HALIN GIRMA 6-10

“Ki bar wankin nan kizo ki wuce ciki.”
Sakalo tayi a tsaye tsoro na kamata
“Bakya ji ne?” Ya daka mata tsawa, da sauri ta bi
bayansa har cikin gidan, dakin su taga ya wuce ya kwankwasa sannan ya tsaya
“Waye?” Zeenat tace tana daga kwance cikin rufa, a
yadda tayi maganar zaka gane knocking din ya takura ta, sake kwankwasa wa yayi
sannan ya tura kofar da sallama, be shiga ba, ya tsaya a kofar yana karewa
dakin kallo, gadon zuwa katifar dake shinfid’e a kasa da ta tabbatar masa da ta
Iman din ce. Tuna lokacin da ya bada kudin gadajen nasu yace a siyawa kowa nasa
amma sai Mama tace daya ya ishesu me dan girma saboda hakan zai sake shakuwa
tsakanin su,da wannan yayi amfani a ganin sa hakan ne ya kuma dauki hakan a
matsayin soyayyar da Maman ke wa yar tasa. A yadda yake jin zuciyar sa a lokacin
zai iya yin komai, sai kawai ya fice daga gidan gaba daya ba tare da ya koma
daki ba.
Tsoro ne ya kama Iman
musamman da bata san me zata ce wa Maman ba akan wankin, shiryawa tayi cike da
fargaba ta tafi makarantar tana fatan koma menene ya taso ya zama daidia kafin
ta dawo dan a rayuwar ta, ta tsani tashin hankali ko kad’an.
Rabi da kwata bata gane
kan karatun ba, haka dai ta taho gidan tana ta zulumi, tana shigowa ta ganshi a
tsaye ya harde hannayen sa a gadon bayan sa yana kallon kofar shigowar. Shigar
jikin sa ta bi da kallo zuwa gyaran da yayiwa fuskar sa, murmushin da ta gani
kwance a fuskar tasa, ya saka ta samun nutsuwa har ta karaso wajen da yake a
tsaye.
“Ashe kina kusa da shigowa, naji a jikina.”
Murmushi tayi kafin tace
“Sannu da zuwa.”
“Yawwa, ya hanya?”
“Alhamdulillah wallahi.*
” Akwai wanda ya kalleki da kina tahowa? Idan akwai fad’a
min naje na same shi.”
Sosai ya bata dariya,
” Kai… Babu kowa fa, ya gida yasu Mama?”
” Mama? Ammi muke ce mata, tana nan lafiya tace ma na
gaishe ki, na gaida wacce ta kwace mata yaronta kafin tazo haka tace.”
Rufe fuskar ta tayi tayi yar dariya
” Allah sarki, ina amsawa nagode.”
” Itama ta gode, tace ta matsu ta ganki.”
“Watarana zata ganni in Sha Allah.”
“In Sha Allah, very soon.”
“Abba Babba yace idan kazo ka shiga ciki.”
” Da gaske? Kice na zama dan gatan Abba.”
Dariya tayi
” Naga alama kam, Abba ya yarda da kai sosai.”
” Allah sarki, ai yana da kirki sosai.”
” Sosai.” Tace
” Bari na bud’e maka, chan ne seat room din sa.”
” Owk.” Yace ya harde a jikin ginin yana kallonta, har
ta bud’e ta dawo sannan ya bita a baya yana admiring steps dinta zuwa ciki.
A kofar dake farkon
kofar ya zauna ita kuma ta shiga ciki, yana zama Aliyu ya shigo da ruwa a tray,
ya ajiye ya gaishe shi sannan ya fita, ruwan ya dauka ya sha sosai sannan ya
kalle ta, gefe take kallo tana wasa da jikin kujerar da take kai.
” Zahraah, tafiya ce ta kamani, ba zan iya wucewa ban sanar
miki ba, ba wani dadewa zan ba in sha Allah, inaso kafin lokacin da zan dawo mu
sake fahimtar juna sosai, idan na dawo sai a shigo da magana me karfi, bana so
a ja lokacin.”
” Allah ya kiyaye ya tsare, ya dawo da kai lafiya.”
” Amin ya Allah, Amin Amin Zahraah Nagode”
Shiru ne ya dan shiga tsakani, shi yana kallon ta yana sake
ganin ainihin kyawun ta, ita kuma ta tafi tunanin Allah yasa ya dawo din kar
taji shiru idan ya tafi, har zuciyar ta bata son tafiyar tasa, amma kuma ya
zatayi? Ba zata hanashi ba ai.
“Ina wannan yayan naki da muka hadu ranar nan? Har ya korar
min ke?”
” Uncle Khalil?” Tayi dariya
” Auw sunan shi kenan.”
” Eh kanin Mama ne, a nan gidan ya taso kafin ya koma
gida.”
Gid’a kansa yayi kamar be sani ba
” Shiyasa ya nuna min iko kenan.”
” Uhum.” Tace kawai bata ce komai ba.
“Yana ina kuwa?”
“Kamar dai ya koma, naji dai mama na fad’an ya tafi be
sanar ba.”
“Ai be isa ya sanar.”
“Na’am?” Tace tana kallon sa
“Sorry ba komai.” Ya maze kamar be ce komai ba, be san
maganar zata fito ba shima.
” Bari na gudu, kar nayi rana.”
Mikewa tayi
” Daga nan zaka wuce?”
” Eh gaskiya, idan na koma gida na koma baya.”
” Ok ina zuwa.”
Ta fita ya tashi ya dan zagaye falon yana observing komai na
ciki, yana tsaye jikin wani frame ta shigo dauke da leda ta mika masa tana dan
russunawa
” Gashi ka kaiwa Ammi, ina gaishe ta.”
Rik’e ledar yayi yana kallon ta, tayi saurin dauke kanta k’asa
ta sakar masa ledar gabanta na faduwa.
” I love you.”
Ya samu kansa da whispering cikin muryar da tayi masifar shigewa
ciki, wani irin feeling taji, sarai ta jishi sai tayi kamar bata ji ba, ta ja
baya sosai tana diriricewa, shi kansa wani iri yake ji, be taba tunanin haka
daga gareta ba, da tasan yadda Ammi take a wajen sa, da kuma yadda sakon nan
yayi nasarar kara masa son ta ninkin ba ninkin, da tun ranar da ya fara zuwa
tayi, kasa matsawa daga in da yake yayi, sai murmushi yake shi kadai.
“Nagode sosai, Ammi ta gode.”
“Ba komai.” Tace tana jin nauyi da kunyar yadda yayi
“Zan tafi, ki kula da kanki kinji? Karki yarda wani ya bata
miki rai, kin fi karfin haka, ke din ta daban ce, ta musamman ce.”
“In Sha Allah.” Tace tana jin dadi , a kalla idan tana
tare dashi tana jin cewa itama tana da yanci, sannan takai matsayin a so ta.
Ta cikin idon sa yake ta
kokarin aika mata da sakon sa, sakon da yake so ya tafi ya bar mata, irin me
zafin nan da zatayi wuyar dauke shi daga tunanin ta, sau daya ya samu nasarar
aika mata da sakon, ya kuma je a yadda yake so, sai ya marairaice mata fuska
yana jijjiga kansa.
“Allah ya kiyaye Allah ya kaimu lafiya.” Tace da sauri
ta bud’e kofar kuusa da ita ta fice ta bar shi a ciki, dariya sosai ya saka, ya
sake rik’e ledar hannun sa gam gam, ya fice yana jin sa tamkar yana yawo a
cikin gajimare.
A kafa yake tafiya rik’e da ledar, iska na kada shi, sam baya
jin komai baya ganin kowa sai tsadadden murmushin sa, shi kadai yasan yadda
yake ji a lokacin, shi ya saka shi tafiya kawai ba tare da ya neme su ba. A
chan bayan layin da suka saba haduwa suna tsaye tana masa mitar kwana biyu be
zo ba, hakuri yake bata akan wata tafiya ce ta taso masa Muhammad din yazo
wucewa
“Kaga saurayin Iman.”
Tace da sauri tana nuna masa shi. Wani kallo Bashir yayi masa
daga nesan kafin yayi saurin juya bayan sa, yayi saurin bud’e motar ya shiga
ciki, yayi kamar yana neman wani abu a ciki
“Baby me kake nema? Fito ku gaisa da Malam mana.”
Kin fitowa yayi ya cigaba da bud’e dashboard yana rufewa,
“Assalamu alaikum.” Moh yayi musu sallama yana karewa
motar kallo.
A wani yanayi Bashir ya fito bayan nacin da Zeenat din tayi
masa, ya diririce ganin Moh din
“Sannu ko?” Moh yace masa yana mika masa hannu
“Sunana Muhammad, kaifa?”
Yace masa, a sakale Bashir ya miko nasan hannun kamar me tsoro
cikin rada rada yace
“Bashir.”
“Yayi Bashir, sai anjima.” Ya wuce ba tare da yace
komai ba. Dariya Zeenat ta saka
“Shi wannan din kika ce shine zai auri Iman?” Yace da
sauri
” In Sha Allah, baka ga sun dace ba? Ko baka ga yanayin su
daya bane?”
” A haka yake tun zuwan sa gidan kuma?
“Babe me ta faru?”
“Noo noo babu komai.”
“Naga duk ka damu ne, me ya faru?”
” Ah babu komai, kawai na ganshi haka haka ne.”