HALIN GIRMA 36-40

“Akwai labari ne muhammadu?”
“In sha Allah Abba, ana iyakar kokari.”
“Toh basu kira ba har yanzu ko?”
“Basu kira ba Abba.”
“Shikenan Allah ya dawo mana dasu cikin koshin
lafiya.”
“Amin Abba”
“Sannu da kokari, kai ma Allah ya biyaka, Allah ya tona
asirin azzalumai, tun jiya ban runtsa ba, na rasa in da zan saka raina naji
dadi, shikenan mutun bashi da daraja a k’asar nan tamu? Ace satar mutum tafi
satar kaza sauki? Wannan wacce irin musiba ce… Allahumma ajirni fi
musibati…”
“Allah ya bayyana su.”
” Amin ya Allah. “
Suka hada baki gaba daya, shigowar Mama da Zeenat a bayan ta ne
ya katse maganar da Moh yaso yayi, ya dan kalle su sai ya dauke kai ya maida
wajen Abba da alamun sa ya nuna yana jin jiki. Gaisawa sukayi da Mama sama sama
tayi masa jaje, sannan Zeenat da gaishe shi itama ya amsa yana mikewa.
“Bari na koma Abba, duk yadda ake ciki zan kira dan Allah
ka kwantar da hankalin ka.”
“Shikenan, Allah yasa muji alkhairi.”
” Sai anjima.” Ya dan kalli gefen da Mama take ya
fad’a sannan ya fice Habib da Mahfuz suka bi bayan sa, sun kusan kai gate din
gidan Mahfuz yace
” Zan iya taimakawa.”
Tsayawa chak Moh yayi da tafiyar da yake ya juyo.
“Idan har zaka yarda zan iya taimakawa.”
“How? Ta yaya?”
“Security ne from an intelligent agency a UK.”
“Sounds good.”
Moh yace yana dan rage hadewaar fuskar sa. Sai ya bud’e hannun
sa alamun babu matsala yace
“Idan har zaka iya taimakawa, shikenan sai muje ko?”
“Let me freshen up, zan zo daga baya. Ina zan same
ka?”
” Habib ka rakoshi gida na, don’t take long please.”
” In Sha Allah.”
Juyawa yayi ya fice su kuma suka koma ciki don Mahfouz ya
shirya, anan suka tarar da Gaji a part din ta saka Abba a gaba tana ta rusa
kuka, bata samu labarin ba sai da Moh yazo yanzu sannan tasan abinda yake
faruwa, taji zancen a radio har ta tausaya amma bata kawo Iman bace ,bata ma
fuskanci zancen ba kwata kwata ma gaba daya. Baki Abba yake bata akan tayi
hakuri amma taki, sai kuka take ita lallai sai an kaita gidan Iman din, a dole
haka Abba ya saka tabi su Habib din ko ta barshi ya ji da kansa shima kawai
dauriya ce irin ta namiji.
  Yana shiga gidan ya tarar da motocin masarauta,
ciki ya shiga kansa tsaye, da mamaki yake kallon Fulani a zaune a falon nasu,
tare da mummy da Mamma sai wasu matan, suna zaune jingum jingum cikin alhini da
jimami, daga gefe hadiman Fulanin ne suma a falon, kallo daya yayi ma duk matan
falon, ya karasa gaban Fulanin ya durkusa ya gaishe ta, ta amsa muryar ta na
rawa alamun bata dade da gama kuka ba, juyawa yayi ya gaida su mummy
wanda sai a lokacin ya samu ganin su, ta fad’a tayi fayau amma kuma a nutse
take sosai, sai yace ma Mamma ta fita fita hayyacin ta, wuce su yayi zuwa ciki,
suka rakashi da kallon tausayawa.
  Dafe kansa yayi bayan ya zauna a gefen gadon,
komai nata yana nan a dakin hatta da handouts din da ta fito dasu ranar da zata
tafin gasu nan a saman gado, be san me yasa abubuwan suka juye masa a yadda be
yi zato ko tsammani ba. Wayar sa ce tayi kara, ya dauka yana kallon sunan, Bubu
ne
“Menene alakar Kamal da batan matar ka?”
“Barka da rana Bubu…”
“Barka dai, ya mukaji da alhinin? Allah ya bayyana su cikin
koshin lafiya.”
“Amin ya Allah.”
“Ina jin ka, menene alakar Kamal da batan matar ka?”
Saman goshin sa ya shafa kad’an, kafin yace
“Bincike ne ya kawo hakan Bubu.”
“Shikenan, Allah ya sa muji alkhairi.”
“Amin ya Allah.” Yace sannan sukayi sallama.
  A tsammanin sa Musaddik zai neme shi da zarar
gari ya waye, ya kuma rakashi duk wani waje da zai je, amma kuma ga mamakin sa
sai gashi har rana ta daga babu ko waya daga gareshi, bayan yafi kowa sanin
muhimmancin da Iman take dashi a wajen sa, shine mutum na farko kuma na karshe
da ya yarda dashi kaf duniyar nan idan ka cire mutane hudu mafiya kusanci
dashi, Ammin sa, Takawa, Aji da Bubun sa, bayan su be yarda da kowa ba sai Musaddik
wanda ya yarda da tsantsar kaunar da shi ma yake masa, fiye da wadda shi yake
masa, say da yawa Musaddik ya sha shiga rigima saboda shi, ya kuma sha shiga
tashin hankali saboda shi, amma kuma ya kasa gane dalili daya, da zai saka
Musaddik din kasa jajanta masa kamar yadda ya saba a baya, duk wani abu masa
tare sukeyi.
  Tashi yayi yana dan zazzagaya dakin, yana so ya
dauke tunanin daga zuciyar sa,yana so yayi wa Musaddik din uzuri a karo na
farko kasancewar dan Adam ajizi ne, watakila wani uzurin ne ya danne wannan
din. Wayar sa ce tayi kara, ya matsa yana dubawa, sakon text message ne from an
unknown number, da sauri ya dauki wayar yana dubawa.
_”Ka shirya?”_
Da sauri ya maida masa reply
“Waye kai, me kake so?”
Sai da aka dau lokaci sannan akayi reply da wata number daban
“Ashe har kana da lokacin tsayawa tambayar waye bayan
rayuwar matar ka da ke cikin hatsari.”
“Ina zamu hadu? Ka dawo da ita nayi maka alkawarin zan kawo
maka kai na da kai na.”
Nan ma sai da aka sake daukar lokaci kafin yayi masa reply da
wata number daban kuma
_”Idan na shirya zan neme ka, karka bata lokaci wajen
tracking din number, ba zaka taba samu ba.” _
Kiran number yayi da sauri, amma sai yaji ta a kashe, ya bi
sauran layukan da sukayi magana suma duk a kashe, text message ya turawa CP na
numbers din dukka.
  Kira ne ya shigo wayar sa daga gate din gidan,
kamar be zai daga ba sai kuma ya tuno da zuwan su Habib, dagawa yayi suka
tambaye shi ko yasan su, yace a farsu su shigo brothers din Iman ne, da haka ya
kashe ya sauya rigar sa zuwa mara nauyi saboda zafin da yake ji.
***Dagata Ummimi tayi ta taimaka mata bayan ta gama amai, ta
gyara wajen ta dawo ta tsugunna a gabanta tana mata sannu, da kai ta amsa mata,
ta rufe idon ta hawaye ya gangaro mata. Shigowa sukayi su hudu, shine a gaba
suna bin bayan sa, ya zo gabanta ya durkusa ya saka hannu ya dago kanta.
“Fine Lady.” Ya shafi gefen fuskar ta, ta saka ragowar
karfin da take dashi ta ture shi, ya tuntsure da dariya yana kallon ta
“Ga Dr nan zai duba min ke, dan ina tunanin nine zan maye
gurbin Capt bayan na aikashi barzahu, kina da kyau.”
“Dr matso, a duba min da kyau idan har ciki ne, a cire shi
ko ta yaya ne, ba zan iya jure ganin sa ba, kaga auren mu ba zai dau lokaci ba
idan aka cire shi.”
Matsawo likitan yayi, ya bud’e idon ta, sannan ya taba goshin
ta, ya dauko wata roba a cikin kayan sa ya mikawa Ummimi.
” Gashi fitsari zatayi.”
Kin karba tayi, na bayan ya daka mata tsawa, ta karba da sauri
tana daga Iman din, dukkan su hawaye suke amma babu me bud’e baki yayi musu
saboda tsoro. Tare sukaje tayi fitsarin suka fito ta dawo ta kawo masa, ya
karba a wajen ya duba, ya kuma tabbatar da ciki ne, yan tambayoyi yayi mata
akan period dinta ta amsa tana kuka.
“Ciki ne oga, na sati shida.”
“Ya za’a yi dashi?”
“Ba zai wahalar fita ba, tunda karami ne. Yanzu dai zan
dawo sai nazo da maganin da zata sha.”
“Yayi kyau, rakashi yaro.” Rik’e masa jaka wanda aka
kira da yaro yayi suka fita, sannan shi ma suka fita.
“Hello… Samha baby.” Ya fad’a da yaji ta daga wayar
“Eh tana hannu har yanzu.”