HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 6-10

       kudin na hannunta
tana juyasu,fuskarta a wadace da murmushi ta koma kujerar data tashi akai ta
zauna,duk abun nan da ake idanun najwa a kanta,tana binta da wani kallo da zai
nuna maka zallar tkaici da haushinta daya cika mata zuciya,sam jawahir batasa
me take ba tana irga kudinta hankali kwance,ganin cewa da gaske jawahir batasan
tana yi ba,lissafin kudinta kawai take,saita miqa hannu ta fusge kudin a tare
tana furta

“banza”da qarfi,hakan yaja mata hankalin jawahir din
yadda takeso,dubanta take baki bude

“me na miki ya najwa”

“banza”ta sake maimaitawa tana hararta,idanuwanta
kamar zasu fado akan jawahir din

“wai me na miki?”

“ke wai.me yasa baki da zuciya,kuma baki da kishin
kanki?,na meye zaki tambayesa kudi,momi ba zata baki bane da ba zaki tambayeta
ba?”sosai jawahir ta bata fuska tana kallon najwan,ranta a dan bace

“amma shi da momyn ai duk daya ne ko?,kuma ko ita ai taga
ina tambayarsa,kuma bata ce komai ba”baki najwa ta tabe

‘bakya ganewa,kuma ba zaki taba ganewa ba…..”

“nidai koma meye bani kudina”ta furta tana miqa mata
hannu

“naqi na bayar din”najwa ta fada tana cusa kudin a gefan
cinyarta,sai jawahir din ta sake gimtse fuska sosai

“kinga ki bani kudina ya najwa,ko momy tace ki daina shiga
harkata ko?”

“idan kina da qarfi ki danne ni ki qwata,sarai dai kinsan
babu abinda zanyi da kudin nan…..”.

 

 

         A hankali ta buda
qofa ta dawo ta cikin falon,idauwanta ya sauka a kansu sanda jawahir ke sake
maimaita wa najwan ta bata kudinta

“lafiyanku?”momyn ta jefa musu tambayarsu,wanda banda
tayi magana babu wanda yaga fitowarta cikinsu

“momy….ya saraki na tambaya kudin ankon yasmin tun
rannan,to ya bani shine ya najwa ta karba ta hanani,tana masifar wai don me zan
tambaya ya saraki”jawahir tayi caraf ta gaya mata,sai data tabbatar ta
aikawa jawahir saqon harara sannan ta maida dubanta ga mony da nufun yin nata
bayanin

“momy wai ba…..”wani kallo momyn ta aika mata,sannan
ta daga hannunta kawai ba tare da tabi takan qorafin da takeso. sako.mata ba
tace

“bata kudinta”fuska ta bata

“momy….”

“nace ki bata kudinta ha’an…?”ta fada da dan zafi
zafi yanzun a muryarta,fuskar najwa a cunkuse,ta zaro kudin ta jefawa
jawahir,ya fada saman cinyarta,bata damu ba ta dauki kudinta taci gaba da
irgawa,momyn ta kalleta

“ajjiye kudin nan kizo kitchen ki hadama daddynku
drink”

“to momy”ta amsa mata tana miqewa da kudinta a hannu
tabi bayanta,yayin da najwa ta bita da harara,tana jin kamar ta shaqeta,saita
gyara glass din fuskarta,ta kuma gyara zaman qaton littafin dake ken cinyarta
taci gaba da dubawa,can qasan ranta abubuwa da yawa na mata yawo,inda tana da
qarfin iko da sai ta canza abubuwa da dama cikin gidan nasu,abubuwa masu tarin
yawa da basuyi rayuwarta yadda takeso ba,basu zauna kuma a gurbi da muhallin da
takeson ganinsu ba.

 

 

      *_9:30 am_*

 

 

*_DARMANAWA HOUSING ESTATE_*

 

*_PROFESSOR RASHID USMAN AZARE RESIDENT_*

 

 

       Daya ne daga cikin
jerin qawatattun gidaje dake gine cikin unguwar,,wanda suka qawatu aka kuma
ginasu bisa basira da kuma kyakkyawan tsari.

  

 

     Gini ne na alfarma
mai cike da qayatarwa da ban sha’awa,kamar yadda akasan ire iren gidajen masu
sukuni suke da kuma unguwaninsu.

 

 

       A hankali momy ta
daga kanta,fuskarta na fidda wani irin murmushi mai haske tunda ta jiyo sautin
muryarsa,tun gabanin ma ya iso inda suke din,yayin da ta tsaida dukkan abinda
takeyi,ciki harda cin abincinta,da kuma hira da take da ‘yammatan dake gefanta
su uku,najwa jawahir da kuma ramla da take ‘yar ruqo a wajenta.

 

 

        Dukkaninsu sunsan
meye ta baiwa hankalinta haka gaba daya,ba wacce bata saba da ganin tarin
kulawa da qauna daga gareta ba zuwa ga samir,wadda ta banbamta da ta kowanne da
dake cikin gidan.

 

 

        Kallo daya
professor yayi mata yaci gaba da cin abincinsa a nutse,don shi din ma hakan ba
baqon al’amari bane a wajensa,illa dai ya kada kansa sannan ya maida hankalinsa
ga farantin gabansa.

 

 

       Cikin sakanni da
basu kai goma ba ya bayyana cikin falon dab dasu,matashin saurayi muhammad
samir me laqabin saraki,ma’abocin tsaho,wanda murjewar jikinsa ta hana
bayyanuwar tsayin da Allah yayi masa yadda za’a fahimta,ya mallaki kalar fatar
da hausawa suke kira da wankan tarwada amma irin wankan tarwadan nan dake da
haske,taqi kadan zai dada ka kirayeshi da farar fata,matsakaicin kyau
gareshi,saidai abubuwa guda biyu sun taru sun qarawa siffarsa kyau da cikar
haiba KWARJINI da yake dashi,da kuma wasu lumsassun idanuwa masu kama da na me
jin bacci.

 

 

        Yana da sanyin
murya,irin sanyin da bai hana bayyanar cikar mazantakarsa gami da jarumtarsa
ba,sam ba miskili bane,kamar yadda wasu mutane da yawa suke masa kallon
haka,abubuwa ne guda biyu suka sanya suke masa wannan kallon,baya shiga sabgar
da bata shafeshi ba,bashi da shishshigi sam,hakanan bai fiya magana kan abinda
yasan yana da qarancin muhimmanci,koma kwata kwata bashi da muhimmancin,yana da
kamewa da wata irin nutsuwa mai jan hankali,yana da zurfin ciki a yawancin
lokuta,komai nasa bisa tsari da dacewa yake tafiya,shi yasa wasu ke ganin abune
mai wuyar gaske iya zama dashi,abunda basu sani ba shine,zama dashi din wani
abune mai dadi ga duk wanda ya soma mu’amala dashi.

 

 

        Akwai boyayyun halayyensa da ba kowanne ya
sanshi dasu ba,ciki kuwa harda makusantansa,yana da tausayi yana da taimako,a
wasu abubuwan ba zaka taba tsammanin cewa ya fito daga gidan girma da arziqi
irin wannan ba,rayuwa sassauqa da yakan gudanar….saidai,matuqar kazo lokacin
da yake kan tsininsa,zaka dauka baida kirki ko kadan.

 

 

       Muhammad samir,da
namiji guda daya tilo da Allah ya mallakawa professor rashid usman azare,wanda
tarin banbamce babancen halaye da zabi na rayuwa yaso ya zama babban shinge
tsakaninsa da mahaifinsa da samun dukkan wata yarda da qauna tashi.

 

 

        “welcome
son…..na tsammaci yau ba zaka fita ba?,naji shurun yayi yawa,duk da na kira
wayarka taqi shiga….saina zabi na barka ba tare dana aika ba,wala’alla kana bacci
ne kada a katse maka shi” hajiya jidda wadda auke kira da mommy ta
fada,dukkan kulawarta tana tare da samir din,fuskarta na fidda wani kalar
murmushi dake nuna farincikin dake tattare da ita na ganin fitowar samir
din,kamar yaune lokaci na farko data fara ganinsa,ko kuma wani gari yayi tafiya
mai nisan zango ya dawo a yau din.

 

 

        Washewa fuskarsa
tayi da wani murmushi mai aji,ya soma qoqarin jan kujera daya don yiwa kansa
mazauni sannan ya amsa mata

“A’ah anna….bani da wani abu da zan aiwatar ne da
safen….shi yasa na zabi na huta kafin na fita yau,don jiya ban samu zama
yadda naso ba” ya qarashe maganar yana duqawa zuwa qasa gefan
mahaifinsa,muryarsa cike da tsantsar ladabi ya furta

“Barka da asuba daddy” kallo daya yayi masa ya maida
kansa ga abincinsa yana amsa masa da

“Ka tashi lafiya?”

“Lafiya alhmdlh” sai ya maida dubansa ga mommy wato
hajiya jidda

“Barka da asuba mommy”

“Barka kadai yarona….da fatan ka tashi lafiya”

“lafiya qalau alhdmdlh”

“To ma sha Allah” ta amsa masa fuskarta na nuna jin
dadin samunsa lafiya da tayi kamar kullum,saita miqe da kanta ta fara bude
dukkan wani kwano dake saman teburin sanda qannensa ke gaisheshi daya bayan
daya yana amsa musu,kamar yadda ta saba tanayi kullum kwanan duniya matuqar ya
halarci wajen cin abinci,zata bude masa dukka ya zaba abinda yakeson ci,don
wani lokaci ma abinda ya zaba yana so shi za’a dafa kowa da kowa,koda ba
zabinka kenan ba,tun suna yiwa mommy mita da qorafi har ya zame musu jiki.

“Me zakaci a ciki samir?,Allah yasa akwai wanda ya dace da
ra’ayinka” mommy ta fada tana murmushi kamar kullum,wanda baka rabata
dashi saman fuskarta,sai a sannan alhj mukhtar yayi magana tun fitowar samir
din,idanuwansa saman fuskar mommy,wani abu na yawo saman zuciyarsa,wani abu mai
nauyin daya wuce a aunashi a mizani

“Ki kalleshi mana da kyau,ba yau ko jiya ko shekaran jiya
aka haifeshi ba,amma kullum kina kallonshi ne kamar ranar nan da aka miqo miki
shi cikin tsumman goyo,a qa’ida ya isa aure,a kuma qa’idance kamata yayi ace a
gaban matarsa yake” kanta ta langabe tana duban professor

“Haba daddy…..kai kake ma samir kallon yayi girma har
haka,ni kam a wajena har yanzu kamar yaron goye nake kallonsa…..bugu da qari
ma daddy idan ba’a kula da samir ba…wa zamu kula dashi?,karka manta shi kadai
Allah ya bamu….”

“Abbaaaa”sautin muryar jawahir tayi kutse cikin
maganar mummy,sautin daya fito a narke,kamar me shirin sakin kuka,waiwayawa
suka dukka suna kallonta,sai daddyn ya daga hannayensa duka biyun kafin yace

“You see…..su kuma daughters dina ki kaisu ina?”
Murmushi ya saki,wani abu na lilo can qasan ranta da zuciyarta

“Dole dukkaninsu subi bayan samir a wajena” a nutse
tsaf daddyn ya waiwaya ya dubi samir din sosai kuma kai tsaye,duk da idanun
samir din na kai kawo ne tsakanin yan uwansa,fuskarsa tana fitar da wani
murmushi me sanyi mai kuma cike da nutsuwa

“Gwara da kika ce a wajenki,ta ina yaronkin zai kama qafar
yarana?,yaron naki da ba jin magana yake ba,wanda ya sarayar da alqiblarsa,babu
wanda ya gane har yau inda yasa gaba” samir ya gama fahimtar qorafinsa na
jiya da yaketa gujewa shi yakeson sokowa a yau din,saiya dan sunkui da
kansa,kana ya daga kan nasa,yana muradun rushe wannan maganar,don baida
sha’awar ci gaba da yinta,don haka cikin girmamawa yace da ita

“Kome akayi yau din zanci mommy,ki zauna ki huta….zan
zuba da kaina,ina sauri ne ma,jiya akwai taron da zanyi da ma’aikata,ban samu
zama ba nasa aka maidashi yau”ya fada yana miqa hannu zai hada tea.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button