HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 36-40

“Menene alakar Kamal da batan matar ka?”

 

“Barka da rana Bubu…”

 

“Barka dai, ya mukaji da alhinin? Allah ya bayyana su cikin
koshin lafiya.”

 

“Amin ya Allah.”

 

“Ina jin ka, menene alakar Kamal da batan matar ka?”

 

Saman goshin sa ya shafa kad’an, kafin yace

 

“Bincike ne ya kawo hakan Bubu.”

 

“Shikenan, Allah ya sa muji alkhairi.”

 

“Amin ya Allah.” Yace sannan sukayi sallama.

   A tsammanin sa Musaddik zai neme shi da zarar
gari ya waye, ya kuma rakashi duk wani waje da zai je, amma kuma ga mamakin sa
sai gashi har rana ta daga babu ko waya daga gareshi, bayan yafi kowa sanin
muhimmancin da Iman take dashi a wajen sa, shine mutum na farko kuma na karshe
da ya yarda dashi kaf duniyar nan idan ka cire mutane hudu mafiya kusanci
dashi, Ammin sa, Takawa, Aji da Bubun sa, bayan su be yarda da kowa ba sai
Musaddik wanda ya yarda da tsantsar kaunar da shi ma yake masa, fiye da wadda
shi yake masa, say da yawa Musaddik ya sha shiga rigima saboda shi, ya kuma sha
shiga tashin hankali saboda shi, amma kuma ya kasa gane dalili daya, da zai
saka Musaddik din kasa jajanta masa kamar yadda ya saba a baya, duk wani abu
masa tare sukeyi.

   Tashi yayi yana dan zazzagaya dakin, yana so ya
dauke tunanin daga zuciyar sa,yana so yayi wa Musaddik din uzuri a karo na
farko kasancewar dan Adam ajizi ne, watakila wani uzurin ne ya danne wannan
din. Wayar sa ce tayi kara, ya matsa yana dubawa, sakon text message ne from an
unknown number, da sauri ya dauki wayar yana dubawa.

 

_”Ka shirya?”_

 

Da sauri ya maida masa reply

 

“Waye kai, me kake so?”

 

Sai da aka dau lokaci sannan akayi reply da wata number daban

 

“Ashe har kana da lokacin tsayawa tambayar waye bayan
rayuwar matar ka da ke cikin hatsari.”

 

“Ina zamu hadu? Ka dawo da ita nayi maka alkawarin zan kawo
maka kai na da kai na.”

 

Nan ma sai da aka sake daukar lokaci kafin yayi masa reply da
wata number daban kuma

 

_”Idan na shirya zan neme ka, karka bata lokaci wajen
tracking din number, ba zaka taba samu ba.” _

 

Kiran number yayi da sauri, amma sai yaji ta a kashe, ya bi
sauran layukan da sukayi magana suma duk a kashe, text message ya turawa CP na
numbers din dukka.

    Kira ne ya shigo wayar sa daga gate din gidan,
kamar be zai daga ba sai kuma ya tuno da zuwan su Habib, dagawa yayi suka
tambaye shi ko yasan su, yace a farsu su shigo brothers din Iman ne, da haka ya
kashe ya sauya rigar sa zuwa mara nauyi saboda zafin da yake ji.

 

***Dagata Ummimi tayi ta taimaka mata bayan ta gama amai, ta
gyara wajen ta dawo ta tsugunna a gabanta tana mata sannu, da kai ta amsa mata,
ta rufe idon ta hawaye ya gangaro mata. Shigowa sukayi su hudu, shine a gaba
suna bin bayan sa, ya zo gabanta ya durkusa ya saka hannu ya dago kanta.

 

“Fine Lady.” Ya shafi gefen fuskar ta, ta saka ragowar
karfin da take dashi ta ture shi, ya tuntsure da dariya yana kallon ta

 

“Ga Dr nan zai duba min ke, dan ina tunanin nine zan maye
gurbin Capt bayan na aikashi barzahu, kina da kyau.”

 

“Dr matso, a duba min da kyau idan har ciki ne, a cire shi
ko ta yaya ne, ba zan iya jure ganin sa ba, kaga auren mu ba zai dau lokaci ba
idan aka cire shi.”

 

Matsawo likitan yayi, ya bud’e idon ta, sannan ya taba goshin
ta, ya dauko wata roba a cikin kayan sa ya mikawa Ummimi.

 

” Gashi fitsari zatayi.”

 

Kin karba tayi, na bayan ya daka mata tsawa, ta karba da sauri
tana daga Iman din, dukkan su hawaye suke amma babu me bud’e baki yayi musu
saboda tsoro. Tare sukaje tayi fitsarin suka fito ta dawo ta kawo masa, ya
karba a wajen ya duba, ya kuma tabbatar da ciki ne, yan tambayoyi yayi mata
akan period dinta ta amsa tana kuka.

 

“Ciki ne oga, na sati shida.”

 

“Ya za’a yi dashi?”

 

“Ba zai wahalar fita ba, tunda karami ne. Yanzu dai zan
dawo sai nazo da maganin da zata sha.”

 

“Yayi kyau, rakashi yaro.” Rik’e masa jaka wanda aka
kira da yaro yayi suka fita, sannan shi ma suka fita.

 

“Hello… Samha baby.” Ya fad’a da yaji ta daga wayar

 

“Eh tana hannu har yanzu.”

 

“Eh ya tabbatar da ciki ne, amma za’a cire shi tunda baki
da bukatar shi.”

 

“A ah… Babu fa abinda zan yi wa masoyinki, kawai wata yar
harkalla ce zamu karasa ta. “

 

” Yawwa toh” tace tana jin dadi.

 

” Sai mun sake magana ko? “

 

” Amma ai bana samun ka kwata-kwata a waya, me yasa?”

 

” Babu komai, idan akwai bukatar muyi magana ni zan kiraki
da kai na.”

 

” Shikenan.”

 

Dariya yayi sosai bayan sun gama maganar, be san bata da tunani
ba kwata-kwata sai yanzu, amfani yayi da ita ya samu abinda yake so, ba kuma
zai kyale wanda ta kwallafa rai akai ba, ba zata taba samun cikar burin ta ba
in dai yana numfashi.

 

***A waje ya tarar da su Habib din bayan ya gama parker motar,
ganin tare suke da Gaji ya sakashi saurin karasawa ya taimaka mata ta fito,
sannan suka gaisa ya saka aka rakata ciki su kuma yace su biyo shi garden dake baya.
Kujeru ne a wajen, ya zauna sannan suka zauna suma, yana karantar yanayin
Mahfuz din, sai a lokacin yayi masa kallon tsaf, ya kuma fahimci hakan yanayin
sa ne, ku kuma yanayin environment din da ya taso kamar yadda Habib yayi masa
bayani dazu.

 

“Ta yaya zaka iya taimakawa?” Yace bayan ya gama
nakaltar yanayin sa, gyara zama yayi sosai, yayi murmushi sannan yace zai masa
yan tambayoyi,da ka ya amsa masa ya bashi go ahead.

 

“Babu wani message ko kira da ka samu daga wajen kidnappers
din?”

 

“Akwai.”

 

“Zan iya gani?”

 

“Why not?” Ya mik’a masa wayar, ya karba ya duba
messages din dukka, ya jima yana sake dubawa kafin ya mik’a masa wayar sa

 

“Kayi tunani sosai, wanene kake da matsala dashi, irin
wadda kasan lallai da zai samu dama akan ka zai iya aikata maka komai?”

 

“Babu shi, bansan waye ba gaskiya.”

 

” Babu ko old friend? Ko abokin aiki?”

 

Shiru yayi cikin tunani

 

” Think… “

 

_” Zan dawo komai daren dadewa, sai na dauki fansa akan ka,
ko da zan karar da komai da na mallaka ma duniya sai na maida rayuwar ka abun
kwatance! “_

 

“JABIR! ” Yace yana mikewa tsaye da sauri, tashi
Mahfuz yayi shima yana kallon sa

 

” Waye shi. “

 

” Aboki na ne, abokin aiki na ne. “

 

” Recently na samu labarin ya zama babban terrorist kuma
yana da connection da manyan k’asar, bayan shi bana tunanin akwai wanda zai
bukaci rayuwa ta, babu. “

 

“Ya akayi na manta? Ya akayi? “

 

” Kasan in da za’a same shi? “

 

Girgiza kai yayi,

 

” Ban sani ba. “

 

Komawa sukayi suka zauna, Mahfuz ya ciro biro da paper ya rubuta
wani abu, daidai lokacin da Moh ya daga wayar Musaddik yace ya same shi a
garden, yana ajiye wayar sai gashi ya zagayo dama chan yana cikin gidan, da
kallo Mahfuz ya bishi kafin ya karaso wajen yace

 

“Waye shi?”

 

“Best friend dina ne.”

 

“Ok.” Yace a gajarce ganin ya karaso, ya mik’a musu
hannu suka gaisa amma da ya bawa Mahfuz hanun sai ya rik’e  hannun nasa har sai da suka kalle shi dukka,
sai ya saki yana murmushi ya jingina da kujerar da yake kai, wani kallo
Musaddik yayi masa ya zauna yana maida hankalin sa kan Moh.

 

“I’m very sorry Capt…”

 

“Babu komai, nasan wani uzuri ne dakai.” Ya katse shi
kafin ya karasa.

 

“Babu wani progress ko?” Yace

 

“Babu.”

 

“Allah ya bayyana su.”

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button