HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 21

“Kinji abinda na fad’a miki ko?”

A hankali ta daga kanta alamar eh, ta daka mata tsawa tace

“Baki zaki bud’e kiyi min magana bana son rainin wayo.”

“Naji.” Tace tana barin kwallar da ta taru a idonta ta shiga sakkowa saman fuskarta. Dariya suka kwashe da ita, suka juya suka fita suna cigaba da zantuttukan su mara sa dadi ji.

***Bangaren amarya Iman kuwa komai na tafiya daidai, ta dade batayi bacci ba tana tunanin Moh da kalar soyayyar sa me tsayawa a zuciya, koman sa abin so da birgewa ne tun daga maganar sa har yadda yake tafiyar da ita. Da k’yar ta samu bacci ya dauke ta bayan ta gama tunanin nasa. Tun asubah da suka farka basu koma ba, kana jin yadda hayaniya take tashi a masarautar kasan akwai gagarumin shirin da ake yi. Shiryawa suka hau yi ita ta fara wanka sannan su Khadija suka yi. Suna fitowa falon suka tarar da abinci a jere na alfarma yana jiran su, nan suka hau kai suka ci suka yi nak, sannan aka turo tafiya da Iman din shashen Fulani. Alkyabba aka sake saka mata sannan suka fito kanta na k’asa tana jin yadda take shan gaisuwa kamar ta tsaya ta amsa amma yan matan nan sunce mata ksr ta tsaya amsawa haka sarautar take. 

   Da murna Fulani ta tarbe ta yau din ma, ta saka aka kaita har uwar dakin ta in da mutane suka dinga shigowa suna ganin ta wanda suke da kusanci da gidan. Ta jima sosai anan har suka soma jin tashin kidan kwarya in da adaidai lokacin su Mamma suka iso sai dai babu Mama, gaisuwa aka sake kafin a rakasu in da ake kidan kwaryar aka nuna musu wajen zaman su, kafin daga bisani a rako Iman din wajen itama. 

   Da yamma kuma aka dawo ciki aka sake shiryawa in da aka nufi hall din dan gabatar da bikin da kuma kyaututtukan da aka shiryawa Iman din. 

  Sakon Maimartaba ne ya samu Fulani akan yana son ganin Matar Muhammad din dan a yau zasu wuce komai dare, mamaki ya kama Fulani dan a yadda suka shirya kwanaki uku zasuyi a nan din kafin su tafi adamawar, bata sani ba Muhammad din ne da kansa yaje ya samu Takawan ya roke shi akan a rage bidiar dan shi kam ya gaji sosai, take kuwa ya amince har ma ya sanar da Bubu tun a daren jiyan. 

   Maimakon a wuce da ita hall din sai aka fara kaita wajen Takawar. Kanta a k’asa sosai kwarjinin sa ya cika wajen ta yadda kowa ya kasa sakewa, nasiha ya soma yi cikin maganar sa da ta saka jikin kowa mutuwa, yayi musu fatan alkhairi sannan ya kare da sake jan hankulan mutane akan yadda rayuwar ta zama, basu dade a wajen ba, suka fito kowa na yaba karamci na Maimartaba da ya karbe su hannu bibiyu ba tare da nuna banbanci ko wani abu ba.

   A gaggauce akayi taron, saboda tafiyar da zasuyi, sosai iman ta samu kyaututtuka masu tarin yawa a yan awowin da basu gaza biyar ba, kowa so yake ace shine yafi, kowa so yake ya burge Fulani da Maimartaba, dan kowa ya san yadda muhammad din yake a zukatansu.

***Motoci ne guda uku suka dauke su zuwa airport din daga su Mamma sai wasu yan uwan Abba su uku shikenan wanda zasu adamawar, shima saboda bikin da zasuyi ne suma badan haka ba da babu me zuwa. a lokacin Moh sun dade da isa suna zaune dasu Musaddik ana hira a wani kebantaccen wuri.

   Zuwan su da aka dan suka dauki hanya babu wani bata lokaci. Ita kadai ce a wajenta, babu kowa a saman duk suna k’asa sai ita kadai kwal har ta dinga tunanin dalilin da ya saka aka kawo ta nan din ba abarta wajen su Mamma ba. Kamshin turaren sa ne ya amsa mata tunanin ta, ya karaso ya zauna kusa da ita yana kashe mata ido. Kayan jikin sa ta kalla wanda suka kasance na sarauta, sai takalmin kafarsa da akayi da fatar zaki yayi kyau sosai shigar gidan sarauta, babu hula akan sa ya rik’e ta hannun sa, sumar sa ta fulani ta sha gyara ya fito a bafulatanin sa sosai. 

   Shi din ma shigar ta yake kallo, yana kuma yaba yadda komai ta saka sai yaga ya karbe ta yayi dai-dai da ita. 

“Ba magana?” Yace bayan ya gama kallon nata

Mirgina kanta tayi gefe tayi masa murmushi tace

“Sannu da zuwa toh.”

“Yawwa.” 

Yace yana jingina da kujerar jirgin sosai, be sake magana ba sai dai yanayin sa ya nuna mata kamar akwai damuwa, tasan yadda yake mata dan haka yau din sai taga kamar bashi ba, bata sani ba ko sarautar ce ta motsa. Satar kallon sa ta dinga yi sai taga ya kulle idon sa yayi kamar me bacci. Duk sai taji ta takura ta kuma damu, taba shi tayi kad’an, ya motsa amma be bude idon nasa ba, sai kamo hannun ta da yayi ya sakalo shi ta tsakanin nasa hannun ya harde su waje daya, kusan rabin jikin ta ya sauka a nasa, bata sake attempting komai ba har zuwa sanda suka iso jirgin ya sauka suka fito still hannun sa na sarke da nasa. 

   

***Kafarta a mike take tana sauraron bayanin da take mata, ko motsi batayi ba, kamar bata jin me take cewa har ta kai karshen bayanin tayi shiru tana kallon ta. Sai da ta dauki lokaci me tsawo kafin ta gyara zama, ta bud’e hannun ta, ta mik’a mata shi, jikinta na rawa ta ciro kwalbar da take nannade a gefen zanin ta, ta saka mata a cikin tafin hannun ta. Jujjuya shi tayi tayi a hannun nata tamkar me son gano wani abu.

“Turare ne ranki ya dade, a jiki kawai ake shafa shi bayan haka babu wani abu.” 

“Kin tabbatar da abinda kika ce?”

“Allah ya taimake ki, yadda nayi miki bayanin haka yake, yace kar ayi wasa dashi, sannan kuma kar ayi sakacin da za’a samu matsala.”

“Rik’e.” Ta mika mata, da sauri ta karba tana damke wa a hannun ta sosai.

” Kin tabbata babu wani abu da ya faru tsakanin su?”

” Na tabbatar, sai da ya nuna min komai kafin ya bani, yau zasu iso sai kiyi kokari kafin su tare a sabon bangaren su dan naji rad’e rad’in bikin ba zai dau kwanakin da aka tsara ba, bisa umarnin Sarki.”

Murmushi tayi me kyau, ta dawo ta zauna bayan ta ciro wata karamar riga ta karata a jikin ta,sai kuma ta ajiye tana mikar da hannun ta baya.

” Kinyi kokari, kina da kyauta me tsoka idan har na samu biyan bukata.”

” An riga ma an samu gimbiya, ki kwantar da hankalin ki.”

“Tukunna dai.”

” Me yayi saura? Yan awoyi ya rage miki ki samu abinda kike so gimbiya ta.”

Jikin tagar dakin ta karasa, ta daga labulayen tana kallon harabar gidan da yadda hadiman gidan ke kaiwa da komowa a tsakanin bangaren Moh din da na Ammi, tasan duk shirin tarbar bakin ake, hankalin kowa ya riga ya koma chan dan haka zatayi amfani da damar ta isa bangaren Moh ta yi zaman jiran dawowar shi!

Rano????

*_ZAFAFA BIYAR 2022????_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*

_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*????????

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*????????????

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*????????

09134848107

 

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button