HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 6-10

“Wacce irin magana ce wannan Zeenat?”

 

” Malama karki pretending kaman baki sani ba, idan bake
kika fad’a ma Gaji wata magana akan Bashir ba waye ya samu Abba ya fad’a masa
Bashir bashi da hali me kyau?”

 

Tashi tayi zaune tana kallon ta, ta girgiza kanta kawai kafin
tace

 

” Kinsan bani da lokacin batawa akan irin wadannan
maganganun, dan haka please bana son maganar.”

 

” Zaki ce bakya so mana kina min bakin ciki, toh wallahi
sai dai ki mutu da bakin ciki amma aure na dashi babu fashi, kije chan kiji da
wanda zaki aura, mutum kamar shi ya kawo talauci duniya.”

 

Tashi kawai tayi ta bar falon zuwa bedroom din Gaji dan ba zata
iya irin wannan shirmen na Zeenat ba, sai dai da gaske maganar ta taba ta, har
taji ta rasa gaba daya walwala da farin cikin ta, kwanciya kawai tayi ta rufe
idon ta tana hasaso rayuwar ta nan gaba!

 

***Cikin shigar Khaki pants da wata jibgegiyar rigar sanyi da ya
saka a saman armless rigar sa ya fito, kansa da yake a kwance yasha gyara ya
tsaya yana sake dubawa a katon mudubin da yake ajiye a falon, yasan Takawa zai
saurare shi ya kuma bi abinda yake so sai dai baya son ko kad’an karya ko wasa
ya shigo a cikin maganar auren sa. Kallon kafar sa yayi, sai ya koma ya sauya
takalmin zuwa wani daban sannan ya fice yana tura hannun sa cikin aljihun dogon
wandon nasa.

   Suna tsaye k’yam suna jiran fitowar sa, kowanne
su cikin shigar da take nuna shi din waye, bud’e masa motar akayi da sauri ya
fad’a yana makala bakin glass din sa yasan yau zai same shi a wajen hutawar sa,
in da ya dace da maganar da zasu tattauna, shiyasa ma yayi shigar sa da yasan
Takawan bazai masa surutu ba, dan ya riga ya san shi, ko yace kowa ya san shi
da tsanar manyan kaya musamman a lokacin zafi sai yace wai takura masa suke.

   Da yake sun san in da zasu, kai tsaye suka wuce
dashi Family house din, in da Takawan ke hutawa a duk ranaku irin wannan ba
tare da shigowar wani shaani na mulki ba. Iyakar abinda ya shafi kansa da
iyalin sa kawai yake tattaunawa a rana cikin saukakakkiyat shiga da ba zaka
taba cewa sarki bane duba da ko yaushe yana nannade cikin rawani da manyan
kaya.

   A kofar wajen motocin nasa suka tsaya, ya balle
murfin tare da me bud’e masa ya fito yana kallon ko ina na harabar gidan. Kansa
sanye da hular sanyi ya cire glass din idon sa ya shiga takawa zuwa ciki.
Gaisuwar da ya tsana ya dinga kokarin kaucewa har ya dangana da inda takawan
yake ya hange shi a zaune a cikin wajen yayi matashi da pillow yana kallon
yadda yan yaran da suka kasance jikokin sa ke wasa a wajen.

   Sarkin dogarai ne ya fara ganin shi,ya washe
cikin farin cikin ganin shi yace

 

“Maraba da Yarima!”

 

“Sarkin dogarai…”

 

Muryar sa ta saka takawa d’agowa, ya gyara daga gishingid’ar da
yayi, ya fad’ad’a fara’ar fuskar sa da tayi ma Moh iso har gaban kakan nasa.
Russunawa yayi cikin girmamawa ya kai gaisuwa, hannu ya mik’a masa ya matso
kusa dashi sosai, ya shafi saman kansa

 

” Sai yau kaga damar leko ni ko Muhammadu?”

 

” Tuba nake Takawa, ayyukan ne suka yi min yawa.”

 

” Toh madallah, naji kace kana son gani na, toh gani ya
akayi?”

 

” Dama magana ce akan abinda Bubu yayi maka magana.”

 

” Auren ka? Jairi toh sai akayi yaya?”

 

Dariya ya saka sosai

 

” Toh kunce sai nayi aure yanzu kuma nazo da maganar kuma,
sai na fasa auren ma gaba daya.”

 

” Fasa mana, waya yayi asara? Kaji dan nema.”

 

Dariya suka saka a tare, kafin Takawa yace

 

” Toh sai ka fadi a inda yarinyar take ko? Idan yaso sai a
nemi iyayenta.”

 

” A ah ni dai Takawa, ayi min aikin gafara a bari a samu
wasu suje su nema min auren ta.”

 

” Wasu?” Yace yana kallon sa

 

” Eh a dangi haka ba, ba manya sosai ba, Ina nufin ba cikin
manyan masarauta ba, yan chan kasa kasan dai.”

 

” A wanne dalili?”

 

” Kawai ni bana so suji tsoro su ga kamar mun fi karfin
su.”

 

Girgiza kai Takawa yayi

 

” A neman aure babu boye boye Muhammadu, a sak dinka zaka
je, kai ne fa jika na farko a gidan nan, sannan a wajen mahaifin ka, wanne irin
tunani ne haka ya shiga kanka?”

 

Sosa kai Moh yayi yana marairaice fuska

 

“Ni dai dan Allah takawa, a bar wasu suje.”

 

“Sam sam kaima kasan hakan ba mai yiwuwa bane, dole ne su
san kai din daga gidan da ka fito.”

 

Shiru yayi yana jin kamar ya daure kansa da ya budewa Takawa
zuciyar sa, yasan shi sarai da tsayawa akan ra’ayin farko, amma yayi tunani zai
fuskance shi duba da irin son da yake masa, dama Musaddik ya gaya masa, babu me
yarda da shirmen sa kamar yadda yake jaddada masa a kullum, babu me biye masa
ko bashi goyon baya. Tun daga lokacin yasan sarai babu me tsayawa ya saurare
shi, balle ya yarda da tsarin sa. Ammin sa ce kadai itama bata ja da maganar
Takawa, ballantana Bubu da baya iya aiwatar da komai sai abinda Takawa din
yace.

  

“Kana jina Muhammadu, maganar da kazo da ita bata kamawa
bace. A tsari na gidan nan ma zamu iya aika musu suzo nan din domin muna da
damar bada diyar tasu, sai dai ba zamuyi haka ba, zamu basu girman su da
darajar su in Sha Allah, za kuma musu duk abinda Muhammad yake so amma banda
shiririta.”

 

Ya karashe yana murmushi, murnushin shima yayi kawai ba tare da
yace komai ba. Suka cigaba da hira irin wadda suka saba har be san iya adadin
awoyin da ya bata ba, sai da suka ci abinci da Takawar sannan ya lallaba ya
shiga gidan ya gaida matan gidan ya kare a dakin kakarsa ya tarar da yan matan
family din sunzo suna da wani get-together da suka shirya sannan suyi maganar
tsari bikin Abidah guda daga cikin jikokin gidan.

   A kaidar sa baya sakar musu fuska ko kad’an domin
suna da rainin hankali sosai, duk da shi basa yi masa neman ma ya kula su suke
amma shi sam baya tsayawa shirmen su, da gaske suka shakkar shiga shirgin sa
hakan yasa yana shigowa shashen suka dinga yayewa da d’aya d’aya.

  Dan tsiririn tsaki yaja sanda suka gama ficewa ya zauna
yana muzurai a dole baya son raini shi. Mutane da yawa na fad’a masa yadda yake
abubuwan sa kadai ya tabbatar da shi din jini ne na sarauta amma shi sam be san
ma yana yi ba ma.

   Ya dan jima a wajen nata kafin ya tafi yana jin
zai dan dade kafin ya sake waiwayo su duba da tafiyar dake gaban sa akan aikin
sa.

 

***Yana zaune a gate din gidan yana dakon shigowar Abba Babban,
a kan idon sa ya dawo ya tashi da sauri ya tare shi ya bud’e masa kofar mota.

 

“Sannu da zuwa Abba.”

 

“Yawwa Ibrahim, kaine yau a gate din kenan.”

 

” Wallahi kuwa Abba, sannu da dawowa, ya aiki?”

 

” Alhamdulillah mun gode Allah, ya naka aikin?”

 

” Alhamdulillah.” Yace yana tuna abinda ya faru dashi.

 

” Allah ya taimaka ya bada sa’a.”

 

” Amin Abba.” Yace yana bin sa rik’e da jakar sa a
baya.

 

” Mika jakar ciki bari na fara gano Gaji.”

 

Yace yana bin hanyar da zata kaishi bangaren Gajin, da sauri
Khalil din ya kai masa jakar ya dawo ya zauna yana jiran ya fito. Ya dan jima a
wajen Gajin kafin ya fito sai dai ganin Khalil ya saka shi mamaki, abunka da
Babba nan da nan ya gane akwai wani abu.

 

” Ya akayi Khalil? Kana son gani na ne?”

 

” Eh Abba.” Yace yana sosa kansa

 

” Haba ko da naji, toh zan turo a kiraka kaji?”

 

” Toh Abba Nagode.” Girgiza kai Abban yayi ya wuce
bangaren sa. Maimakon ya koma gida sai yayi zaman sa anan yana jiran kiran
Abban. Yana zaune kuwa yaga fitowar Sadik ya tashi da sauri ya tare shi

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button