HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 36-40

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

****

Zaune yake a office din commissioner of police lokacin da
message din ya shigo wayar, karantawa yayi yana kai karshe ya mike tsaye da
sauri.

 

“Ya akayi?” CP ya tambaya shi yana kallon yana yin sa

 

“Akwai matsala…” Sai ya mik’a masa wayar ya soma
zagaye a cikin office din cikin tsananin tashin hankali, idan har akwai ciki a
jikin Iman toh lallai tana cikin halin tashin hankali, yasan yadda ciki
musamman a watannin farko yadda yake wahalar wa yawa yawan mata suna shan
wahala kafin ciki yayi kwari wasu kamar zasu rasa ransu saboda tsabar wahala.
Ya take ciki yanzu? Me take ci?

 

“Akwai wani da kake da matsala dashi banda matsala ta cikin
gida?”

 

CP ya tambaye shi bayan ya maimaita karanta sakon fiye da sau
goma, har ya gano abu daya a cikin sakon, akwai kiyayye me zafin gaske tsakanin
duk wanda ya turo sakon, duk wanda yake son ranka ba karamin kiyayye yake maka.

  Girgiza kai yayi ba tare da yayi magana ba,

 

“Idan ka gamsu da maganganun da mukayi, lallai muna da
bukatar Kamal a binciken mu, domin idan har ka tattara bayanan baya da na yanzu
zaka gane akwai wani abu da yake a boye a bayan dukkan cases din, case din ka
da Laila, evidence din da ya wanke ka, sannan matar ka, zai iya yiwuwa wani ne
da yake son ta tun ba yanzu ba, ko kuma wanda yake da matsala da kai ne amma
shi da kansa yake son daukar fansa shiyasa har yayi kokarin wanke ka a baya,
duk wannan tunani na ne, ban ce ya zama gaskiya ba, amma ina ji a raina, cases
din suna da alaka da juna.”

 

Zama ya kuma yayi a kujerar da ya tashi yana tattare bayanan
dukka a kwakwalwar kansa, jiya baki daya ranar a cikin bincike yayi ta, babu
mutum daya da binciken sa ya nuna masa sai Kamal. Evidence din farko shine
sanda ya shiga bangaren sa, sai na biyu da suke zaune suna magana da wani mutum
ya sunkuyar da kansa, wata mace a gefen sa itama babu fuskar ta, fuskar Kamal
din ce kadai ta nuna wanda ya tabbata shi be sani ba, yana kyautata zaton gadar
zare suka danawa Kamal din sukayi amfani da son mulkin sa suka samu abinda suke
so sannan suka yi dumping din sa.

 

“Duk abinda ya kamata ayi, ayi Sir.”

 

“Zamu fara da Kamal, ina fatan hakan ba zai zama matsala ga
Maimartaba ba.”

 

“In Sha Allah.” Yace yana mikewa, jiri ne ya debe shi,
yayi kamar zai fadi da sauri CP ya tashi yana riko shi

 

“Subhanallah, Capt akwai matsala ba, sai ka daure saboda
tana matukar bukatar taimakon ka a wannan gabar.”

 

Gid’a masa kai yayi yana rik’e kansa da yake mugun sarawa, be
runtsa ba tunda ya diro garin Kano, ba kuma yajin idan ka cire ruwa ya sakawa
cikin sa wani abu, sai da ya dawo daidai sannan ya mike yayi masa sallama, ya
rakashi da ido yana yaba wa kwazon sa.

 

***Gidan su Iman din ya wuce kai tsaye, dan sunyi waya da Abba
da safe yake ce masa bashi da lafiya, kamar ma bp din sa ne yayi sama, yasan
batan Iman din ne ya saka shi shiga matsalar.

   A kofar gida ya tarar da Habib da saurayin nan na
ranar nan, dauke kai yayi kamar be gansu ba, sai da Habib din ya taso yazo
wajen sa yana kokarin kiran waya.

 

“Sannu da zuwa.”

 

“Ah… Babban Yaya.”

 

Ya mik’a masa hannu suka gaisa, sannan yayi masa jajen abinda ya
faru, suna maganar Mahfuz ya karaso wajen, ya mik’a masa hannu kansa tsaye,
kamar ba zai bashi hannun ba, sai kuma ya mik’a masa a dakile suka gaisa.

 

“Zanga Abba.”

 

“Owk Bismillah.”

 

Yayi gaba, shi kuma suka biyo bayan shi tare da Mahfuz har part
din su, Abba na kwance a falo kan doguwar kujera, Mama ta shiga ciki dauko
Hijab suka shigo, ya durkusa har k’asa ya gaida Abban, wanda yake kallon sa
ciki da tausayawa, ya ga dauriyar sa sosai dan kana kallon sa zaka gane yadda
ya tabu, ya rame sosai amma be karaya ba, be kuma zauna ba tun da ya dawo.

 

“Akwai labari ne muhammadu?”

 

“In sha Allah Abba, ana iyakar kokari.”

 

“Toh basu kira ba har yanzu ko?”

 

“Basu kira ba Abba.”

 

“Shikenan Allah ya dawo mana dasu cikin koshin
lafiya.”

 

“Amin Abba”

 

“Sannu da kokari, kai ma Allah ya biyaka, Allah ya tona
asirin azzalumai, tun jiya ban runtsa ba, na rasa in da zan saka raina naji
dadi, shikenan mutun bashi da daraja a k’asar nan tamu? Ace satar mutum tafi
satar kaza sauki? Wannan wacce irin musiba ce… Allahumma ajirni fi musibati…”

 

“Allah ya bayyana su.”

 

” Amin ya Allah. “

 

Suka hada baki gaba daya, shigowar Mama da Zeenat a bayan ta ne
ya katse maganar da Moh yaso yayi, ya dan kalle su sai ya dauke kai ya maida
wajen Abba da alamun sa ya nuna yana jin jiki. Gaisawa sukayi da Mama sama sama
tayi masa jaje, sannan Zeenat da gaishe shi itama ya amsa yana mikewa.

 

“Bari na koma Abba, duk yadda ake ciki zan kira dan Allah
ka kwantar da hankalin ka.”

 

“Shikenan, Allah yasa muji alkhairi.”

 

” Sai anjima.” Ya dan kalli gefen da Mama take ya
fad’a sannan ya fice Habib da Mahfuz suka bi bayan sa, sun kusan kai gate din
gidan Mahfuz yace

 

” Zan iya taimakawa.”

 

Tsayawa chak Moh yayi da tafiyar da yake ya juyo.

 

“Idan har zaka yarda zan iya taimakawa.”

 

“How? Ta yaya?”

 

“Security ne from an intelligent agency a UK.”

 

“Sounds good.”

 

Moh yace yana dan rage hadewaar fuskar sa. Sai ya bud’e hannun
sa alamun babu matsala yace

 

“Idan har zaka iya taimakawa, shikenan sai muje ko?”

 

“Let me freshen up, zan zo daga baya. Ina zan same
ka?”

 

” Habib ka rakoshi gida na, don’t take long please.”

 

” In Sha Allah.”

 

Juyawa yayi ya fice su kuma suka koma ciki don Mahfouz ya
shirya, anan suka tarar da Gaji a part din ta saka Abba a gaba tana ta rusa
kuka, bata samu labarin ba sai da Moh yazo yanzu sannan tasan abinda yake
faruwa, taji zancen a radio har ta tausaya amma bata kawo Iman bace ,bata ma
fuskanci zancen ba kwata kwata ma gaba daya. Baki Abba yake bata akan tayi
hakuri amma taki, sai kuka take ita lallai sai an kaita gidan Iman din, a dole
haka Abba ya saka tabi su Habib din ko ta barshi ya ji da kansa shima kawai
dauriya ce irin ta namiji.

   Yana shiga gidan ya tarar da motocin masarauta,
ciki ya shiga kansa tsaye, da mamaki yake kallon Fulani a zaune a falon nasu,
tare da mummy da Mamma sai wasu matan, suna zaune jingum jingum cikin alhini da
jimami, daga gefe hadiman Fulanin ne suma a falon, kallo daya yayi ma duk matan
falon, ya karasa gaban Fulanin ya durkusa ya gaishe ta, ta amsa muryar ta na
rawa alamun  bata dade da gama kuka ba, juyawa yayi ya gaida su mummy
wanda sai a lokacin ya samu ganin su, ta fad’a tayi fayau amma kuma a nutse
take sosai, sai yace ma Mamma ta fita fita hayyacin ta, wuce su yayi zuwa ciki,
suka rakashi da kallon tausayawa.

   Dafe kansa yayi bayan ya zauna a gefen gadon,
komai nata yana nan a dakin hatta da handouts din da ta fito dasu ranar da zata
tafin gasu nan a saman gado, be san me yasa abubuwan suka juye masa a yadda be
yi zato ko tsammani ba. Wayar sa ce tayi kara, ya dauka yana kallon sunan, Bubu
ne

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button