HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 36-40

“Kayi addu’a muhammad, babu abinda zai faru kaji?”

 

Da ka ya iya amsa masa, sai a sannan ya ga su Abba, ya matsa ya
gaishe su, dukkanin su suna cikin tashin hankali, Abba kamar bashi ba saboda
tashin hankali, sun riga Takawa zuwa wajen amma ba’a barsu sun shigo ba saboda
tsoron da yake wajen sai da Takawa yazo sannan suka samu shigowa. Sunyi waya da
Maman Iman din tun dazu ya kuma san zuwa yanzu sun karaso amma ba lallai su
shigo kai tsaye ba, sai ya dubi Muhammad yace

 

“Mahaifiyar ta suna waje, nasan ba za’a barsu su shigo
ba.”

 

“Bari naje.” Ya fad’a yana yin gaba, daya daga cikin
sojan ya bishi suka tafi tare, daga chan baya ya hango su a tsaye suna magana
da wani Soja da yaki fafur barin su, su shiga wajen, ganin Moha da kansa ya
nufo wajen ya saka sojan sake kallon matan.

 

“Alhamdulillah.” Mamma tace tana share hawayen ta

 

Bud’e musu sojan nan yayi tun ma kafin ya karaso, dan yayi masa
alamar ya barsu, suka shigo suka sameshi, ya gaishe su, sannan suka tambaye shi
Iman din, Alhamdulillah kawai yace suka bishi zuwa ciki duk jikin su ya kara
sanyi sosai da lamarin.

    Be barsu sun karasa wajen da su Takawa suke ba
kasancewar duk maza ne, sai yasa aka kawo musu kujera suka zauna shi kuma ya
karasa ciki.

   An dauki tsawon lokaci kafin likita guda daya ta
fito, har zata wuce sai ta ga Takawa, da sauri ta je ta durkusa ta gaishe shi,
sannan tace suna kokarin su in sha Allah babu matsala, sannan ta je ta dauko
abu ta dawo ta koma ciki.

     Sun iya iyakar kokarin da zasuyi wajen
ganin sun tsaida cikin amma kuma hakan be yiwu ba,saboda karfin maganin da aka
bata ba zai bar cikin ba, Allah yaso babu wani illa da yayi mata bayan fitar da
cikin. Wankin ciki suka hada sukayi mata sannan aka saka mata drip saboda ta
rasa ruwa sosai a jikinta tsawon kwanaki tana amai sannan babu abincin da take
ci. Numfashin da take fitar wa ne kadai zai baka tabbacin tana da rai bayan
haka babu wani abu na jikinta da yake motsi, tayi fayau kamar ba ita ba, sai
uban fari da tayi kamar babu wadataccen jini a jikinta.

   Tura ta akayi zuwa dakin da aka kwantar da ita,
sannan Drs din suka fito wajen da su Takawa suke, suka kwashi gaisuwa sannan
sukayi bayanin yadda al’amarin ya kasancewa pills din da aka bata ne yayi karbi
sosai, jiri ne ya kwashi Muhammad yayi kamar zai fadi wani bafade yayi saurin
taro shi, ya rik’e shi jikin sa. Hakuri kowa na wajen ya dinga bashi, kafin a
bada damar a shiga a ganta, Takawa ne ya fara shiga sannan su Abba suka shiga
tare dasu Mummy, sannan suka fito aka bar Muhammad din ya shiga. Tunda ya shigo
ya hangi yadda take fitar da numfashi a wahalce, jikin sa ya kara sanyi sosai,
shine duk ya jawo mata wannan matsalar tana zaman zaman ta. A da ya dauka
matsalar sa kawai gidansu ne, shiyasa gaba daya ya taso da tsanar mulki tun
bayan da yaga abinda ya faru da Baban su Laila lokacin bashi da wani girma
sosai amma hakan be bar kwakwalwar sa ba, ya taso da tsanar mulkin da ganin
cewa duk wata masifa tana cikin gidan sarauta.

   Sunyi aiki tare da JABIR zai iya kiransa da
abokin sa mafi kusanci dashi a wanchan lokacin, bashi da hannu a matsalar da
JABIR din ya samu daga sama har aka sallame shi aka kuma karawa Moh din matsayi
irjn wanda ya Jabir din ne ya chanchanta, bayan nan duk wata alaka tasu ta
yanke, har ya manta dashi sai lokaci zuwa lokaci yake tunashi,be taba saka wani
abu a ransa game dashi ba, rayuwar sa yake kansa tsaye ba tare da sanin akwai
babban makiyinsa da yake burin ganin bayan sa ba.

   Maganar Takawa ce ta fado masa wadda yayi masa
ita dazu kafin ya bar asibitin

 

_”Ka sani bawa baya taba wuce ko ketare kaddarar sa, dan
haka ka dauka wannan din kaddarar ka ce kayi addu’a Allah ya baka ikon cinyeta.
Sanin kanka ne mutum be isa ya hana ko dakatar da kaddarar ka ba, kafi kowa
sanin yaran da suke tare da kai suna tsaron ka gida da mota ba wai na matsayin
da kake dashi bane a aikin ka, alfarma tace ya saka aka baka su har haka, wanda
duk munyi hakan ne saboda mu baka kariya a gida da waje, sai dai yanzu na kara
tabbatar wa babu dan adam din da ya isa ya tsare ka face Allah, kuma duk abinda
Allah ya kaddara zai faru toh fa sai ya faru ko da a gaban idon mutum
ne.”_

   Gaban gadon ya ja ya tsaya cikin tsananin
tausayin ta, be taba kawo tunanin wani abu zai faru da su haka ba a dan
kankanin lokaci nan, ya zata shikenan ta rabu da duk wata matsala tun da suka
riga sukayi auren su, ashe ba haka bane. Hannun wanda babu drip a jiki ya
rik’e, ya zauna a gaban gadon yana karewa fuskar ta kallo, daga gani kasan ba
jin dadin baccin take ba, bacci ne me cike da wahala iri iri.

    Ya jima sosai a dakin, babu motsin komai, kamar
babu kowa aciki, knocking akayi, ya cire kansa da k’yar ya kalli kofar ba tare
da yayi magana ba, sai da aka sake kwankwasawa sannan yace

 

” Bismillah. ” Turo kofar akayi, Zeenat da Habib ne a
gaba sai Mam, sai sauran jama’ar gidan da sai yanzu suka samu damar shigowa
wajen, tashi yayi daga zaunen, ya mikawa Habib hannu suka gaisa, fuskar sa ta
dan daga alamun yayi kuka, ya mai jiki yayi masa sannan suka gaisa da sauran
matan, suka fita tare da Habib din waje,

 

“Ina Mahfuz?”

 

Yayi karfin halin tambayar sa dan yayi tunanin tare zasu zo. Dan
duban sa Habib din yayi kamar me tunani, sai kuma yace

 

“Ai tare aka fito dasu daga wajen da Iman din take.”

 

Kallon rashin fahimta Moha yayi masa yace

 

“Ban gane ba?”

 

Kwalla ce ta zubowa Habib din yayi saurin sharewa yana daurewa
yace

 

“Dazu da safe ya fito daga gida akan zaizo ya same ka, nace
zan raka shi amma ya bari anjima yace zai gane ma ai, shikenan ya tafi, bansan
ya akayi ba, sai gashi shima an same shi a chan in da Iman din take.”

 

Kafin ma ya karasa tuni Moh ya firgice, yasan an ce akwai mutum
uku bayan iman da Ummimi, daya an harbe shi ma aamma sam be kawo tunanin komai
ba, be ma kara tunawa ba saboda damuwar da ta danne shi, yana so dai yaje ya
tabbatar da Musaddik na cikin wadanda aka samo din amma sai yake ganin kamar
idan ya matsa daga wajen ta komai zai iya faruwa.

 

“Yana ina?”

 

“Yana chan emergency unit har yanzu bamu ji komai daga
garesu ba, su Abba dai suna chan?”

 

“Innalillah wa inna ilaihi rajiun, muje.”

 

Sauri sauri ya dinga yi kamar zai tashi sama, idan wani abu ya
samu yaron fa? Ya zai da ransa wai? Ba’a barin kowa ya shiga wajen nasa saboda
yadda case din nasa ya zama very complicated case, bayan sun yi nasarar cire
bullets din amma sam jinin ya ki tsayawa, ana kara wani, wani yana fita, su
kansu abin ya basu tsoro ganin yadda yake zubar da jini, shiyasa suka hana kowa
shiga, su Abba da suka dawo wajen tun da suka samu labari jikin kowa ya gama
sarewa da al’amarin Mahfuz din.

   Moh na isa wajen dr na fitowa daga ciki, jikin sa
babu kuzari ya nufo wajen da su Abban suke, ya kalle su daya bayan daya kafin
yace

 

” Sai dai muyi hakuri… “

 

Wani irin zubewa Moh yayi a wajen, kirjin sa na masa wani irin
suya, ashe Ajali ne ya kawo shi k’asar? Ashe dama shine sanadin mutuwar sa, me
yasa yayi masa wannna tsawar, me yasa ya ci masa mutunci bayan be san wani abu
dangane dashi ba,

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button