HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 6-10

 

          a qalla ya kusa
minti ashirin a zaune a haka,wanda hakanan yaji zaman yayi masa dadi,ko ba
komai ya dan samu break na wasu mintuna.

 

 

        Dan waiwayawa yayi
gefansa,a sannan ya hango tahowar professor shi da wasu mutane hudu,saiya miqe
ya gyara zamansa,ya kuma kunna motar yana jiran qarasowarsa.

 

 

        yana jin sanda ya
shiga yana sallama da mutanen,suka maida murfin motar suka rufe masa,don haka
saiya tashi motar,dai dai sanda professor ya furta

“alhamdulillah”yana sauke ajiyar numfashi.

 

 

        A nutse yake tuqin
har suka fita daga airport din,a hankali professor rashid yace

“lawan….ko ka sake koyon sabon salon tuqi ne?”raba
idanu samir yayi hagunsa da damansa,saiya lanqwashe murya yace

“eh alhaji”dan jim professor yayi sannan yace

“to yayi kyau”daga haka bai sake cewa komai ba,zaman
shuru yaci gaba da ratsawa a tsakaninsu.

 

 

          “Daka sani
ai baka wahalar da kanka ba samir…..”yaji abban nashi ya fada bayan
tsahon wani lokaci,ya ganeshi kenan,qyaleshi yayi kamar bai gane ba,qaramin
murmushi ya subuce a kuncinsa,jerarrun fararen haqoransa suka bayyan,har yayi
kamar bazaice komai ba sai kuma ya tanka

“yau daya dai abba….ai nima na samu ladan yau
din”wayar hannunsa professor ya ajjiye,ya tsurawa gaban motar idanu,kamar
anan fuskar samir din take,baisan me yasa a kullum shi da tilon dan nasa komai
nasu yasha banban ba,komai nasu ba iri daya bane,abinda yake sam ba cikin tsari
da burinsa ba,ya jima da sanin cewa ba haka yakeso ya kasance ba,ba haka
tsarinsa yaso ya zama ba,to amma duk ta inda yake tunanin zai gyarota babu wani
sauran dama data rage masa,don haka a maimakon yayi magana,saiya buge da hade
yatsunsa waje daya,yana maida tunaninsa wani waje daban.

 

 

          Duk sanda yayi
tafiya irin wannan ya dawo iyalansa dama ma’aikatan gidan kan cika da
murna,kamar yanzun,da samir ke biye dashi dauke da wata qawatacciyar qaramar
jaka mai zubin akwati,yana biye da professor har zuwa cikin qawataccen falon
gidan,mai yalwa da kuma burgewa,wanda ya wadata da dukkan wani nau’in kayan
alatun rayuwa.

 

 

       mutum uku ne ke
dakonsa zaune cikin falon,biyu daga cikinsun matasan yammata ne,daya tafi daya
tsaho da haske,kamar yadda daya tafi daya shekaru da basu wani taka kara sun
karya ba,don dukkansu ba zasu gaza shekara sha tara da ashirin ba.

 

 

        Daga wata kujera
kuma mai mazaunin mutum biyu,macace xaune itama wadda ta mallaki shekaru É—ai
É—ai har  shekara hamsin,saidai idan har
kai mai kallo xa’a qyaleka kayi mata Æ™iyasin shekaru,to ba shakka zaka ce
dauka cewa bata wuce shekara talatin da biyar ba.

 

 

         Tun a kallon
farko xaka bata sunan HAMSHAQIYA saboda ta cancanci sunan,fara ce
sol,shekarunta sam basu boye hasken fatarta ba,tana da matsakaicin kyau wanda
ya cakuda da tarin ado da qawar da take qawata kanta dashi kullum kwanan
duniya,kallon farko zai gaya maka ta saba da ado ya zame mata jiki,salon irin
abun nan da hausawa suke cewa WANKA YABI JIKI,tun daba hannayenta zuwa wuyanta
kayan ado ne na mata,fuskarta wadace take da murmushi kamar bakinta zai
yage,idanunta qur bisa saman fuskar wadan nan halittu guda biyu,wato samir da professor,tana
dubansu da wani irin kallo me nauyi da zurfi.

 

 

        Dukkaninsu suka
miqe kowanne fuskarsa na nuna tsantsar farinciki,daya daga cikin matasan
yammatan nan wadda da alama batakai shekarun daya ba ita ta tako da sauri zuwa
inda professor yake

“Abba…..sannu da dawowa”ta fada da ‘yar siga ta
shagwaba,da alama kuma hakan habit dinta ne,tana dora kanta saman
kafadarsa,kamar marayan daya samu tallafi,murmushi ya saka yadan dora kansa
saman kanta

“barka kadai auta….na sameku lafiya?”

“lafiya qalau abba,saidai munyi missing
dinka”murmushin yakuma saki

“gani na dawo ai jauhar,duk wata kewa ta qare ko?”kai
ta gyada,sai dayar itama ta matso,tasa hannu kadan tana gyara eye glasses
dinta,fuskarta itama murmushinne kwance

“barka da zuwa abba”

“barka kadai lelen abba…..na sameku lafiya?”

“lafiya lau abba ya hanya?”

“alhmdlh,ya karatu?”saida ta saki wani ni’imtacce
murmushi,tana jin wani dadi na ratsata,ta daga idanun a hankali ta maida
gashi,samir…….wanda har yanzu yake tsaye a bayan abban nasu tamkar wani
dogari,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa yana kallon dukkan abinda ke
faruwa, inside him yana jin tsaiwarsa a wajen cikin abubuwan da suke gundurarsa
nan da nan,ya qagu duka a gama wadan nan gaishe gaishen.

 

 

        dauke idanunta
tayi ta maida kan abban,a duniya tana jin dadi tana alfahari abban nasu ya
tambayeta karatunta,tana jin wani qwarin gwiwa yana shigarta aduk sanda ya
tambayeta wani abu daya danganci karatunta,takanji burinta kwadayinta da qwarim
gwiwarta yana daduwa

“alhmdlh abba….komai lafiya”

“ma sha Allah”ya fada yana maida dubansa xuwa
gareta,har yanzu bata matsa daga inda take tsaye ba,amma hankalinta idanuwanta
da hankalinta dukka yana kansu

“sarautar mata…….yada tsaiwa a nan?”murmushi ta
saki

“to ai naga hankalinka duka yana kan yaranka,kaga gwara na
barku ku gama tukunna…..barka da dawowa”

“barka kadai…..na sameku lafiya?”

“alhmdlh”ta fada taba jifansa da wani murmushin,saita
tako a hankali ta raba ta gefansa,idanunta saman fuskar samir,suna hada idanu
ya kauda kansa ya miqa mata jakar professor dake riqe a hannunsa,hannu ta miqa
zata amsa tana cewa

“ka kyauta samir”ya fahimci abinda take nufi,saiya
saki qaramin murmushi yana juyawa kadan zai fita

“ya da haka son…ka bari daddy ya kintsa muci abincin rana
tare mana”ta furta cikin nuna zallar kulawa,kansa ya girgiza yana sosa kan
mashi da tsinin key din mota,shida yakeson tsallakewa fadan professor,yayi
imanin idan ya zauna suci abin tare zai tono laifin da shi yaketa qoqarin
bunnewa ne

“akwai abubuwa da yawa dana bari,zanje na rage wasu,bazan
jima yau a waje ba zan dawo gida” sanda yake maganar shima professor ya
nufi hanyar da zata sadashi da sassansa da suka qunshi bedrooms manya guda
biyu,da.katafaren falo guda daya

“da zaki daina wahalar da kanki wajen tsaidashi,ki barshi
ya tafi kawai, saboda haka yakeso,hakan ya tsarawa kansa kamar ko yaushe”
sarai samir yasan magana ce mai harshen damo yayi masa,sai data waiwayo ya
kalli samir

“ohk….saika dawo,Allah ya tsare” kansa ya gyada
sannan ya juya zai fice,itama ta rufawa professor baya.

 

 

          “ya
saraki”kiran da aka masa shine abu na biyu daya shiga kunnensa daga hirar
professor da matarshi,sai yaja tunga ya tsaya sannan ya waiwayo a hankali sanda
take tasowa a shagwabe ta riskeshi.

 

 

        Idanuwan najwa tar
bisa fuskar jawahir sanda take nufar yayan nasu,saita sanya hannunta ta cire
airpiece guda daya cikin biyun dake maqale a kunneta,tana jin wani abu na
tokare zuciyarta,ta tsani taga tana magana dashi sam,tana son taji yanzun me
zatace da shi ne.

 

 

        “ya
saraki…..please,alqawarinmu fa” ajiyar zuciya yayi hade da lumshe
idanu,lokaci guda kuma ya furzar da iska daga bakinsa,baice komai ba saiya cusa
hannunsa cikin aljihunsa ya fiddo sabbin ‘yan dari biyar biyar masu dama ya
miqa mata,wani dan tsalle ta saki bayan ta amshu kudin

“thank you so much,am proud of you my yaya”murmushi
kawai ya bita dashi sannan ya taka ya fice.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button