HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 6-10

“Bakwa ganin idan iyayen yaron nan suka san in da yazo
neman aure zasu kyale shi, duba da mu din ba wasu bane akan irin girma da
nasabar gidan da ya fito.”

 

“Idan har a yadda bincike na ya nuna min ne, iyayen sa basu
da matsala masu son talakawan su ne, dan haka muyi addua kawai in sha Allah
alkhairi ne.”

 

“Shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi,.”

 

“Yanzu kayi magana, Amin ya Allah.”

 

” Ina neman alfarma daya, da mu bar maganar nan a tsakanin
mu zuwa muga abinda Allah yayi.”

 

” Hakan yayi, Allah ya shige mana gaba.”

 

Suka hada baki a tare, sai kuma suka shiga wata hirar tunda
daman su dan dade basu yi irin wannan zaman ba, anan duk suka ci abinci a tare
sannan kowa ya tafi zuwa sabgar sa. Aka bar Yaya a zuwan zai kira Muhammad din
da daddare ya sanar dashi ya bashi izinin yazo yaga Fatiman su daidaita, da
daddaren bayan ya gama komai ya turawa Muhammad din text message akan ya cigaba
da zuwa. Muhammad na zaune shi da Musaddik suna kallon video da ya saka akayi
wa Khalil suna kwasar dariya text din ya shigo, tashi yayi ya daka tsalle kafin
yace

 

“Yess!!!

 

” Ya akayi?”

 

” Karfe nawa yanzu?”

 

Yace yana kallon agogon falon

 

” Opss Ashe dare ya fara, ba dan ba dan ba da yanzu zanje
na ganta, amma ba komai kafin na wuce Abuja zan tsaya na fara ganin ta.”

 

” Me faru wai.”

 

” Karanta!” Ya mik’a masa wayar

 

” Ah congratulations angon fatiti, Allah ya tabbatar mana
da alkhairi.”

 

Rik’e k’ugu yayi yana hararar sa

 

” Allah ka sake bata mana suna sai na saka frog jump, kaji
ma na ratse.”

 

” Kut! Allah fa ka raina ni Moh, komai sai kace zaka sani
frog jump an fad’a ma nima kamar wadanchan dogs din naka ne na bakin
gate.”

 

” Ka dai kula, kana magana ne da Captain Muhammad Ahmad
Santuraki, Captain Moh!”

 

” Whatever, ni dai muhammadu na sani, ba wani bragging da
zaka min.”

 

” Zaka gane ne idan na dauke ka na je na jefa wa mayunwatan
zakunan nan na barack, ba zaka sake kiran sunana gatsal ba.”

 

” An gaya ma kowa irin khalil ne? Lusari!”

 

Dariya suka saka Muhammad ya shiga gwada yadda Khalil din yake,
suka sake tuntsurewa da dariya suka tafa

 

” Ashe farar kura ce a wajen, sai uban cika baki dan iskan
yaro, gobe ma ya sake, naso ka dan saka su sun sassama masa jiki
wallahi,.”

 

” A hakan ma nasan sai sunci zalinsa ai.”

 

” Wicked soul!” Yace yana dariya

 

” Naji, bari naje na kira Baby na, naji voice dinta me dadi
kafin gobe naje na ganta, dan yanzu ina da license, na matsu na ganmu tare,
muna yawo a garin nan cikin mota my hands in to her’s, ga cool music na tashi
Malam, wow love in the air.”

 

” Toh Mr Romeo, Allah ya kaimu dai zamuyi kallo, yadda kake
son ta Allah yasa tana maka ko rabin sa ne.”

 

” I don’t care, as long as munyi aure, zan koya mata yadda
zata so ni.”

 

” We shall see.”

 

***Ruwan zafi ne a katon bawo, Khalil na zaune a gaban ruwan
hajiyar su na danna masa bayansa, gaba daya jikin sa ciwo yake kafarsa kamar
zata cire yake ji, babu irin tambayar da batayi masa akan me ya same shi ba
amma yaki fad’a mata, haka Mama ta bugu tana fad’an tafiyar Khalil din hajiyar
ta fad’a mata a yadda ya dawo, kuma yaki cewa komai. Yana jin su har suka gama
ya tashi ya koma dakin sa ya kwanta yana tariyo abinda ya faru cikin tausayin
kansa. Shi ya jawo yana takama da shegen bakin sa ya je ya kaishi ya baro, dama
an fad’a mutum ya kiyayi harshen sa, akwai hadisi guda da akayi magana akan
harshe da kiyayar sa, yaga izina a kansa, gashi bashi da damar fadawa wani
abinda ya faru domin yasan shi za’a yi wa dariya, ko da muhammadu a iya soja ya
tsaya matsayin da yake kai ya isa ya taka shi son ransa ba kuma wanda ya isa
yace dan me? Balle ganowar da yayi waye Muhammad din, anan ya gane bakin rijiya
ba wajen wasan yaro bane, shi din ma ganganci ne da kuruciya. Eh toh kuruciya
mana tunda dai yasan a girme Muhammad din zai girma shi dole ya fishi hankali
da komai. Abu daya ne zai hana shi walwala, yadda zai yi da tarin soyayyar ta,
gashi yayi masa kashedin ko a hanya babu shi babu ita, ya kuma tabbatar idan
har ya kuskura yayi wani abu, za’a iya neman shi ma baki daya a rasa, dan masu
kudin nan yasan ba wani abu bane a wajen su su batar da mutum bat, har abada a
daina jin labarin sa.

   Tagumi ya rafka yana jin kamar yayi ta kurma ihu
ko yaji sassaucin radadin da zuciyar sa ke masa. Allah sarki Khalil 😂

1/9/22, 10:17 – Buhainat: Halin Girma

    10

 

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi
08184017082 or 09134848107* 

 

I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my
photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb

 

 

***Be ji sallamar ta ba, sai ganin ta yayi kawai a dakin bayan a
zahiri tayi sallamar amma saboda baki daya hankalin sa na ga tunani shiyasa be
ji ba sam.

 

“Ya Khalil wai a kawo maka abinci…”

 

Ai kafin ta karasa ya daka mata uwar tsawa

 

“Uban abincin, dallah Malama karki dame ni.”

 

“Toh… Me yayi zafi? Hajiya ce ta aiko ni ai.”

 

“Fitar min daga daki!” Yace yana tasowa, da gudu ta
juya tana dariya, sai da ta ga ta fice sannan ta daga murya tace

 

“Bani na kar zomon ba…”

 

Ransa ne ya sake baci, ya bigi kofa yana komawa ya fad’a saman
katifar sa yana jin kamar yayi ta cizon kansa.

 

A falo ta samu Hajiya ta zauna tana haki

 

“Allah ya taimake ni na kusa cin duka, daga tambaya kawai
ya hayayyako min Hajiya.”

 

“Toh wai ko dai Khalil tsokana yayo ne aka tattaka shi,
kinsan fa Khalil ba dai tsokana da cika baki ba.”

 

“Alamu dai sun nuna Hajiya, fad’a ya takalo da yafi karfin
sa wallahi, gashi nan yaki fad’an abinda ya faru.”

 

“Toh Allah ya kyauta ” Hajiyan tace tana tashi ta fita
zuwa dakin nasa.

 

***Tana tsaye a bayan kitchen dinsu, wanki ta gama tana ta sauri
saboda kwana biyu bata maida hankali zuwa islamiyya saboda abubuwan da suka
sako kai, tana wankin tana tunanin maganar da sukayi da Abba da ta zama tamkar
bitar karatu haka take yin sa, takun tafiya taji, ta juyo sai taga Abban a
tsaye yana duban ta, da sauri ta dan russuna,

 

“Abba sannu da zuwa.”

 

“Wanki ake ne?”

 

“Na’am.?” Tace tana zaro ido sanin cewa ba da sanin sa
take wankin ba, musamman ya samu almajiri yake wanke musu kaya ita da Zeenat da
Marwan yake biyan shi ta hannun Mama, duk da yasan dole zasuyi wanki irin kayan
ciki da abubuwan da ba za’a iya bawa me wanki ba, amma kuma tarin kayan da ya
gani a wajen da ya gane na Marwan ne sai wasu na Maman ya saka ransa mummunan
baci, har a jiya sai da Maman ta karbi kudin wanki a wajen sa da zumar yau me
wankin zaizo karbar kudin sa ya kuma bata babu musu. Yanayin sanyin garin zai
yi wuya wajen wanki musamman da tun da dadewa yasan fatar Iman din bata son
wahala idan tayi wanki hannun ta kanyi ja sosai, shi kuma Allah ya hore masa
son yaya Kuma gasu ba wai yawa ne dasu ba shiyasa duk wani aikin wahala baya
son siyi duk da ba wai kwata kwata ba zasuyi komai ba, amma kamar wanki yana
ganin be kamata shima a saka shi a cikin aikin mata ba, mata na wahala da aikin
gida kula da yara da girki wankin aka dauke musu zasu samu sassauci. Matsowa
yayi ya sake leka kayan kafin ya girgiza kansa ya juya bayan yace

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button