HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 6-10

_”You don make me fall in love, you don make me fall in
lov, Baby I love you.”_💕

 

Dariya sosai Musaddik ya saka

 

” JJC kawai, zaka cika mana kunne da wata wakar ka.”

 

“Idan fitsari abin banza ne, kaza ma tayi mana?”

 

“Okh haka ne, shikenan ai.Wait and see. Ni yanzu ba wannan
ya kawo ni ba, me yasa ka saka aka dakatar da gayen nan ne?”

 

Tashi yayi rik’e da cup din yana bata fuska

 

“Kaga dacewar ya nemi irin abinda nake nema?”

 

“Kamar ya?”

 

“Ba’a takara da Sarki, be chanchanci karawa dani ba, bashi
da qualities din da zai iya neman auren ta, cika bakin sa ya saka na nuna masa
iyakar sa, anyways warning ne kawai, zan sake gwada hankalin sa , idan yayi
hankali fine, idan be ba kuma sai muje a haka, sai a karbi application din
wasu.”

 

Gid’a Kai Musaddik yayi be sake cewa komai ba, yasan waye Moh,
yasan bashi da matsala ta kowanne bangare, amma bashi da dadi idan har kayi
crossing din sa, zai nuna maka shi din babba ne a cikin manya!

 

“Ka fahimta dai ko?”

 

“Yes Captain!” Ya mike sannan ya sara masa.

 

“Aje waya!” Yace masa suka kwashe da dariya a tare.

 

HALIN GIRMA

 

Hafsat Rano

 

 

WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

 

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da
wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na
MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

 

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu
dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma
kasan cewa tafiyar ta dabance_*

 

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN
NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

 

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

 

*_DEEN MARSHALL👉🏾
Mamuhghee_*

 

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat
rano_*

 

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn
abdul_*

 

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss
xoxo_*

 

*_ÆŠABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

 

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ÆŠAI ÆŠAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU
AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

 

2👉🏾400

3👉🏾500

4👉🏾700

5👉🏾1000

 

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

 

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

 

08184017082

 

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE
DA SHAIDAR BIYANKU*

 

09134848107

 

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽

#team zafafa biyar .

 

___________

1/6/22, 17:52 – Buhainat: *HALIN GIRMA*

 

            7

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi
08184017082 or 09134848107* 

 

I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my
photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

***

Kukan ta ne yake karuwa Mama na tsaye a kanta, ta ja tsaki tace

 

“Bana son shirman banza kina ji na? Akan namiji zaki zauna
kina rafka wannan kukan kamar uwarki ce ta mutu ko ubanki?”

 

“Mafita nake so mu samawa kanmu, saboda anga zaki huta
shine aka shiga aka fita ake so ayi mana bakin ciki, idan ba haka ba, me ya
kawo wadannan zantukan?”

 

Cikin kuka tace

 

“Wallahi Mama nasan Iman ce taje ta samu Gaji da maganar
tunda dama ita yace yana so ai, shine dan taga wanda yazo wajen nata talaka ne
shine zata min bakin ciki, toh wallahi babu wanda ya isa ya hanani auren
Bashir, naji na gani kowanne hali ne dashi.”

 

Shiru Maman tayi tana kallon yar ta ta, idan har ta bari maganar
ta sha ruwa akwai matsala, sanin cewa Zeenat din ba wani farin jini bane da
ita, dama dai jamaar Iman din ne tun farko take sanin yadda zatayi, dole ta san
abinda ya kamata amma duk da haka ba zata nunawa Zeenat din komai ba

 

” Kina jina? Ki tashi ki tafi dakin ku, ki daina wannan
kukan tunda ba ubanki bane ya mutu, zan san yadda zanyi komai ya
daidaita.”

 

Da bayan hannun ta ta goge kukan, ta fice tana rangaji, tana
sake kudurewa a ranta babu gudu babu ja da baya a auren ta da Bashir din.

 

  Tana isa daki ta tarar da missed calls din sa, ta bi
kiran da sauri tana sake daidai ta kanta.

 

” Gani a waje.” Yace tana dagawa.

 

” Mu hadu a bayan layi akwai matsala karka zo gida.”

 

” Me ya faru?” Yace a kidime.

 

” Babu komai gani nan zuwa.”

 

Kashe wayar ta, tasan zai ta tambayar ta menene gwara kawai taje
suyi magana su sama wa kansu mafita dan ba zata iya hakura dashi ba.

 

Ficewa tayi ta kofar kitchen bayan ta gyara fuskar ta, ta bar
gidan cikin sauri tana tsoron haduwa da Ya Habib ko wani.

  A chan bayan layin ta hange shi jikin motar sa, a tsaye
yake yana ta jijjiga jikin sa daga gani baya cikin nutsuwar sa, tana isa ya
juyo da sauri.

 

” Lafiya baby?” Yace yana riko hannun ta. Kuka ta saka
da sauri yace

 

” Na shiga uku, me ya faru?”

 

” Abba ne yace wai na rabu da kai, wai yayi bin…”

 

” Shisshsh…” Yace da sauri yana dora hannun sa a
saman bakin ta

 

” Kinsan dai hakan ba gaskiya bane ko? Sharri akayi min ko
menene akace domin a hana mu aure, duk wanda ya yi min wannan sharrin na bar
shi da Allah kawai.” Yace yana girgiza kansa

 

” Shikenan yanzu rabuwa zaki dani? Nasan rayuwata shikenan
ta kare, idan har zaki iya yarda mahassada su shiga tsakanin mu, bakya so na
baby, rayuwata shikenan ni.”

 

” Ni ban yarda da duk abinda akace ba ai, kawai sharri ne
na sani, amma ya zanyi da Abba? Bayan shi din kaifi daya ne akan maganar
sa.”

 

” Dan Allah Zeenat karki yarda a raba mu, wallahi Ina sonki
, bansan ya zanyi da rayuwa ta ba idan har baki aure ni ba.”

 

Hawaye ya fara yi tayi saurin sa hannu ta goge masa

 

“Zanyi duk yadda zanyi, ba zan bari a raba mu ba…”

 

” Da gaske? Kinyi alkawari?”

 

” Nayi maka alkawari.”

 

” Dan Allah karki saba alkawari dan Allah, ki taimaka wa
rayuwa ta, kinji?”

 

” Karka damu.” Tace tana jin wani karfin zuciya,

 

” Ba zan taba yarda su yi min abinda bana so ba, Kai nake
so kuma duk yadda kake ina son ka a haka.*

 

“Nagode nagode baby, in sha Allah ba zakiyi dana sanin
amincewa dani ba.”

 

Zatayi magana wayar sa tayi kara

 

” Sorry.” Yace mata kafin ya daga yana rage volume din
wayar sosai

 

” Malam tun dazu nake jiran ka, ka dawo min da mota zan
fita, wai ina ka tsaya ne?”

 

” Gani nan yanzu in sha Allah.”

 

Ya kashe kiran ya ce

 

” Baby bari naje, urgent call daga Baba, zamuyi waya
kinji?”

 

” Tam shikenan.” Tace a sanyaye

 

” Yawwa ga sakon ki…” Ya bud’e murfin motar ya fiddo
da ledoji, hannu tasa ta karba tayi godiya, ta juya ta soma tafiya shi kuma ya
shiga motar ya tada ita da sauri ya bar wajen, yasan ba zasu kare kalou ba da
ita, amma kuma hakan shine kadai zai kankaro masa mutuncin sa.

 

***Daki ta koma ta ajiye ledar bayan ta bud’e taga ice cream ne
da Pizza, sai charger waya da yake ta lalace ta ta, sai wasu tarkachen alawoyi.
Bata taba komai ba sai charger din ta jona wayarta a jiki sannan ta fice zuwa
bangaren Gaji dan ta samu Iman a yi wacce za’a yi.

   Iman din ce kuwa kadai a falon tana karanta
hisnul muslim. Sai ganin mutum tayi a kanta, bata tanka mata ba ta sauke kanta
ta cigaba da karatun ta kawai.

 

“Saboda kina bakin ciki kin samu fakiri talaka shine zaki
kai munafurci kice Bashir bashi da hali ko?”

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button