga ya biyo ta, ta dube shi
tana tsaye gaban bathtub din, ta marairaice fuska, yi yayi kamar be ganta ba,
ya rufe kofar ya karaso ya durkusa yana taba ruwan.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button