HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 36-40

“Karka yi kokarin shanye bacin ran da kake ciki muhammadu,
ka fitar da komai zaka ji sauki.” 

 

Jan jikin sa yayi zuwa gaban Takawan, ya kwantar da kansa a
saman cinyar sa.

    Ya jima sosai a haka,
kafin ya fara jin nutsuwa na saukar masa, sai a lokacin ya dago, ya zauna
daidai.

 

“Sannu, babu abinda zai faru in sha Allah, zasu dawo lafiya
lou.”

 

“In Sha Allah.”

 

***Babu wanda batan Iman be girgiza ba, hatta Mama da take
ikirarin bata son ta sai da taji babu dadi, gidan ya cika duk kowa ya zo suna
zaman jajantawa juna, zeenat dama ko da Habib ya kaita gidan su Bashir din
achan suka same shi, yace su dawo zai zo da daddare sai su tafi, haka suka sake
kwaso kafa suka dawo gashi shiru be zo ba har washegari sai kuma wannan bakin
labarin.

   Mummy da Mamma sun zo a
ranar suma, suka sauka a gidan Iman din, kana kallon su kasan suna cikin tashin
hankali, kowa baya cikin nutsuwar sa musamman Abba, da mahaifiyar ta wanda suka
fi kowa kusanci da ita idan ka cire mijinta. Shi ba zaka taba gane ainahin
yanayin da yake ciki ba. Tunda ya shigo gidan ya shige daki ya kulle kansa, ya
dauko system din sa ya jona ta, yayi playing video din nan yana son ganin wani
abu. Ya dade sosai a dakin, har ma suka manta da ya shigo gidan, ba laifi gidan
da mutane wanda suka zo daga chan gidan sarki, sai su Ya Maryam da yan uwa dai
na kusa. Duk suna jiran tsammani.

 

***Sosai take galabaita saboda aman da take ta faman yi, babu
wani abu da yake zama a cikin ta komai taci sai ta dawo dashi, zuwa lokacin ta
gama galabaita dan ko tashi bata iyayi komai sai dai Ummimi tayi mata. Sau biyu
yana fad’a musu cewa gimbiya ta bata da lafiya amma suka yi biris da ita, suka
kyaleta a cikin wahalar suna sane da labarin yadda ake neman su babu dare babu
rana, duk wani moves din da jami’an tsaron suke suna sane dashi.

   Sigari ya zuka ya
fezar, sannan ya karbi sabbin layukan da ya saka aka kawo masa wajen guda
hamsin, daya ya dauka, ya mik’a hannu ya dauki yar karamar waya a gefen sa ya
saka, ya hau kai yayi murmushi ya shiga text message ya saka number Moh, ya
rubuta

 

_”Ba kudi muke bukata ba, rayuwar ka muke bukata a matsayin
fansa ga rayuka biyu masu muhimmanci a wajen ka, matar ka da cikin da take
dauke dashi.” _

 

Yana tura wa ya balla sim din, ya kyalkyale da mahaukaciyar
dariya.

 

_” Let the game begins Captain MAS!” _

 

 

 

 

_ZAFAFA2022🔥_*

 

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO_*

_SO DA ZUCIYA_

 

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

 

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

 

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

 

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

 

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

 

*_Zaku tura kudin a_*

 

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

 

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

 

08184017082

 

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

 

09134848107

 

 

 

8

2/19/22, 19:58 – Buhainat: Halin Girma

38

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

****

Zaune yake a office din commissioner of police lokacin da
message din ya shigo wayar, karantawa yayi yana kai karshe ya mike tsaye da
sauri.

 

“Ya akayi?” CP ya tambaya shi yana kallon yana yin sa

 

“Akwai matsala…” Sai ya mik’a masa wayar ya soma
zagaye a cikin office din cikin tsananin tashin hankali, idan har akwai ciki a
jikin Iman toh lallai tana cikin halin tashin hankali, yasan yadda ciki
musamman a watannin farko yadda yake wahalar wa yawa yawan mata suna shan
wahala kafin ciki yayi kwari wasu kamar zasu rasa ransu saboda tsabar wahala.
Ya take ciki yanzu? Me take ci?

 

“Akwai wani da kake da matsala dashi banda matsala ta cikin
gida?”

 

CP ya tambaye shi bayan ya maimaita karanta sakon fiye da sau
goma, har ya gano abu daya a cikin sakon, akwai kiyayye me zafin gaske tsakanin
duk wanda ya turo sakon, duk wanda yake son ranka ba karamin kiyayye yake maka.

  Girgiza kai yayi ba tare da yayi magana ba,

 

“Idan ka gamsu da maganganun da mukayi, lallai muna da
bukatar Kamal a binciken mu, domin idan har ka tattara bayanan baya da na yanzu
zaka gane akwai wani abu da yake a boye a bayan dukkan cases din, case din ka
da Laila, evidence din da ya wanke ka, sannan matar ka, zai iya yiwuwa wani ne
da yake son ta tun ba yanzu ba, ko kuma wanda yake da matsala da kai ne amma
shi da kansa yake son daukar fansa shiyasa har yayi kokarin wanke ka a baya,
duk wannan tunani na ne, ban ce ya zama gaskiya ba, amma ina ji a raina, cases
din suna da alaka da juna.”

 

Zama ya kuma yayi a kujerar da ya tashi yana tattare bayanan
dukka a kwakwalwar kansa, jiya baki daya ranar a cikin bincike yayi ta, babu
mutum daya da binciken sa ya nuna masa sai Kamal. Evidence din farko shine
sanda ya shiga bangaren sa, sai na biyu da suke zaune suna magana da wani mutum
ya sunkuyar da kansa, wata mace a gefen sa itama babu fuskar ta, fuskar Kamal
din ce kadai ta nuna wanda ya tabbata shi be sani ba, yana kyautata zaton gadar
zare suka danawa Kamal din sukayi amfani da son mulkin sa suka samu abinda suke
so sannan suka yi dumping din sa.

 

“Duk abinda ya kamata ayi, ayi Sir.”

 

“Zamu fara da Kamal, ina fatan hakan ba zai zama matsala ga
Maimartaba ba.”

 

“In Sha Allah.” Yace yana mikewa, jiri ne ya debe shi,
yayi kamar zai fadi da sauri CP ya tashi yana riko shi

 

“Subhanallah, Capt akwai matsala ba, sai ka daure saboda
tana matukar bukatar taimakon ka a wannan gabar.”

 

Gid’a masa kai yayi yana rik’e kansa da yake mugun sarawa, be
runtsa ba tunda ya diro garin Kano, ba kuma yajin idan ka cire ruwa ya sakawa
cikin sa wani abu, sai da ya dawo daidai sannan ya mike yayi masa sallama, ya
rakashi da ido yana yaba wa kwazon sa.

 

***Gidan su Iman din ya wuce kai tsaye, dan sunyi waya da Abba
da safe yake ce masa bashi da lafiya, kamar ma bp din sa ne yayi sama, yasan
batan Iman din ne ya saka shi shiga matsalar.

   A kofar gida ya tarar da Habib da saurayin nan na
ranar nan, dauke kai yayi kamar be gansu ba, sai da Habib din ya taso yazo
wajen sa yana kokarin kiran waya.

 

“Sannu da zuwa.”

 

“Ah… Babban Yaya.”

 

Ya mik’a masa hannu suka gaisa, sannan yayi masa jajen abinda ya
faru, suna maganar Mahfuz ya karaso wajen, ya mik’a masa hannu kansa tsaye,
kamar ba zai bashi hannun ba, sai kuma ya mik’a masa a dakile suka gaisa.

 

“Zanga Abba.”

 

“Owk Bismillah.”

 

Yayi gaba, shi kuma suka biyo bayan shi tare da Mahfuz har part
din su, Abba na kwance a falo kan doguwar kujera, Mama ta shiga ciki dauko
Hijab suka shigo, ya durkusa har k’asa ya gaida Abban, wanda yake kallon sa
ciki da tausayawa, ya ga dauriyar sa sosai dan kana kallon sa zaka gane yadda
ya tabu, ya rame sosai amma be karaya ba, be kuma zauna ba tun da ya dawo.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button