HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 21-25

” Karki damu, hakan ba zai faru ba, I promise you
that!”

 

” Allah ya bada sa’a.” Tace a sanyaye

 

” Zan je Abuja anjima ko gobe da safe zanyi kwana biyu, na
dawo”

 

” Tafiyar ba zata bamu matsala ba?”

 

” In sha Allah.”

 

” Shikenan, Allah ya kaimu ya dawo da kai lafiya.”

 

Tayi shiru tana tunanin yadda zata taimaka masa ta taimaki kanta
dan ba zata taba iya zama da Laila ba a yanayin ta.

 

***Idan tace tayi bacci a ranar tayi karya, tun bayan fitar
matar gidan da kawayenta bata sake nutsuwa ba, kuka take tun tana yi da hawaye
har ya zama babu hawayen sai suya da zuciyar ta, take kamar zata fito. Da
asubar fari taji ana buga kofar dakin amma a hankali, tashi tayi da k’yar tana
jin jiri jiri saboda yunwar da ta kwaso ta zare sakatar dakin. Da sauri ya
shigo ciki ya maida kofar ya rufe yana kallon ta, matsawa tayi baya tana masa
kallon tsana

 

“Karka matso nan wallahi zan iya illataka, ka maida ni
gidan mu wallahi ba zan zauna anan ba.”

 

“Rage muryar ki dan Allah, kar taji, kiyi hakuri zan yi
kokari naga na lallabata ta bar mu, mu koma gidan mu dan wallahi a matse nake,
kinsan dai mutum da sabuwar amarya.”

 

“Wallahi bazan koma ko wanne gida ba, gidan mu zaka mayar
dani ka sake ni kuma, ba zan zauna da kai ba na tsane ka.”

 

Saurin damkota yayi, ya toshe mata baki yana hade jikin su waje
daya

 

“Idan kina daga murya wallahi zamu dade a haka, idan ta
gano na sato hanya nazo ni dake duk ba zamu fita ba, yanzu ki kwantar da
hankalin ki, ki bita duk yadda tace zan dinga shigowa nan din da asubah tunda
bata tashi da asubah sai gari yayi haske sosai.”

 

Fizge kanta tayi tana masa mugun kallo

 

“Na tsane ka, na tsane ka Bashir har bansan iya adadin
tsanar da nayi maka ba, Allah ya isa cutar dani da kayi, kasan dama kana da
mata amma shine ka auro ni, wallahi sai ka sake ni ko na jawo maka abinda zaka
dade kana dana sani.”

 

“Baby!” Yaji muryar hajjajun tasa tana k’wala masa
kira, jikin sa ne ya hau rawa yayi hanyar fita hankalin sa a tashe,kafin ya
karasa ta turo kofar cikin shigar kayan bacci masu shegen kyau, tayi musu wani
kallo kafin ta kama hannun sa tana murmushi

 

“Kana nan ashe, toh wuce muje ko?”

 

“Toh;” yace yana yin gaba.

 

“Ke kuma, ki fito ki fara min aiki kafin gari ya gama
wayewa, akwai menu na kalolin abincin da nake son gani kullum a saman dining
bana kuma so ki wuce karfe goma baki gama komai ba.”

 

Ta juya tana karkada mata mazaunanta ta buga kofar. Hawayen
bakin ciki ne suka sakko mata, ta share tana shiga dan kurkutaccen bandakin da
ke gefen dakin ta dauro alwala da k’yar sboda yadda yake wani shegen wari ta
shinfid’a dankwalin ta, tayi sallah akai sannan ta bi ta hanyar zuwa kitchen
din dan ta tabbata idan har ta sake muguwar matar ta dawo bata fito ba zata iya
nada mata shegen duka babu abinda ya dameta gashi babu me kwatar ta dan shi
kansa Bashir din ba abakin komai yake ba.

  Menu din ta dauka tana kallo, babu abu daya daga cikin
kalolin girke-girken guda biyar da ta iya a ciki, tasan dai tabbas Iman tana yi
musu dukka a gida amma ita bata taba ko da sha’awar gwadawa ba, daga indomie
sai tea sune kadai take yi, sai yar taliya ko macaroni shima ba kullum ba, duk
wani girki me wahala kamar su tuwo da sauran su.

 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

 

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*

_SO DA ZUCIYA_

 

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

 

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

 

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

 

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

 

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

 

*_Zaku tura kudin a_*

 

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

 

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

 

08184017082

 

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

 

09134848107

2/1/22, 10:25 – Buhainat: Halin Girma

      25

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

***Ta dade a kitchen din tana jujjuya yadda zata yi, gashi
lokaci na tafiya dan har kusan bakwai ce zatayi, barin kitchen din tayi ta wuce
ta fara gyara falon, duk da ba wani datti da yayi amma sai da ta sake share shi
ta bubbuge kujerun ta tattare komai ta ajiye a gefe har da rigar baccin da ta
gani a jikinta dazu. Daga nan ta sake komawa kitchen din kawai ta yanke
shawarar tayi abinda zata iya, ta dauki indomie ta dafa da egg sannan ta dafa
ruwan tea ta jera musu akan dinning din ta wuce dakin da yake a mazaunin nata
da tunanin yadda zata samu waya ta kira gida, ko kuma ta samu hanyar da zata
bar gidan dan bata ga alamar Bashir zai kyaleta ta sauki ba.

  Tana zaune tana sak’awa da warwarewa aka turo wata
yarinya kiranta, kamar ba zata tashi ba, sai kuma ta mike tabi bayanta tana
taraddadin abinda zata tarar. Matan jiya ne jere akan dinning din, sai uwar
gayyar daga gefe ta hade rai sosai tana mata mugun kallo, tun kafin ta karaso
ciki ta hau surfa mata ashar

 

“Saboda tsabar ke yar iska ce, abinda nace ki dafa daban
abinda kika dafa daban ko? Zo nan.”

 

Kin zuwa tayi, ta k’ame a wajen tana kallon su

 

“Ji yadda ta tsare mu da ido Hajiya Lay, amma dai yarinyar
nan bata da kunya.”

 

“Ku barta, bata san wacece Layuza ba, zan koya mata
hankali.”

 

Bud’e baki Zeenat din tayi, tace.

 

“Ke nake aure ne wai ko shi?”

 

“Kutmelec! Ni kike wa wannan tambayar?”

 

“Toh ai naga dai iyaye na Bashir suka aura min ko? Me yasa
kike nuna kamar ni din me aiki ce a gareki, ni bansan ki ba, bansan wacece ke
ba kawai zaki dinga nuna iko akaina “

 

“Lallai yarinya, kinyi babban kuskure da har zan fad’a ki
mayar, toh dake da Bashir din duk a karkashi na kuke, kuma baki isa ki hada
miji dani ba wallahi, kinyi kad’an ace kece kishiyata, dan haka yanzu baki da
maraba da me aiki a gidan na, kuma dan ubanki dole kiyi duk abinda nace, na
samu labarin komai da yadda auren ya kasance, shegen kwadayi da son zuciyar
uwarki dake ya jawo miki, dan haka ki wuce ki yi abinda na saki kafin na taso
na yi miki mugun dukan da zaki kasa tashi wallahi.”

 

” Ai da kawai daidaita mata shegen bakin nan nata akayi
gobe ba zata sake fad’a ki fad’a ba.”

 

” Barta, zata gane kurenta.”

 

Zumburo baki tayi, ta ki barin wajen ita a lallai basu isa ba,
ganin haka ya saka Hajiya Layuza tasowa aikuwa tana ganin haka ta kwasa da gudu
bata tsaya ba sai data kai dakin tayi saurin saka sakata tana maida numfashi.

 

***Tagumi Mama ta rafka, duniyar gaba daya ta daina mata dadi
tun bayan da ta tabbatar da babu wani abu da zata iya dan Abba sai da ya sake
jaddada mata akan duk wani abu da ya samu auren Zeenat toh ta tabbatar da
mutuwar nata auren, ada taso suyi duk wacce zasuyi amma daga baya sai tayi wa
kanta fad’a ta hakura ta zuba wa sarautar Allah ido, gashi ta kikkira wayar
Zeenat din amma ko da yaushe bata shiga, takanas ta tura Habib ya je har kofar
gidan amma sai ya tarar a rufe, abinda ya kara daga mata hankali kenan, ta saka
Abba a gaba tana kuka dole ya dauki waya ya kira Bashir din, ya kuma yi mata
handsfree dan taji. Maganar an je an ga gidan a rufe Abban yayi masa nan ya
shaida masa ai suna family house dinsu sai sun danyi kwanaki zasu dawo gida
haka al’adar gidan su take, addua Abban yayi musu daga nan ya kashe yana kallon
Maman da tayi tsuru tana ji har suka gama.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button