HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 36-40

“Layin  da yake private mun saka an bud’e mana shi,
kuma mun tabbatar da ana kira da layin ne daga wani bangare ma dajin falgore!

 

“Yana ina yanzu? ”

 

” Yana ciki, idan an gama shiryawa shine zai shige gaba,
kaine team captain din da zai jagoranci tafiyar daga bangaren mu. “

 

” Ok sir! “

 

Yace yana sara masa, wucewa yayi zuwa in da aka ajiye fake
Musaddik din, yana so ya tantance banbance banbancen dake tsakanin sa da
Musaddik dinsa da ya kasa ganewa, yana durkushe a k’asa bayan dukan da ya sha,
ya tabbata dai da JABIR ya tantance shi sosai kafin ya kawo shi, dan hatta
tsawo da yanayin sa irin ma Musaddik din ne, fuskar sa ya dago, ya kare masa
kallo zuciyar sa na tafarfasa, kamar zai daure amma sai ya k’asa, ya dunkule
hannu ya naushe shi a baki, nan da nan kuwa sai jini, ya saka kafa ya hambare
shi. fitowa yayi ya tsaya a filin yayi bayanin yadda zasu yi idan sun isa, duk
suka amsa suka shiga motocin su a gurguje suka dauki hanyar dajin falgore.

    Gudu suke kamar zasu tashi sama, haka suke a duk
sanda suka fita operation amma kuma na yau yasha banban da sauran operation da
suka taba zuwa, yau abun nasu ne, su aka taba kai tsaye shiyasa kowa yake ji kaamar
abin ya shafe shi sosai, cikin kankanin lokaci suka isa saboda masifar gudun da
suke, barbazuwa sukayi a dajin kamar yadda yake according to plan. A daidai
lokacin Dr da zai kawo maganin ya iso, tana kwance kamar kullum ta gama
galabaita sosai ya shigo rataye da jakar sa, tana ganin sa ta mike da sauri,
bata ma san tana da ragowar karfin nan ba sai data ganshi, ya ajiye jakar ya
ciro magungunan a ajiye su, sannan ya koma gefe ya tsaya yana jiran shigowar
ogan, jim kadan sai gashi ya shigo, ya duba magungunan yayi masa bayanin yadda
za’a sha.

 

“Tashi!” Ya daka mata tsawa yana tamke fuska

 

“Dan Allah kayi hakuri, dan Allah.”

 

“Wallahi sai kin sha.”

 

“Dan Allah kayi hakuri.” Ummimi tace tana kuka

 

“Shut up munafuka, idan na sake jin bakin ki sai na sheke
ki har sai kin daina numfashi. “

 

Gefe ta koma jikin ta yana ta rawa, bindiga ya ciro ya nuna Iman
dashi

 

“Karbi kisha kafin na harbe ki. “

 

Hannu ta miko ya zuba mata, ya kafe ta da jajayen idon sa, yana
nuna ta da bindigar, ta sha sannan ya juya yana murmushin mugunta ya fice
likitan yabi bayan sa. Dakin da ya ajiye Musaddik da driver ya shiga, ya tarar
da Musaddik din a kwance amma kuma sallah yake daga haka, kwafa yayi ya fito
bayan ya rufe kofar, yazo wajen yaran nasa da suka cika harabar wajen dauke da
manyan bindigu cikin shirin ko ta kwana.

 

“Zan shiga na kwanta, ku kula sosai bana so a samu
matsala.”

 

“An gama Oga.”

 

  Suka hada baki wajen fad’a, ciki ya shiga su kuma suka
cigaba da tsaiwa a wajen.

  Zagaye gaba daya dajin sukayi, kowa ya kama stand dinsa,
Moh da sauran zaratan sojojin suka kutsa kai ciki, sai da suka dan shiga sosai
sannan suka hango bukkokin dake wajen, wanda suka tabbatar da nan suke. Sake
rarrabuwa sukayi waje waje, suka sake zagaye bukkukin.

  Sai da suka gama shiryawa tsaf, sannan Moh ya basu
signal na su yi attacking dinsu, nan fad’a musu ta sama ta ka, nan suka rikice
suka shiga kokarin maida martani, sai dai yawan Jami’an tsaron ya ninninka
yawan su,. Cikin baccin da ya soma dauke shi yaji alamun yamutsewar wajen,
kafin ya kai ga mikewa aka bugo kofar dakin aka shigo, Moh ne a gaba yaran sa
na take masa baya, dukkansu a shirye suke su bada rayuwar sa dan ceto Madam din
Oga. Kasancewar be shiryawa zuwan su ba, sai ya zama kamar sun ci galaaba akansa
ne, babu bindiga ba babu komai a hannun Moh, ya matse shi a jikin bango ya
shiga bugun sa, bugu ba na wasa ba, sai da yayi masa laga-laga ya sake shi
cikin jini ya fadi kasa, ya bi ya take kansa da kafarsa cikin tsananin bacin
rai ya soma magana.

 

“Kafin kaga karshe na, ni zan ga karshen ka da duk wanda ya
goya maka baya…”

 

” Oga an samu Madam, she’s bleeding so badly.” Da
sauri ya juya yabi bayan dan sanda da ya shigo, ya bar yaran nasa da JABIR.

  Jini ne sosai yake zuba, da sauri ya karasa gabanta,
idon ta da yake kokarin rufewa da kalle shi. Rawa jikin sa yake ya tallafota
jikin sa

 

” Bude idon ki, dan Allah ki bud’e idon ke, me sukayi miki?
Me sukayi miki?”

 

Karasa rufewa idon sukayi ruf, ya dagata ya fita da ita jikin sa
na rawa, idan har wani abu ya same ta, sai ya karar da dangin JABIR kaf.

 

_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

 

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*

_SO DA ZUCIYA_

 

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

 

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

 

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

 

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

 

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

 

*_Zaku tura kudin a_*

 

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

 

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

 

08184017082

 

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

 

09134848107

2/24/22, 08:05 – Buhainat: Halin Girma

 

40

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

****Wasu daga cikin sojin ne suka bi bayan sa, in da sauran
jami’an tsaron suka cigaba da dudduba bukokin har suka samu nasarar ganin
Musaddik da driver a wani daki, sai makamai masu yawan gaske suma daki gida,
dukkan su suna bukatar taimakon gaggawa musamman Musaddik da yake cikin
mawuyacin hali.

   Karar harbi suka ji, daga baya wanda basu san
dalilin harbin ba, a zaton su sun kama duk yaran JABIR din, da shi kansa JABIR
din bayan dukan da Moh yayi masa. Zagayawa baya sukayi, suka ga mutum a kwance
cikin jini, bashi da alamun yana tare da sauran yan iskan amma kuma basu san me
ya kawo shi wajen ba.

 

“Mu taimaka masa.”

 

“Waye ya harbe shi?”

 

“Akwai sauran yan iskan a baya, let’s check, ku dauke shi
ku tafi dashi zamu biyo bayanki. “

 

” Ok. “

 

Suka ce suka taimaka masa, da k’yar yake numfashi saboda tsabar
wahala, a motar da aka saka Musaddik suka saka shi, suka bi bayan motar da Moh
suke ciki dan basu taimakon gaggawa. Rik’e yake da hannun ta yana kuka wiwi
kukan da ya kasa dauriyar rik’e shi,  gani yake kamar motar bata sauri
duk kuwa da irin gudun da suke tsulawa, idan har wani abu ya same ta, ba zai
bar kowa ba wannan alkawarin sa ne.

  Sanda suke karaso asibitin tuni iyayen gulma yan jarida
sun iso domin samun na watsawa, kofar baya suka koma suka bi, suka shiga
asibitin dan a yanayin da take ciki ba zai yarda wasu yan iska su dauke ta a
hoto su yada wa duniya ba, duk ma wata gidan jarida ko talabijin da tayi
gangancin haka sai ya yi shari’a dasu.

   Da sauri nurses din suka karbeta, daidai lokacin
da Babban likita ya karaso cikin tawagar sauran manyan likitoci mata da maza,
aka shiga da ita ciki domin bata taimakon gaggawa.

   Zagaye ya soma yi a wajen cikin yanayi na fitar
hayyaci, wayar sa da take ta faman nemam agaji ya gaza fitowa da ita balle ya
iya amsa kiran da ake ta faman doka masa da ba zai wuce daga makusantan sa ba,
bashi da sukunin ciro wayar balle ma ya amsa ta, balle ya iya wata magana ba
tare da yasan halin da Iman din sa take ciki ba.

     Cikin kankanin lokaci asibitin ya cika da
manyan mutane daga masarauta da kuma gidan gwamnati, Takawa ne ya karaso a
karshe ya samu shiga wajen da Moh din yake shi kadai sai wasu sojoji daga gefe,
sauran mutane suna ta dayan bangaren in da aka kai Musaddik da saurayin da aka
harba wanda yake cikin yanayi mara dadi.

   Yana ganin Takawa yayi saurin isa gareshi, sai
kuma ya ja ya tsaya a gabansa ba, hannun sa ya kama, ya ji yadda hannun yake
rawa sosai kamar wanda yake jin masifaffen sanyi.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button