HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 36-40

“Amin.”

 

“Ya aiki?” Mahfuz ya tambayi Musaddik unexpectedly

 

“Aiki Alhamdulillah.”

 

“Wanne aiki kake?”

 

“Harkar kwangila, kaifa?”

 

“Detective!”

 

Wani kallo Musaddik yayi masa, yayi shiru,.sai kuma ya kalli Moh

 

“Naga kamar kana da baki, dama inaso muyi maganar flash din
nan ne tunda naga ka dawo.”

 

“Flash?” Mahfuz yayi karaf ya tambaya

 

“Let’s talk about that later.” Moh yace sai ya mik’a
wa Musaddik hannu

 

“Suna ina?”

 

Sosa kansa yayi

 

“Dalilin da yasa kaga kamar ina janye kaina a case din nan
kenan, wallahi bansan ya akayi ba, na rasa su gaba daya.”

 

“What!”

 

“Kayi hakuri,ranar da aka sace wayata aka hada dasu gaba
daya, bansan ya zan maka bayani ba, nasan kuma muhimmancin flash din a wajen
ka, shiyasa na kasa nutsuwa.”

 

Murmushi kawai Mahfuz yayi, ya dire pen din hannun sa akan dan
deborin da yake gaban sa, ya dora hannun sa akai ya jingina yana masa kallon
tsaf.

 

” Idan nace wani abu zaka yarda dani?”

 

Girgiza masa kai Moh yayi dan maganar batan flash din ba karamin
bashi mam I’llaki tayi ba.

 

“Ina bukatar yara hudu cikin yaranka na gate.”

 

” Me zasuyi maka?” Musaddik yace ransa a bace.

 

” Wait and see.” Yayi murmushi, shi Moh ba gane kan
maganar ba kwata kwata, yayi dai abinda Mahfuz yace ya kirawo su suka zo, suka
tsaya daga gefe, tashi Mahfuz yayi ya zagayo ta bayan Musaddik,

 

“Take off your mask!”

 

“Kamar ya?”

 

“Me kake nufi Mahfuz?” Moh da shima ya mike ya fad’a
cike da mamaki

 

” This man is deceiving you, ka kalli hannun sa, ka kalli
fuskar sa, akwai banbancin skin color, he’s definitely using a mask, idan har
ya musa, zan tabbatar maka.”

 

“Noo…you are mistaken, wannan Musaddik ne, trusted friend
dina ba zai taba deceiving dina ba,you cannot accused somebody without a
proof.”

 

” Shine zan maka proving yanzu ai, wait and see, guys… Ku
rik’e shi.”

 

” Dakata!”

 

Moh yace ransa na baci, ba zai dauki wulakanta Musaddik yana
kallo ba.

 

“Waye wannan Capt, waye zai zo ya shiga tsakani na da
kai?”

 

“Calm down aboki na, misunderstanding aka samu amma zan
masa magana…” Sai ya juya wajen Mahfuz din

 

“Let’s call it a day, zamuyi magana gobe, Habib ku jirani a
wajen mota.”

 

“Muje Mahfuz.” 
Wani kallo yabi Musaddik din dashi, sannan ya juya suka bar wajen da
Habib.

 

Juyawa kan Musaddik yayi da ransa yayi masifar baci, ya shiga
bashi hakuri akan abinda Mahfuz din yayi, yace ya jirashi yana zuwa bari ya
sallame su. Yana barin wajen ya ciro waya, ya kira shi yana matsawa chan gaba.

 

“Akwai matsala.” Yana dagawa yace

 

“Ya fara suspecting dinka ne?”

 

“Be fara ba, wani banzan yaro ne bansan daga ina yazo ba,
yaso dole sai ya nuna masa gaskiyar mask da na saka…”

 

“Ya yadda?”

 

“Be yarda ba, kasan ya yarda dani sosai, so ba zai taba
kawowa ba. “

 

” You have to be very careful, shi kuma yaron zan san yadda
zan yi dashi. “

 

” Ok sir. ” Ya kashe wayar yana juyowa, sukayi ido
biyu da Moh da yake tsaye a bayan sa kamar mayunwacin zakin da ya shekara be ce
ba.

 

 

 

 

***Assalamu alaikum sisters, masu korafi naga wasu daga cikin
korafin ku, ina mai baku hakuri akan matsalolin da aka samu, dan gane da rashin
posting halin girma shekaran jiya da jiya, hakan ya faru ne sakamakon ciwon
hakorin da ya matsa min hade da zazzabi, wanda har ta kai ban iya samun duba
sakonni ba balle har na iya zaman rubutu

 

  Duk cikin zafafa biyar
babu wadda a cikin mu take jin dadi a duk sanda batayi posting ba, Allah ne
shaida ana iyakar kokari wajen ganin Anyi abinda ya dace. Sai dai idan abu ya
sha kan mutum a ba yadda ya iya. Allah ya huci zuciyar duk wanda ransa ya baci
ta dalilin jira ko wani abu, ba da gangan bane wani lokacin kuma ajizanci ne na
dan Adam.

 

Allah ya rufa asiri ya sa mu gama lafiya

2/21/22, 08:16 – Buhainat: Halin Girma

39

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

****

 

“Capt… Yaron nan ya bata min rai, ya za’a yi ya zarge ni
haka?”

 

Sassauta fuskar sa yayi, ya dafa shi

 

“Karka damu yarinta ce.”

 

“Naga alama, waye shi? Aina yake?”

 

“Bansan shi ba, abokin Habib ne I guess!”

 

“Amma ka barshi ya zage haka, naji ma kamar hausar shi bata
fita.”

 

“Eh, born and raised a UK ne, dole zaka ji banbanci,
anyways ya wuce na masa fad’a kuma.”

 

“Shikenan, yanzu menene next? Da ya kamata muyi?”

 

Daga kafada Moh yayi cikin halin ko in kula yace

 

“Babu komai for now, muna cigaba da addu’a.”

 

“Bari na wuce, I’m sorry akan maganar missing files din
nan.”

 

“Karka damu.”

 

Da kallo ya bishi har ya fice daga wajen, ya daga waya ya kira
waya, sukayi magana sannan ya kashe. A kalla Mahfuz ya zama wani haske a
binciken sa, kowa da yanayi da tsarin aiikin sa, ya san aikin sa sosai ya kuma
masifar burgeshi, he’s smart and intelligent daga ganin shi,kuma da yake akwai
banbancin yadda k’asar mu take da tasu sun fi mu skills da kayan aiki.

  Shugaban su ya kira, ya fad’a masa abinda ake ciki, ya
kuma tabbatar masa da zasu yi duk yadda zasuyi, a yanzu za’a binciki layin
mudassir din a nan za’a gane da wadanda yake waya, yana ajiye wayar ya kira
Ammi sukayi magana sannan ya kira Aji da yake ta avoiding kiran sa tun ranar,
yana dagawa kuwa ya haushi da fad’a akan kin daga wayar sa da yayi, hakuri ya
bashi kawai sukayi magana ya kashe.

  Bayan kamar awa daya aka kirashi, ya shirya a gurguje ya
fita cikin tawagar yaran matasan sojoji, kowanne a cikin su a kalla zaka gane
babu sauki a tattare dashi, bakin glass ne a fuskar Moh, baka ko ganin kwayar
idon sa. A wani waje suka hadu, ya tarar da taron jami’an tsaro birjik kowannen
su cikin shiri, babu kalar da babu na jami’an tsaro tun daga kan police, DSS,
civil defense, uwa uba sojoji. Gaisuwa ya dinga amsawa daga kananan ma’aikata
har ya karasa wajen manyan da suke kasan wata rumfa suna magana. Details din
bayanan da aka samu ta wayar Musaddik din suke dubawa, in da ya nuna babu wata
waya da yake yi illa da mutum uku, Moh din sai wata number da take kiran sa
kullum a private number sai kuma Samha Bello Turaki, da Kamal Abubakar
Santuraki

   Kansa ne yayi masifar daurewa, menene alakar
Samha a cikin case din? Karba yayi ya sake dubawa sosai ya tabbatar da abinda
yake a rubuce. Yasan Laila ce take son shi ba Samha da take kawarta ba,menene
akalar Samha da Iman dinsa da har za’a hada kai da ita a sace ta?be san dalili
ba,  abu daya ya yarda dashi, dukkan su anyi amfani dasu ne, domin a samu
galaba akan sa, su kuma idon su ya rufe, suna son ganin bayan  din suka
fadawa gadar zaran JABIR!

 

“Mun gabatar da duk binciken da zamuyi akan shi, mun kuma
tabbatar da ba Musaddik bane, yayi amfani da fuska ne, sannan yayi amfani da
wata na’ura da take kwafar murya, wadda take da masifar tsada Kuma alamu sun
nuna ya jima tare da kai, ba zaka taba ganewa ba idan har ba sani kayi ba,
Musaddik yana da kusanci da kai shiyasa har sukayi amfani dashi wajen samun
kanka, da weakness dinka, sai kuma dan uwanka  Kamal da suka taimaka musu
don cimma tasu bukatar da hadin guiwar Samha da bamu san wata alaka dake
tsakanin ku ba.”

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button