HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 36-40

“Muje mana.” Yace ganin yaki tada motar

 

“I’m sorry sir.” Yace sannan ya tada motar suka bi
bayan su sauran. Sake neman layin Musaddik yake a lokaci daya yana neman nata
amma duk magana daya ce, switch off, kansa ne ya daure sosai ta yadda za’a ce
basu da charge a wayar su kuma tun jiya, be san me yasa ba, sai kawai yaji
kamar babu lafiya.

 

“Me ya faru?”

 

“Na’am?”

 

“Kaji ni ai, what’s going on!”

 

“I’m very sorry sir, bamu san yadda akayi hakan ta faru ba,
amma we are trying our best kuma gaba daya k’asar ma.”

 

“Ban gane ba, me kake nufi?”

 

“Kayi hakuri sir, in sha Allah za’a gansu.”

 

” Nace maka me ya faru? Me kake nufi?” Ya fad’a a
tsawace yana tasowa kamar zai dake shi

 

“Kayi hakuri sir, ana neman Madam da driver ta da House
help din, tun jiya basu daw…**

 

” What!!!” Ya fad’a da karfi

 

“We are very sorry sir!”

 

” Wannan zancen banza ne, zancen wofi, menene amfanin ku?
Nace menene amfanin ku?”

Ya harzuko sai kawai ya taka birki suka tsaya

 

” Ta yaya akayi tun jiya basu dawo ba, kuma babu wanda zai
kirani ya fad’a min? Tun jiya fa!”

 

” Ohhh… Innalillah wa inna ilaihi rajiun, what’s going
on, me yake faruwa?”

 

A cikin tsananin tashin hankali yayi maganar, zuwa lokacin
idanun sa sun yi masifar kadawa, wani abu me karfi yazo ya tsaya masa a
makoshi, ya dinga jin kamar ya kamasu yayi ta bugu har sai sun fada masa yadda
akayi suka yi wannan sakacin.

   Basu wuce gida kai tsaye ba, station suka wuce
yana ta kiraye kirayen waya cikin karfin hali, ashe tuni labarin ya kai wa
shugaban su har ma da abokan tafiyar sa amma kowa yayi masa kus, ransa yayi
masifar baci, ga wani irin tashin hankali da yake ciki, yana tsoron wani abu ya
faru da ita, ba zai taba yafewa kansa ba, ba kuma zai yafewa duk wanda yake da
hannu a wannan al’amarin ba.

     Duk bayanan da ya kamata ya samu ya samu
a station, abu daya ne basu da tabbaci shine in da suke, dan duk babu waya a
tare dasu,sannan an cire tracker din dake hade da motar ta daina aiki tun daga
cikin school din anan ne last location din motar.

   Jiri ne yaji yana kokarin kayar dashi k’asa, da
sauri aka bashi kujera ya zauna yana dafe kansa, wayar sa da take ta faman kara
alamun kira ya zaro yana duba number din, Ammi ce tun dazu take son su yi
magana be samu dama ba, yace zai kirata amma kuma yasan ta kasa hakuri ne, kowa
ya shiga tashin hankali da dimuwa kasancewar kuma har an kwana amma babu wani
labari.

    Daga wayar yayi muryar sa a chan ciki, ya gaida
Ammin ta amsa cike da tausayawa tilon dan nata, tasan yana da karfin zuciya da
kokarin maida komai ba komai ba a tsawon rayuwar sa bata ga wani abu da ya
gigitashi ya firgita shi ba, amma tasan dole ne wannan tashin hankalin ba zai
iya rik’e shi ba, ba zai iya shanye shi ba ace matar ka na hannun bata gari, ba
kuma kasan abinda zai je ya dawo ba. Lallashi da ban baki ta dinga yi masa,
tana so ko yaya ne ya kwantar da hankalin sa duk da tasan ba lallai ba, yaji ta
ne kawai amma bashi da sukunin nan, yana cikin wasiwasi da tunanin wanda zai
aikata masa wannan danyen aikin, idan kidnapping dinta akayi saboda ransom
yasan tabbas zasu neme su a tsakanin kwana uku, amma kuma idan ba dan hakan
bane fa? Tsoro ne ya kara kamashi, ya mike da k’yar cikin wasiwasin abinda zai
je ya dawo, baya fatan wani abu daban ya bullo wanda be taba tunani ko hasashe
ba, a tunanin sa duk wani me matsala dashi ba zai wuce gidan su ba, Kamal da mahaifiyar
su, wambai da sauran masu goyon bayan Kamal din, bayan su, baya tunanin akwai
wani da wata matsala ta hada su da har zai iya yi masa haka.

   Tunanin sa ne ya katse, yana tuna abinda yake
cikin flash din nan da ya bawa Musaddik, yana bukatar sake dubawa ko zai samu
wata amsa a cikin video din, amma kuma ya kalla yafi sau nawa, sai dai kamar
akwai wani abu da yake missing, be san menene ba, amma kuma zai koma baya ya
sake dubawa sosai.

    Tunanin sa ne ya tsaya
akan Kamal, dalilin da ya kaishi bangaren sa har ya ajiye masa wannan macijin
robar, babu wani abu da ya dauka bayan wannan ajiyar da yayi,tashi yayi da
sauri

 

“Tracker ce!”

 

 Ya furta ba tare da yasan
a fili yayi maganar ba.

 

“Me kake tunani?” Shugaban yan sandan yace shima yana tashi
tsaye

 

“Kwanakin baya an ajiye min abu me kama da micijin robar
irin na wasan yara a adamawa,ina kyautata zaton tracker ce a jiki, ya akayi
nayi missing step din?”

 

“Wa kake tunani?”

 

” Bana tunanin kowa, amma koma waye ne, yana da alaka da
wannan case din.”

 

” Ina macijin robar.”

 

” Yana gida!”

 

” Nan ko adamawa?”

 

” Yana nan…”

 

“Ok muna bukatar shi ko zai taimaka mana wajen binciken
mu.”

 

” Shikenan.”

 

Hannu ya mik’a masa

 

” Sai naji daga gareku.”

 

” In sha Allah zamuyi kokarin mu.”

 

” Nagode.” Ya juya ya fice yana ayyana yadda zai fara
bibiyar su tamkar yadda suka dade suna bibiyar sa suma.

 

” Kamal…! I’m coming for you.”

 

A waje ya tarar dasu Abba da wasu yan tsirarin makusantan fada,
sai Musaddik da yake zaune daga gefe, wani kallo Moh yayi masa suna gaisawa
dasu Abba suna jajantawa juna, sai ya taso ya iso wajen su, ya tsaya daga gefe
suka gama gaisawa, tafiya Moh yace su Abba suyi saboda daren da ya fara yi
sosai, sallama sukayi masa akan zasu dawo gobe jikin kowa a mace suka tafi
gida.

 

” Ina ka shiga?” Ya jeho masa tambayar bayan ya raka
su Abba da ido sanda suke barin station din

 

“Ina gida, bansan me yake faruwa ba saboda an dauke min
waya a masallaci bayan mun idar da sallah jiya, sai Mom ce take fad’a min wai
meenal ta gani a media shine….”

 

“Is ok.” Yace yana yin gaba

 

” Menene kake shirin yi next?” Ya bishi yana tambayar
shi

 

” Me zanyi? Bayan case din yana hannun da ya dace, sai mu
zuba ido mu gani.”

 Yayi maganar kamar be
damu da abinda ya farun ba, gid’a kai Musaddik yayi ya cigaba da bin bayan sa
ganin yadda yake sauri kamar zai tashi sama. Har wajen mota ya rakashi, ya
tsaya daga baya maimakon ya shiga kamar yadda suka saba, alamar ya akayi Moh
yayi masa ganin ya toge daga baya be shigo ba

 

” A mota nazo, zamuyi waya Allah ya bayyana ta Allah ya
rufa asiri.”

 

” Ok.”

 

 Kawai yace ya zuke glass
din motar sama, suka bar wajen.

 

“His acting strange, amma tun yaushe?”

 

Ya tambayi kansa yana mamakin yanayin Musaddik din, share zancen
yayi kawai ya lumshe idon sa, kirjin sa na masa wani irin suya.

   A harabar masarautar
suka tsaida motocin, aka bud’e masa ya fito ya nufi ginin bangaren Takawa,
yanayin tafiyar sa kadai zaka kalla ka gane tsantsar damuwar da tayi masa
dabaibayi, har be san kalar tunanin da ya kamata yayi ba, a wanne hali take? Me
taci me suke mata? Duk shin yake masa yawo akai, a daren yau ba sai gobe ba,
zai fara aikin da yake ta jinkirtawa tsawon lokaci yana jiran right time kamar
yadda yasha cewa, sai dai yanzu yana ji aransa shine right time din.

   Tun da ya shigo Takawa
yake kallon sa cike da tausayawa, akwai sauran dauriya da jarumta a tattare
dashi duk kuwa da babu kaso mafi rinjaye na karsashin sa, amma karya kake daga
kallon fuskar sa ka iya tantance abinda yake wakana a zuciyar sa. Hakan ya dade
yana bashi nasara akan duk mutanen da basa son shi, dan be basu kofar da zasu
gano lagon sa ba, kuskuren sa daya, da yake kyautata zaton shi ya basu damar
cutar dashi, shine yadda ya kasa boye son da yake mata, har ya zama musu wani
tsani na ganin sun kaishi k’asa.

  Ya jima da sanin Kilishi
bata son ko ganin wulgawar shi, haka Kamal yana cikin jerin mutanen da zasu iya
yin komai don ganin bayan sa, sai kuma wambai da wasu mukarrabn fadar, sai dai
asalin kiyayar ba tashi bace, ta mahaifiyar shi ce da suke ganin an auro ta
daga gari irin na kano, suna ganin kamar hakan zai saka kanawa su zama sune
zasu mulke su. Sai dai idan ka tattara duk wadannan mutanen toh zaka samu basu
da wata alaka da iman din, balle idan sun cutar da ita su amfana da wani abu,
hakan ya saka kansa ya sake chunkushewa, ya rasa kalar tunanin da zai.

   Zubewa yayi agaban
Takawar, sai a lokacin yaji kamar an zare duk wani karfin zuciyar sa, yaji
bashi da sauran katabus, yaji komai masa ya saki, sai ya dinga jin sa tamkar
wani karamin yaron da aka dake shi aka kuma hanashi kuka.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button