HALIN GIRMA 36-40

“Eh ya tabbatar da ciki ne, amma za’a cire shi tunda baki
da bukatar shi.”
“A ah… Babu fa abinda zan yi wa masoyinki, kawai wata yar
harkalla ce zamu karasa ta. “
” Yawwa toh” tace tana jin dadi.
” Sai mun sake magana ko? “
” Amma ai bana samun ka kwata-kwata a waya, me yasa?”
” Babu komai, idan akwai bukatar muyi magana ni zan kiraki
da kai na.”
” Shikenan.”
Dariya yayi sosai bayan sun gama maganar, be san bata da tunani
ba kwata-kwata sai yanzu, amfani yayi da ita ya samu abinda yake so, ba kuma
zai kyale wanda ta kwallafa rai akai ba, ba zata taba samun cikar burin ta ba
in dai yana numfashi.
***A waje ya tarar da su Habib din bayan ya gama parker motar, ganin
tare suke da Gaji ya sakashi saurin karasawa ya taimaka mata ta fito, sannan
suka gaisa ya saka aka rakata ciki su kuma yace su biyo shi garden dake baya.
Kujeru ne a wajen, ya zauna sannan suka zauna suma, yana karantar yanayin
Mahfuz din, sai a lokacin yayi masa kallon tsaf, ya kuma fahimci hakan yanayin
sa ne, ku kuma yanayin environment din da ya taso kamar yadda Habib yayi masa
bayani dazu.
“Ta yaya zaka iya taimakawa?” Yace bayan ya gama
nakaltar yanayin sa, gyara zama yayi sosai, yayi murmushi sannan yace zai masa
yan tambayoyi,da ka ya amsa masa ya bashi go ahead.
“Babu wani message ko kira da ka samu daga wajen kidnappers
din?”
“Akwai.”
“Zan iya gani?”
“Why not?” Ya mik’a masa wayar, ya karba ya duba
messages din dukka, ya jima yana sake dubawa kafin ya mik’a masa wayar sa
“Kayi tunani sosai, wanene kake da matsala dashi, irin
wadda kasan lallai da zai samu dama akan ka zai iya aikata maka komai?”
“Babu shi, bansan waye ba gaskiya.”
” Babu ko old friend? Ko abokin aiki?”
Shiru yayi cikin tunani
” Think… “
_” Zan dawo komai daren dadewa, sai na dauki fansa akan ka,
ko da zan karar da komai da na mallaka ma duniya sai na maida rayuwar ka abun
kwatance! “_
“JABIR! ” Yace yana mikewa tsaye da sauri, tashi Mahfuz
yayi shima yana kallon sa
” Waye shi. “
” Aboki na ne, abokin aiki na ne. “
” Recently na samu labarin ya zama babban terrorist kuma
yana da connection da manyan k’asar, bayan shi bana tunanin akwai wanda zai
bukaci rayuwa ta, babu. “
“Ya akayi na manta? Ya akayi? “
” Kasan in da za’a same shi? “
Girgiza kai yayi,
” Ban sani ba. “
Komawa sukayi suka zauna, Mahfuz ya ciro biro da paper ya rubuta
wani abu, daidai lokacin da Moh ya daga wayar Musaddik yace ya same shi a
garden, yana ajiye wayar sai gashi ya zagayo dama chan yana cikin gidan, da
kallo Mahfuz ya bishi kafin ya karaso wajen yace
“Waye shi?”
“Best friend dina ne.”
“Ok.” Yace a gajarce ganin ya karaso, ya mik’a musu
hannu suka gaisa amma da ya bawa Mahfuz hanun sai ya rik’e hannun nasa har sai da suka kalle shi dukka,
sai ya saki yana murmushi ya jingina da kujerar da yake kai, wani kallo
Musaddik yayi masa ya zauna yana maida hankalin sa kan Moh.
“I’m very sorry Capt…”
“Babu komai, nasan wani uzuri ne dakai.” Ya katse shi
kafin ya karasa.
“Babu wani progress ko?” Yace
“Babu.”
“Allah ya bayyana su.”
“Amin.”
“Ya aiki?” Mahfuz ya tambayi Musaddik unexpectedly
“Aiki Alhamdulillah.”
“Wanne aiki kake?”
“Harkar kwangila, kaifa?”
“Detective!”
Wani kallo Musaddik yayi masa, yayi shiru,.sai kuma ya kalli Moh
“Naga kamar kana da baki, dama inaso muyi maganar flash din
nan ne tunda naga ka dawo.”
“Flash?” Mahfuz yayi karaf ya tambaya
“Let’s talk about that later.” Moh yace sai ya mik’a
wa Musaddik hannu
“Suna ina?”
Sosa kansa yayi
“Dalilin da yasa kaga kamar ina janye kaina a case din nan
kenan, wallahi bansan ya akayi ba, na rasa su gaba daya.”
“What!”
“Kayi hakuri,ranar da aka sace wayata aka hada dasu gaba
daya, bansan ya zan maka bayani ba, nasan kuma muhimmancin flash din a wajen
ka, shiyasa na kasa nutsuwa.”
Murmushi kawai Mahfuz yayi, ya dire pen din hannun sa akan dan
deborin da yake gaban sa, ya dora hannun sa akai ya jingina yana masa kallon
tsaf.
” Idan nace wani abu zaka yarda dani?”
Girgiza masa kai Moh yayi dan maganar batan flash din ba karamin
bashi mam I’llaki tayi ba.
“Ina bukatar yara hudu cikin yaranka na gate.”
” Me zasuyi maka?” Musaddik yace ransa a bace.
” Wait and see.” Yayi murmushi, shi Moh ba gane kan
maganar ba kwata kwata, yayi dai abinda Mahfuz yace ya kirawo su suka zo, suka
tsaya daga gefe, tashi Mahfuz yayi ya zagayo ta bayan Musaddik,
“Take off your mask!”
“Kamar ya?”
“Me kake nufi Mahfuz?” Moh da shima ya mike ya fad’a
cike da mamaki
” This man is deceiving you, ka kalli hannun sa, ka kalli
fuskar sa, akwai banbancin skin color, he’s definitely using a mask, idan har
ya musa, zan tabbatar maka.”
“Noo…you are mistaken, wannan Musaddik ne, trusted friend
dina ba zai taba deceiving dina ba,you cannot accused somebody without a
proof.”
” Shine zan maka proving yanzu ai, wait and see, guys… Ku
rik’e shi.”
” Dakata!”
Moh yace ransa na baci, ba zai dauki wulakanta Musaddik yana
kallo ba.
“Waye wannan Capt, waye zai zo ya shiga tsakani na da
kai?”
“Calm down aboki na, misunderstanding aka samu amma zan
masa magana…” Sai ya juya wajen Mahfuz din
“Let’s call it a day, zamuyi magana gobe, Habib ku jirani a
wajen mota.”
“Muje Mahfuz.” Wani
kallo yabi Musaddik din dashi, sannan ya juya suka bar wajen da Habib.
Juyawa kan Musaddik yayi da ransa yayi masifar baci, ya shiga
bashi hakuri akan abinda Mahfuz din yayi, yace ya jirashi yana zuwa bari ya
sallame su. Yana barin wajen ya ciro waya, ya kira shi yana matsawa chan gaba.
“Akwai matsala.” Yana dagawa yace
“Ya fara suspecting dinka ne?”
“Be fara ba, wani banzan yaro ne bansan daga ina yazo ba,
yaso dole sai ya nuna masa gaskiyar mask da na saka…”
“Ya yadda?”
“Be yarda ba, kasan ya yarda dani sosai, so ba zai taba
kawowa ba. “
” You have to be very careful, shi kuma yaron zan san yadda
zan yi dashi. “
” Ok sir. ” Ya kashe wayar yana juyowa, sukayi ido
biyu da Moh da yake tsaye a bayan sa kamar mayunwacin zakin da ya shekara be ce
ba.
***Assalamu alaikum sisters, masu korafi naga wasu daga cikin
korafin ku, ina mai baku hakuri akan matsalolin da aka samu, dan gane da rashin
posting halin girma shekaran jiya da jiya, hakan ya faru ne sakamakon ciwon
hakorin da ya matsa min hade da zazzabi, wanda har ta kai ban iya samun duba
sakonni ba balle har na iya zaman rubutu
Duk cikin zafafa biyar
babu wadda a cikin mu take jin dadi a duk sanda batayi posting ba, Allah ne
shaida ana iyakar kokari wajen ganin Anyi abinda ya dace. Sai dai idan abu ya
sha kan mutum a ba yadda ya iya. Allah ya huci zuciyar duk wanda ransa ya baci
ta dalilin jira ko wani abu, ba da gangan bane wani lokacin kuma ajizanci ne na
dan Adam.
Allah ya rufa asiri ya sa mu gama lafiya
2/21/22, 08:16 – Buhainat: Halin Girma
38
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb