HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 4

Ad

_____

 

*HALIN GIRMA**_Hafsat Rano_*

4

****

*Adamawa-Yola*

Tun daga yanayin manyan motocin da suka cika harabar  ya tabbatar da bakin dake cike da fadar, yana da yakini dalilin kiran Bubun kenan a kalla zasu ganshi sannan ayi masa maganar da tafi komai kona masa rai, maganar mulki da yake dukkan kokarin sa wajen guje mata.

    Be jira an bud’e masa ba, ya balle murfin motar ya fito bayan hango Aji da yayi yana nufar ciki tare da tawagar sa, da saurin sa ya cimmusu,domin ya samu su shiga a tare, ko ya gujewa idanun Bubun daga zuwan nasa. Yasan a cike yake taf dashi

“Aji!” Ya kira shi da sunan da yake kiran sa

“Hoo d’an nema, na dauka ba zaka zo ba ai.”

” Na isa naki amsa kiran ka ko na Bubu? Ai ban isa ba.”

Ad

” Dadin baki, idan har da gaske ne ai sai ka amsa kiran da muka jima munayi maka ko?”

Sosa keya yayi ba tare da yace komai ba, suka karasa ciki. Da ido Bubu ya kafe shi tun shigowar sa, tabbas ya rame fiye da ganin da yayi masa kwanaki da suka wuce, sannan akwai wani yanayi a tattare dashi da be gamsu ba, a gabansa ya tare, ya kwashi gaisuwa ya cigaba da bin sa da idon ba tare da shi ya yarda sun hada ido ba, gefen Ajin ya samu ya rabe yana sake hade fuskar sa tamau, murmushi kawai Bubu yayi ganin da gaske Muhammad yake har yau yana nan akan bakan sa, ya rasa dalilin da ya saka shi baya son mulki ko kad’an, tamkar ba dan naga da ba, kamar wanda aka juyawa tunani kwata kwata akai, gashi da gaske yake jin ya kamata ace ya huta, yakamata ya karbe shi kamar yadda ya karbi Aji a lokutan baya. Sai dai d’an nasa sam be shirya hakan ba, abinda yasa yake dada jan lokacin sosai, burin sa kawai yasa a gaba tun bayan shigar sa jami’ah, in da ya kwallafa rai akan aikin tsaro, ya kuma samu cikar burin sa duk da ba hakan ne ya kasanci burin sa ba shi.

    Kamal ne ya shigo wajen, ya gaida kowa cike da girmawawa sannan ya samu gefe ya zauna yana fuskantar Muhammad din, kallon juna suka yi ba tare da wata magana ba, murmushi kawai Kamal din ya sakar masa wanda ya kasa maida masa domin ya san ma’anar sa, be damu ba ko kad’an, da ace Bubu zai ji shawarar sa da ya jima da yiwa Kamal din abinda yake muradi, amma shima kemaimai yaki, ya kwallafa rai akan Muhammad din, ko me yasa? Oho. Ya dage kafadarsa alamun baya da bukatar ya sani ma dai.

 Duk batutuwan da aka tattauna a wajen be tsinci komai ba, zuciyar sa ta lula chan zuwa in da ya baro, tunanin halin da take ciki ko abinda take aikatawa kawai yake har kusan kowa ya gama ficewa ya zama na daga shi sai Aji, da Bubu.

“Muhammadu.” Yayi firgigit sai kuma ya hau sosai kai yana murmushi

“Barka da rana Bubu.”

“Kalli shigar ka fa Muhammad, kalle ka? Hakan ya dace a matsayin ka da gidan nan? Haka kaga dan uwanka Kamal yayi shiga irin ta masarauta?”

“Wallahi Bubu garin sauri ne, kuma gashi ba wani iya nada rawanin nan nayi ba wallahi, infact ciwon kai wallahi yake sani, amma za’a gyara ba za’a sake ba.”

Murmushi Aji yayi me dan sauti, ya kalle shi yana sake fadada fara’ar fuskar sa.

“Ayi hakuri ranka ya dade munyi kuskure ba zamu sake ba.” A duk sanda irin hakan ta faru Ajin ne ke yin uwa yayi makarbiya ya hana ayi masa fad’a, hakan yasa ba kasafai Bubun ke korafi gaban Ajin ba, sai ya tsuke bakin sa kawai be sake cewa komai ba.

Tashi yayi, ya dan russuna a gaban mahaifin nasa

“Zan shiga ciki Bubu!”

“Ka same ni a shashe na bayan sallar magriba.”

” In sha Allah. A tashi lafiya.”

” Aji sai na shigo wajen yar tsohuwa ta.”

” Tana nan tana jiran ka da manshanun ta da yajin daddawa.”

Murmushi yayi, ya fice suka raka shi da ido. Yana fita Bubu yaja tsaki

” Na rasa me yake damun yaron nan wallahi, ace yaro ya taso a cikin abu amma sam ya tsane shi? Wannan wanne irin abu ne?”

” Mu cigaba da hakuri kawai Ahmadu, komai zai wuce ne.”

” Allah yasa, kowa jira na yake, mutanen gari da manyan mutane kowa ya zuba ido yaga me zanyi akai, ga Kamal da gaske yake son mulkin nan, gashi sam be chanchanta ba, na rasa yadda zan.”

“Shima ka barni dashi kawai, ayi masa abinda yake so din, yanzu dai a zaman da zakuyi sai kayi masa maganar auren muji, a kalla auren zai taimaka masa ya zauna a cikin mu, kaga dole ya koyi komai.”

” In sha Allah, idan ma bashi da yarinyar da tayi masa ni zan nemo masa.”

” Kul, Muhammad ba irin yaran da za’a yi musu haka bane, mu da muke son amfani da soyayyar shi ga yarinyar, abi dai komai a sannu.”

” Shikenan in sha Allah, Allah yasa mu dace.”

” Amin ya Allah.”

***Bangaren Ammin sa ya wuce, yana tafe yana amsa gaisuwar da ya tsana, ayi ta gaida mutum kamar wata tsiya, hakan na daya daga cikin abinda yake hada shi da gidan su, ya gwammace yayi guduwar sa waje daya kawai ba tare da hayaniyar mutane ba.

   Tana zaune ta dora kafarta a saman dan tumtum din dake falon, kafar na damun ta sosai shiyasa ko yaushe zaka ganta a mike ana dan mammatsa ta. Yana tura kofar duk suka mike, har rige rigen gaishe shi suke kowa yasan yadda Ammin ke masifar ji da tilon dan nata, mace me kirki da sanin yakamata, shiyasa ta karbe kowa a gidan daga ma’aikata har dangi kowa nata ne, wajen Bubu ma Itace star,itace kuma uwar gidan sa dan dai Allah be bata yawan haihuwa bane.

Ad

_____

1 2 3Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button