HALIN GIRMA 21-25

“Ka fita.”
Ta fad’a muryar ta babu karfi, banza yayi kamar be ji ta ba, ya
ciro towel a cikin jerin sabbin towels din dake jere a cikin wata drawer,
sannan ya dauko brush da toothpaste ya saka mata a jiki ya ajiye a gefe ya hau
nannade hannun rigar sa. Kamar ta rusa ihu haka taji, ta rasa yadda zatayi ta
hanashi, bata ga alamar ma zai hanun ba, sai kawai ta hakura ta zubawa sarautar
Allah ido, bata san rashin kunyar namiji ta kai haka ba. Sai da ya gama abinda
yayi niyya ya tabbatar yayi mata yadda zata ji dadin jikin ta sannan ya
kyale ta ya fito yana jawo mata kofar.
  Kwanciya ta sake yi a cikin tub din ruwan na
ratsa ta, gefe tana tuna abinda ya wakana tsakanin su. Murmushi tayi, duk
kalaman sa na dawo mata daki daki, abu daya ne ya tsaya mata har take kokarin
alakanta shi da abinda ya faru kafin nan, idan har shi din ba mutumin kirki
bane, idan har wani abu ya faru tsakanin sa da Lailah, ba zai sha wahala wajen
neman hanya ba.
  Saurin kawar da tunanin tayi kunyar kanta na
kamata kamar yana wajen, da wanne idon zata koma wajensu Mamma ma wai tukunna,
da wanne idon? Kwankwasa mata kofar yayi ganin ta dade, sai ta tashi tana
karfafa jikin ta, ta dauro towel din bayan ta goge jikinta ta fito kanta a
k’asa. Ajiyar zuciya taji ya sauke bayan ya kare mata kallo, hankalin sa yaki
kwanciya tunanin sa ko yayi mata illa ne, sai yaga akasin haka, be sani ba ko
duk cikin dauriyar da ya gane tana da ita bane. Lokacin sallah ake kira a cikin
masallacin cikin Masarautar, daga jikin kofar ya tsaya be fita ba, yana kallon
ta har ta gama ta saka doguwar jallabiyar sa daya ajiye mata a gefen gadon,
murmushi yayi ya fice kansa sanye da farar hula da ake kira da tashi ka fiya
naci ya dora doguwar riga irin wadda ya dauko mata.
  A sahun farko ya samu Kamal, daga liman sai shi,
hakan ya bashi mamaki amma ya share, bayan an idar suka gaisa a tsattsaye ya
fice yana son komawa ya ga halin da take ciki. Sun hadu da Bubu amma be masa
magana ba, ya dai ce masa ya sameshi idan garin ya gama wayewa, sai dai yanayin
fuskar Bubun ta saka shi tunanin akwai wani abu me girma.
  A saman sallayar ya tarar da ita, ta kwanta akan
hannun ta ta mik’ar dashi, karasawa yayi ya daga ta, ya maida ta saman gadon
yana zama a gefen ta. Rufe idon ta tayi da sauri jin ya matso da fuskar sa
daidai saitin tata. Iska ya fitar me zafi, ya tashi ya kashe wutar dakin ta
dawo ya hawo gadon ya kwanta.
“Me ya faru?”
Yayi mata tambayar kai tsaye, yadda yayi sounding zaka gane daga
muryar sa, maganar yake so suyi, shiru tayi bata ce komai ba, dan bata san me zata
ce ba, tace masa ta same shi da wata a daki ko me? Ta yaya ma zata fara?
“A lokacin da kika zo dakin part din nan, wani ya shigo? Ko
kinga wani a ciki?”
Nan din ma shiru ta sake yi masa, kasan zuciyar ta na ce mata
kar ta yarda,kawai zai yi amfani da innocent dinta ne ya nuna mata kamar be san
komai, daga gefe kuma wata zuciyar na ce mata ta fad’a masa watakila be sani
ba, watakila so ake a hada su, tunda har yanxu bata san komai akan sa ba, ba
zata iya dorar da wani abu ba balle har ta iya judging dinsa, kawai dai a
matsayin ta na mutum me tunani , tana kyautata masa zato.
  Birkitota yayi da karfi muryar sa na fita da dan
karfi akan dazu yace
“Tell me, me ya faru? Wani abu ya faru? Kin samu wata ko
wani da kika zo? Wani ya fad’a miki wani abu ne? Me ya faru!”
Kuka ta samu kanta da fashewa da, ya tashi da sauri yana kunna
wutar dakin, ya dawo ya tashe ta zaune suna fuskantar juna, zuwa lokacin ya ji
yana neman loosing temper dinshi.
“Kalle ni, look at me! Menene? Me ya faru da ban sanshi ba?
Tell me, waye yazo?
” Maimartaba ne yazo.”
” Maimartaba!?” Ya furta da dan karfi cikin yanayin
dake nuna tsantsar mamakin sa
“Me yazo yi a part dina? Me yace? Me ya faru? Wani abu ne
ya faru while i’m sleeping?”
” Eh.” Ta daga masa kai, tsugunawa yayi a wajen yana
tattaro dukkan nutsuwar sa, gabansa na faduwa da abinda zata ce dan yasan ba
karamin abu bane zai kawo Bubu part din sa.
” Believe me, bansan komai ba, kamar yadda babu alkalami
akan me bacci, na rantse miki bansan me ya faru ba.”
Goge fuskar ta, tayi da hancin ta a jikin sa, ta dago tana
kallon kasa tace
” Naga wata Laila a nan.”
Ta nuna wajen da Lailan ta zauna
” Lailah!? “
“Eh.”
“Ehen, sai me?”
“Tana zaune a wajen tana kuka sosai, daga nan sai Maimartaba
ya shigo, sannan ya tafi sai kuma wata mata ta shigo ta daga ta suka fita
  Abu ya hadiye me karfi, ya yi kokarin ganin be yi
wani abu ba, a hankali yaji kamar ana masa rad’a
_Be calm Moh, be calm.”_
Kamar wanda aka saka abu aka bubbuge ma guiwa haka ya zube a
wajen, zai tolerating komai amma banda fushin Bubu, shi za’a wa wannan kazafin?
Abinda be taba tunani ko shaawar aikatawa ba, Zina? Shi Muhammad shi aka yiwa
wannan sharrin? Saboda yayi kamar be san wani abu yana faruwa ba, shine har aka
samu damar yi masa wannan kullin?
 Tana ankare da yadda ya shiga kaduwa, tana kuma ganin
yadda Adam apple dinsa ke hawa da sauka tsakanin makogwaron sa, idon sa kadai
zaka kalla ka tabbatar da ransa yayi masifar baci.
  Sai da yayi kusan minti goma be ce komai ba, ba
dan bashi da abinda zai ce din ba, sai dan yadda mamakin Iman din ya hanashi
komai, be zaci haka daga gareta ba, idan wata ce, ba zata iya daukar abinda ta
gani ba, har ta tsaya jiran shi, ya ga kokarin ta sosai kuma ya jinjina mata, hakan
ya kara mata matsayi a zuciyar sa.
 Girgiza mata kai yayi yana kama hannun ta
“Kin yarda dani?”
” I don’t know.” Tace tsakanin ta da Allah
“Bansan yadda zan dauki abun na ajiye ba, all I know shine
I’m hurt, more than yadda nayi tunanin I ll be.”
Folding hannun nata yayi a cikin nasa ya damke.
“I promise to make everything right, koma menene we will
over come it, in sha Allah, together we will build tomorrow, I promise you
that!”
Shiru sukayi babu wanda ya sake magana, ko be ce ba, ko be ba
ita zata gano komai, zata gane kafin ma ya gane, tana da kaifin tunani, sannan
tana karantar komai kafin tayi judging din mutum.
  Kwanciya tayi ganin suna zaune kowa da abinda
yake tunani, ganin ta kwanta sai ya mike ya fita, ya nufi part din Ammi duk da
lokacin garin ke karasa yin haske. Ya san tana zaune har lokacin tana azkar
kamar yadda ta saba a ko da yaushe.
  Yadda ta ganshi ya shigo jikin ta, ya bata babu
lafiya, katse abinda take tayi ta mike tana kallon sa har ya karaso
“Lafiya Babana?”
“Ina kwana Ammi?” Ya duk’a k’asa ya gaishe ta, kafin
ya amsa mata tambayar ta
“Ba lafiya ba Ammi, yarinyar nan Laila tayi abinda zan nuna
mata ko ni waye, ganin kamar ban san me take ba ya bata damar aikata abinda ta
aikata wanda zai zame mata dana sani, dama chan Ammi kece kike hanani, saboda
zumunci amma not anymore.”
“Me ya faru?!”
“Bubu be sanar dake komai ba?”
“Be ba, me ya faru?”
Iyakar abinda ya sani ya sanar da ita, jikinta yayi sanyi, ta
kuma san Bubu zai iya daukar kowanne mataki akan muhammad din, tun da be taba
sanin wani abu daya danganci Laila din ba da shi, ita kawai da Muhamamd din ne
suka sani sai Kilishi.