HALIN GIRMA 21-25

“Babu abinda zai faru, kai dai ka rike gaskiya, zatayi
halin ta.”
“Shikenan, zanje naga Bubu, zanji me zaice.”
“Allah ya taimaka, zanyi magana dashi nima in sha
Allah.”
Fita yayi ita kuma ta zauna a wajen tana hango abinda zai je ya
dawo.
Kasancewar safiya ce, shiyasa ya shige kai tsaye wajen Bubun, a
lokacin ya fito wajen shashen bayan sallah yana duba wasu littattafan sa. Sai
dai yau ya kasa yin komai, tunda aka fito masa da littafan ya kasa taba ko guda
daya, balle har ya karanta, abinda ya gani jiya yayi masifar girgiza shi, ya
kada shi sosai, har yayi furucin da yake jin idan har Muhammad be wanke kansa a
tsawon kwanaki biyar ba, ko da yana da gaskiya ya zama dole ya auri Lailah tun
kafin maganar ta fito waje, a jita a ko ina.
  Aji ya samu da maganar a lokacin dan ji yayi
yana neman faduwa k’asa, sai dai yadda yayi tunanin maganar zata taba Aji sai
yaga akasin haka, yana zaune kem fuskar sa bata chanja ba ko kad’an, har sai da
Bubun ya kasa daurewa ya tambayi Aji dalilin da be ji abun ba, murmushi yayi
yace.
“Ahmadu kenan, da Muhammad da Laila su dukkan su nawa ne,
ni na haifi iyayensu na kuma san kowa a cikin su, na san abinda kowa zai aikata
da wanda ba zai aikata ba, duk da yanzu ance baa shaidar mutum, amma ni zan
shaidi Muhamamd ko aina ne, lallai akwai wani al’amari bayan abinda kai din ka
gani.”
“Amma kuma komai ya nuna, a yadda na ganshi naga Lailan,
bani da hujjar kare shi ko yarda dashi, idan har nayi haka sai naga kamar banyi
wa Yaya adalci ba, mutane zasu ce ko dan babu shi. “
” Duk abinda zakayi karka tuna mutane dan dama su baa raba
su da abin fad’a, kayi gaskiya kawai. “
” Toh ta yaya zan yarda da Muhamamd be aikata ba? Da wacce
hujja zan yarda dashi? “
” Ka bashi lokaci, ya kare kansa, idan har ya amsa laifin
sa shikenan, idan kuma ya kawo hujja gamsasshiya toh.”
” Idan har muhammad ya kasa kawo hujjar bai aikata abinda
ni da mahaifiyar Laila muke tunanin ya aikata ba, nayi alkawarin aura masa ita
a tsakanin kwanaki hudu! “
 Dawowa yayi daga tunanin yadda suka kwashe da Aji yayi,
ya bata rai sosai sanda Moh ya dire a gabansa, cikin girmamawa ya gaishe shi,
amma sai yaki amsawa, ya kausasa murya yace
” Ban kiraka nan dan ka gaishe ni na amsa ba, ban kuma
kiraka nan dan muyi doguwar magana ba, me ya faru tsakanin ka da Lailah? “
” Babu komai Bubu. ” Yace kai tsaye dan dama ya riga
ya shiryawa tambayar
” Babu komai? “
” Eh babu, duk abinda ka gani sharri ne, bansan komai akai
ba. “
” Waye shaidar ka? ”
” ALLAH! ”
Ya fad’a kai tsaye, shiru Bubu yayi, ya dauki wani lokaci kafin
yace
” Ka dauki alaka ta da kai ta d’a da mahaifi ka ajiye a
gefe, ka kalle ni a matsayin alkali da aka kawo min kara ka, na baka nan da
kwana hudu ka kawo min kwakkwarar hujja, idan har kwana hudu ya wuce babu
komai, nayi maka alkawarin aura maka Laila! “
” Aure?!!! “
” Aure, tashi ka bani waje.”
Jikin sa a sanyaye ya tashi, ya fice cikin sauri sauri ya nufi
part din Lailan, yana tafiya yana huci, ji yake kamar ya dauko bindiga ya harbe
ta, mutanen da suka fara fitowa wanda suka kasance masu aikace aikace a
tsakanin parts din suka hau mamakin ganin Moh a irin lokacin shi kadai babu
wani tare dashi. Be same ta a bangaren nata ba, tana bangaren Kilishi,juyawa
yayi zuwa bangaren Kilishi yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai yi musu.
   Sai da ya kusa zuwa sai kuma zuciyar sa
tace yaje yayi musu me? Yafi karfin haka, ba girman sa bane, dan haka sai kawai
ya koma nasa part din yana lissafin kwanaki hudun da Bubu yace, yasan zai iya
yin komai ba kuma sai karya alkawarin sa ba, idan kwanakin suka cika bashi da
wata hujja. Abu na karshe da zai iya shine auren Lailah, gwara ya hakura da
komai akan ya aure ta.
  Bacci ya sameta tanayi, baccin da yasan na
wahala ne, duk tausayin ta ya kamashi, shi da yaso ta huta sosai kafin ta fara
sanin komai amma sai gashi daga shigowar ta gidan ta fara da karo da abinda
yafi komai muni. Peacefully take baccin,fiye da wanda tayi jiya, a kalla yanzu
ta samu kwanciyar hankali bayan ta sanar masa da abinda yake damun ta, yasan
tayi dauriya sosai.
  Kissing goshin ta yayi, ya gyara mata kwanciyar
ya koma dayan side din ya kwanta da tunanin kwana hudu
Rano
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/1/22, 10:25 – Buhainat: Halin Girma
   24
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
Sai da rana ta daga sosai sannan ta farka, da sauri ta mike tana
mamakin dadewar da tayi tana bacci ita da ya kamata ta koma wajen su Mamma.
Sakkowa tayi tana jin jikin ta da dama-dama, ta shiga takawa a hankali zuwa
toilet din dakin,ta wanko fuskar ta, ta fito ta gyarata sannan ta cire
jallabiyar tasa ta maida kayan ta, ta ajiye masa a gefen gadon ta fito zuwa
falon. Tunanin yadda zata iya komawa wajen su Mamma take da kuma yadda zatayi
da kunyar da take ji daga zuwa ta dawo sai kwana bayan ba haka ya kamata ba a
ganinta. Abin takaicin ma bata dauko wayar ta ba balle ta kira, tana tsaye tana
tunanin yadda zata fita taji maganganu a kofar part din,wajen window ta isa, ta
daga curtains din tana son ganin komai. Gabanta ne ya fadi, tayi saurin cika
window din a daidai lokacin da taji suna karasa maganar su. Kyakkyawa ce ajin
farko, kana ganin ta kaga bafulatanar adamawa, yau ba kamar jiya da ta soma
ganin ta ba, tana cikin shiga me kyau harda Alkyabba, tayi kyau fuskar ta fes
alamun tana cikin farin ciki. Kokarin daidaita kanta tayi sanda taji an turo
kofar an shigo, idonsu ya hadu lokaci daya, wani banzan kallo Lailan ta watsa
mata tana karaso wa ciki a gadarance, ta samu saman daya daga cikin kujerun
falon ta hakimce baiwar ta,ta gyara mata k’asan rigar sannan tace ta fita ta
basu wuri. Tana fita ta kalli Iman irin kallon sama da k’asa kafin tace
“Barka da rana amaryarmu.”
“Sannu.” Kawai Iman din tace ta juya zata bar wajen
amma sai ta dakatar da ita
“Nace ba, ya kika ji da kwanan bakin ciki? A ranar farkon
ki a dakin mijinki?”