HALIN GIRMA 4

“Welcome welcome.” Yace masa yana juyawa suka shiga ciki. Da sauri Mama ta fito jin hayaniyar su..
“Wa nake ji kamar Khalil, inyee lallai yaron nan Ashe dai da gaske kake.”
“Gani dai, ai dama na gama shirin zuwa kawai ban sanar dake bane sai jiyan.”
“Maraba lalle da manyan yan jarida.”
Zama yayi a cikin kujerun falon, itama maman ta zauna tana gyara dan kwalin kanta.
“Wai dama kinsan zaizo Mah?”
“Nima sai jiya na sani, na zata kuma halin nasa ne Ashe da gaske yake shiyasa ma ban fad’a ma kowa ba.”
“Ina wuni Anty?”
” Lafiya lou Khalil, yaso Hajiya da kowa da kowa?”
” Duk suna nan lafiya, itama tayi mamaki da nace zanzo, gashi kuma zan dade sosai dan aiki ne ya kawo ni.”
” Ahaap ko da naji, Ashe zuwan dai da dalili, jairi dama nasan akwai abinda ya kawo ka.”
” Abubuwa dai Anty, karki manta da wannan maganar tamu hadda ita ma.”
Tsaki taja ta harare shi
” Zaka fara ko?”
” Nayi shiru.” Yace yana dora hannun sa baki
” Yafi maka dai.”
” Ina su Zeenat ne? Banji duriyar su ba.”
” Zaka ji su ne ai ba dai kananan ba, ka tashi ku shiga ciki ka huta kaci abinci, sannu da zuwa.”
Tashi yayi, yabi bayan Habeeb suka wuce dakin sa suna hirar yaushe gamo, idanun sa da kunnuwan sa na jiran yaji ta inda zasu bullo, he can’t wait to see her beautiful face, ko me Anty zatayi masa kuwa ba zai fasa bawa zuciyar sa abinda ta dade tana so ba. Kishin ta daban soyayyar sa daban. Period!
****Zaman ta a bangaren Gajin yafi komai yi mata dadi, abu daya ne kawai yake dan takura ta yawan maganar Gajin, duk da haka take daurewa tana amsa mata, gashi ta manta wayar ta a kitchen bayan ta gama wankin nan, gashi taji alamar Khalil din yazo ta tabbata idan taje dauka zasu iya haduwa, ta kuma san me hakan ke nufi a wajen Mama.
Zaman ta ta cigaba kawai har sanda taji ana kiran sallar, alwala tayi ta zauna ta jira a tayar, tana jin sanda za’a tada sallar ta fita zuwa bangaren nasu, lokacin tasan sun tafi sallah Maman ma kuma ta shiga ciki tayi sallar itama, ta baya ta bi, ta shiga kitchen din a daidai lokacin da ya saka wayar a kunnen sa
“Waye?”
Yace yana gyara rikon da yayi wa kofin hannun sa, tashi zaune Moha yayi da sauri, ya kalli screen din wayar ko be kira number daidai ba? Kai Anya? Daidai yadda ta fad’a masa ne
“Fatima nake nema, ko tana kusa?” Yace jin me maganar ya sake tambayar waye a karo na biyu.
“Fatima? Malam Waye kai din da kake neman ta?”
“Sanin waye ni ba zai taba maka dadi ba, idan tana kusa ka bata zanyi magana da ita.”
” Ba zan bata ba, abun yar karfi ne kazo ka karba idan kana dashi, mtsw.”.
Yaja dogon tsaki hade da kashe wayar, kafar ta ta sako a kitchen din zata shigo domin ta karbi wayar ta da ya daga mata ba tare da izinin ta ba, muryar Mama ta dakatar da ita, ta juya da sauri ta bar kitchen din.
” Kai kuma me kake anan kana jin an tada sallah?”
“Ruwa nazo sha.”
Yace yana juyawa ya bar kitchen din, kofar bayan ta leka ta tabbatar babu komai a wajen, tayi kwafa ta juya bayan ta jawo kofar ta ciki.
Wani irin tashin hankali ne ya ziyarce shi, ya tashi da sauri yana jawo dayar wayar tasa, cikin kankanin lokaci ya birkice ya koma Captain Moh din sa na ainihi, a yau ba sai gobe ba zai juya, dan ba zai taba daukar rainin hankali ba, ba dan ganin da zai wa Bubu ba, da babu abinda zai hanashi daukar hanya a yanzu, amma dole ya hakura zuwa lokacin da ya dauka masa duk da yana ganin yayi masa masifar nisa.
Kaiwa da komowa ya dinga yi a tsakanin dakin, zuciyar sa tamkar zata hudo daga kirjin sa saboda tsabar kishi.
_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR ????????????????sune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL???????? Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA????????hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA????????billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA????????miss xoxo_*
*_ƊABI’AR ZUCIYA????????huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2????????400
3????????500
4????????700
5????????1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107sex
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*????????????????????????????????????????
#team zafafa biyar
****
[ad_2]