HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 21-25

“Bakin ciki kuma? Na me kenan?” Ta tambaya Kai tsaye
kamar bata gane me Lailan take nufi ba

 

“Na abinda kika gani mana, bakin gani, kinga true color din
so called mijinki ko?.”

 

” Ohh, wannan wasan kwaikwayon wai? Yayi kyau sosai ya kuma
tsaru yadda ya kamata, sai dai shi actor din be san kan wasan ba dan be ma san
me yake faruwa ba, shine kawai matsalar film din amma yayi kyau.”

 

“Me kike nufi?” Tace a hasale tana mikewa tsaye

 

” Abinda kika sani shi nake nufi, kin dauka zan yarda da
banzan plan dinki? I’m not an illiterate, I can tell when someone is lying,
beside mijina ba zai taba aikata abinda kika ikirarin ya aikata, and i trust
him yadda bakya tunani.”

 

“Wow! Wow!! Wow!!! Sannu da kokari, I love your confidence,
amma wanne irin sani kikayi masa haka? Da har zaki bashi irin wannan yardar?
Kinsan waye namiji kuwa?”

 

” It doesn’t matter yaushe na sanshi, all that matters now
shine, miji na ne, kuma nayi trusting nashi, dari bisa dari.”

 

” Shikenan, sai muga yadda zakiyi depending mijin naki at
this critical condition, let’s see how far you can go….”

 

” Kwana hudu kachal kike da, idan har baki samu way out ba.
Ki shirya karba ta a matsayin kishiyar ki, sannan na fitar dake ta karfin
gaske, dan baki da waje a gidan nan, captain nawa ne right from the start kuma
he will always be mine.”

 

Murmushi Iman tayi mata, tana jin wani irin tsana da haushin
Lailan, tana jin zata iya komai, idan tace komai tana nufin komai domin taga ta
fitar da shi daga koma menene, akwai babban kalubale a gabanta, amma ba zata
karaya ba, duk wanda ya rik’e Allah da addu’a ya gama, da ikon Allah sai tayi
galaba akan duk wani makiyin su. Ta daina shiru, duk wanda yace mata kule! Zata
ce masa chas! Ita kanta bata san tana da courage din da zata iya maida mata
martani ba, sai gashi.

 

Juyawa tayi ta koma bedroom din dan ba zata cigaba da bata
lokaci akan wadda bata tunanin tana da hankali ko kad’an. Wayarta ta gani ajiye
a saman chest of drawers ta dauka ta kira Mamma da k’yar, sukayi magana ta
ajiye ta zauna tana lissafin rayuwar da zatayi a irin wannan gida, tuna sanda
ake mata fad’a irin na bankwana tayi, wata Babar su Abba tana ta jaddada mata
hakuri da kuma shirya wa duk wani kalubale na gidan sarauta, karta bari a
takata kar kuma ta cuci kowa, akwai makirci sosai wanda zata gamu dashi amma
idan ta nutsu tayi hakuri da karfin addu’a Allah zai bud’e mata komai.

   Bata jima a zaune ba taji ana mata knocking, ta
tashi ta bud’e ta fito, russunawa tayi har k’asa da sauri ta gaishe ta, kunya ta
kama Iman din ganin Matar da zata yi kusan sa’ar Mama tana gaishe ta a haka.
Kaya ta mika mata cikin girmamawa tace ta chanja zata rakata bangaren Fulani
(Ammi) juyawa tayi ciki, dan dama kayan jikin ta sun dame ta sosai. Sai da ta
shirya tsaf  sannan ta fito, ta lura Laila ta jima da barin falon sai dai
mayen kamshin da take yana nan a falon. Kai tsaye shashen Ammi suka wuce wanda
sai a sannan ne ta sake karewa fadar gani sosai. Anan suka tarar da su Mamma da
wasu mutanen wanda da yawan su kana kallo zaka gane alakar su da gidan saboda
yanayi na kama da suke da juna. Shigowar su ya saka kowa maida hankali kanta
kowa na son ganin amarya, tunda jiya babu wanda ya samu ganin ta saboda dare.
Kanta a k’asa taki yarda ta dago saboda yadda take jin kamar ta nutse, a
tunanin ta duk sun san daga in da ta taho, bata san Mamma bata fad’a ba sun dai
barshi a zuwan sun barota ne tana shiryawa. Sai da duk suka lafa ne aka
zazzauna sannan ta gaida Mamma da take kallon ta da murmushi, murmushin da ita
kadai ta san ma’anar sa, hakan ya sake saka Iman din cikin jin kunya.

  Sanda ta shigo Ammi bata falon, tana zaune suna magana
da Amaani ta dawo, da sauri Iman din ta zamo daga kujerar ta gaishe ta, ta
rik’e ta, ta mik’ar da ita tsaye tana amsawa a sake sosai, sannan ta saka a
raka Iman din part din Kilishi.

   Hannun ta cikin na Amaani suka shiga, babu kowa a
falon farko sai wata baiwa guda tana goge-goge,wadda ta rako su ce tace su
zauna sannan ta nufi kofar ciki don sanar da zuwan su. Jim kad’an ta dawo ta
tsaya a gefe, zuwa wani lokaci Kilishin ta fito, fuskar ta kadaran kadahan ba
zaka gane komai ba, Iman bata kalle ta ba, ta gaishe ta cikin girmamawa ta amsa
a yatsine bata ma zauna ba.

 

“Hari wannan din itace sirikar tamu?”

 

“Itace ranki ya dade.”

 

“Lallai sannu yarinya, shi ko Muhammad ya rasa wa zai dauko
mana sai yar karamar yarinya haka? Ko da yake ra’ayin sa ne ai, ba kuma a san
ya akayi ba dai, ko da yake dama dai yaran talakawa sai a hankali, idon su idon
me arziki sai in da karfin su ya kare, sannu kinji? Allah ya bada zaman
lafiya.”

 

Sai ta juya

 

” Hari naga amarya, ki gaida uwar dakin naki.”

 

Wani abu ne ya tokare wa Iman a makogwaro, idan har ta fahimci
maganganun matar tana nufin asiri tayi ta aure shi kenan, a fakaice ta ci mata
mutunci babu gaira babu dalili, bayan bata san ta ba, idan banda jiya sai yau
ne karo na biyu da ta taba ganin ta. Ajiye ta tayi a daidai mazaunin da da
ajiye Laila, ta kuma kuduri aniyar zama dasu daidai da yadda suka zaba.

  Daga nan sai suka wuce bangaren Aji da Hajja, amma a
mota saboda tazarar dake tsakanin bangarorn biyu, sosai taga karamci da
girmamawa dan Adam, Hajja kamar ta goye ta saboda murna, ta dinga tsokanar ta
da ta kwace mata miji da rana tsaka, murmushi kawai Iman din take, hakan ya
janyo suka dade sosai a bangaren har zuwa sanda taji sallamar sa, ta dago suka
hada ido sanda yake shigowa ciki, jamfa da wando ne a jikin sa kalar sararin
samaniya, ya tsaya iya kar guiwar sa, kansa sanye da hula me kalar duhu, yayi
kyau sosai, da sauri ta janye idon ta kunyar abinda ya faru daren jiya na hasko
mata, murmushi yayi me kyau ya karaso ya zauna kujerar dake fuskantar ta. Hajja
dake nade a saman wani cushion me laushi ta tabe baki tana dubanss

 

“Saboda rashin kunya shine ka biyo bayanta ko?”

 

“Toh ya zanyi? Kin rik’e min ita kin hanata tafiya.”

 

“Ah lallai, shine ka biyo baya kazo kaga ni, toh ba zan
cinye ta ba ai.”

 

“Kai yar tsohuwar nan kin fiye rikici wallahi, kishi ne
nasan yake damunki ba wani abu ba.”

 

Dariya tayi tace

 

” Ai na bar mata kai tuntuni, kuje ku karata nima Amadu na
ya ishen.”

 

A tare duk suka yi dariya, ya kashe mata ido daya tayi saurin
dauke kai kamar bata ganshi ba.

 

” My wife!”

 

Yayi kiranta a hankali karaf sai a kunnen Hajja, ta banka masa
harara ya sosa kai

 

“Dan nema, kin hadu da aiki kinji Fatima, mijin nan naki
bashi da kunya sam, bari kiga na tashi, taso yan mata muje na baki wani abu ki
bar wadannan.”

 

Tashi Amaani tayi tabi Hajjan, suna shigewa yayi saurin komawa
kusa da ita.

 

“Ka ganka ko?”

 

“Me nayi?” Ya tsare ta da ido yana marairaice fuska

 

“Gashi nan ka kori Hajja.”

 

“Rigimar tace kawai fa, mun saba irin haka da ita.”

 

“Toh ka koma chan ka zauna.”

 

” Wai kunya ta kike ji? Ko kunyar Hajja?”

 

” Both!” Tace tana kauda kanta

 

Murmushi yayi kawai

 

” Kinsan me? Bubu ya bani kwana hudu na kawo masa
gamsasshiyar hujja, idan ban kawo masa ba, zai aura min Laila.”

 

Sak tayi, duk da Laila ta riga ta fad’a mata amma ji daga bakin
sa ya sakata shiga yanayi,

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button