HALIN GIRMA 6-10

jawahir ce ta miqe
da hanzari ya dauka cup din ta soma hada masa,mummy tadan kalleta saita dauke
kanta
“yi a hankali sarkin rawar kai,kada ki zuba masa a
jiki”mummyn ta fadi sanda jawahir ke aje masa tea din,murmushi yayi ya
dauka yana.kaiwa bakinsa,shi yasa yakeson autar tasu,sosai take nuna kumawa kan
dukkan wani abu daya shefeshi,ba kamar ‘yar uwarta ba,wadda har yanzu bai
fuskanci inda ta sanya gaba ba,shegen sin jiki gayunbanza,izgili da yiwa.mutane
kallon banza hadi da rashi iya magana dukka najwa ta hadasu,abu daya da yasa
bata iya wani kyakkyawan abu a gabansa ko a kansa shine,baya daukar raini,kamar
yadda baya raina kowa,tafi kowa sanin ainihin wayeshi,wannan shine ya ke mata
waigi a kansa.
miqewa prof yayi
yana yagar tissue
“idan ka dawo yau din bayan sallar isha’i,ka sameni zamuyi
magana dakai”
“ok daddy”ya fada da muryarsa mai dadi,sannan yaci
gaba da kurbar tea din a nutse.
cup din ya ajjiye
bayan ya gama amsa wata waya,mummy ta dubeshi
“bakaci komai bafa samir?”
“mommy,am late”
“a maka packaging ka tafi dashi mana,ya zaka fita aiki babu
cikakken abinci a cikinka”
“ba komai mommy,zan nemi wani abun naci idan na samu
break”
“a’ah..,.najwa……maza,shiga kitchen ki cewa baraka ta
baki warmers qanana”fuska tadan bata
“Mommy…..yace a barshi fa”idanu ta fitar mata gaba daya
“ni kuma nace ki dauko…..”tuni ta miqe ma kafin
mummyn ta qarasa bayani,saboda wani kallo da samir din ya jefeta dashi,harta
soma takawa tajishi yana fadin
“dawo ki zauna,jawahir…..jeki dauko,guda daya ma is
ok”taf tsoro ya cika cikinta,saboda ba kasafai yake bi takanta ba,tana
tsoron irin wannan kallon nasa,saita ci gaba da tafiya ta miqe zuwa kitchen
din,wata tsawa ya watsa.mata wadda ta sanyata tsaiwa,ta kuma kasa juyowa,har
jawahir tazo ta wuceta da saurinta kuwa kamar yadda ya umarceta
bata motsa ba har sai dataji fitarsa
yana cewa idan an zuba jawahir din ta miqa masa yana cikin mota.
koda ta koma harara
Mommy ta bita da ita,sannan ta rufeta da fada,tana kallon fuskar jawahir,da
alama taji dadin yadda mummyn ta balbaleta da fadan,sai tayi sakato,mamaki fal
ranta,me yasa mummy ke mata fada da zafi har haka?,bata tanka ba har jawahir ta
fice daga parlour din,saita dauki jakarta dake gefe wanda dama shirin makaranta
tayi,kawai ta fice a falon.
yana daga zaune a
driver seat ta buda gidan baya ta sanya warmer din sannan ta rufe,saita zagayo
inda yake zaune din,fuskarta da murmushi
“a dawo lafya yaya”
“Allah yasa”ya amsa yana shirin rufe murfin
motar,saidai jawahir din bata matsa ba tana tsaye still a wajen,kansa ya daga
bayan ya sauke glass din motar yana dubanta
“ya akayi auta?”murmushi ta sakeyi
“kayi haquri yaya da abinda ya najwa keyi….ni kaina
bansan meya canza ba”qawataccen murmushin gefan baki ya saki
“karki damu, she’s still my sister…..ina tunanin tana da
damuwa,but we will talk later”kaita gyada kawai kana taja baya,ya tada
motar a nutse,ya qarasa bakin gate ya danna horn,idanunsa saman fuskar mai
gadinsu da yaketa marmashe gyada yana zubawa cikin jiqaqqen garin kwaki,ya taso
da hanzari ya durfafi qofar zai budeta,sai samir ya yafitoshi da hannu,don haka
yabar bude qofar ya iskoshi da sauri ya iso bakin window inda samir ke zaune
“Allah ya taimaki saraki”
“an tashi lpy baba”
“lafiya qalau dana”
“abinda aka dafa ne yau baba bai maka ba,na ganka da
garinka harda gyada?”samir ya tambayeshi yana dan murmushi,murmushin shima
yayi,a ladabce yace
“ko daya mai gida,yau dai bamu samu abun karin
bane”fuskarsa cike taf da mamaki bayan yadan yamutsata yace
“kamar yaya?,kune baku da sha’awar ci?”da sauri ya
girgiza kai
“ko daya,Allah ya taimakeka wazaiqi abinci irin na gidan
professor?,inajin dai yau da gobe ne irin ta bahaushe,wani lokaci ku samu,wani
lokacin kuma saidai kowa ya siya abinda yake dashi”baice komai ba saiya
duba agogon hannunsa,bashi da lokaci da cikin gidan zai koma,bai zaci wasu
cikin gida dake rayuwa tare dasu ba’a basu abinci ba,saiya bude aljihun gaban
motarsa ya aciro yan dubu dubu guda biyu ya miqa masa
“gashi,ka ajjiye wancan ka siya wani abun me dumi
kaci”hannu bibbiyu yasa ya amsa kudin yana zabga masa godiya,sannan ya
tafi qofar ya dage masa gate din,yaja motar da dan hanzari ya fice.
1/7/22, 08:18 – Buhainat: Halin Girma
  9
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi
08184017082 or 09134848107*Â
I’m on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my
photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb
***
Yana jin sanda motar ta tsaya, ya juyo da sauri ya kalle shi,
hankalin sa na kan wayar sa yana dannawa, fuskar sa a hade tsaf babu alamun
wasa ko kadan, tsoro ne ya sake shigar Khalil din sosai, yaji kamar yayi ta
kurma ihu yana neman taimako, amma kuma ya san babu wanda zai taimaka masa
musamman idan aka zo aka ga wanda yake tare dasu.
 Ji yayi an murda handle din bangaren sa, yayi saurin
matsowa sai gashi a tsakiyar motar, daf da Moh, wani banzan kallo ya watsa masa
da ya sakashi saurin komawa inda yake zaune.
“Come ou!” Wani murdadden soja yace matsa bayan kofar
ta gama budewa, idanu ya soma rabawa tsakanin Moh da sojan fuskar sa ta nuna
matukar tashin hankalin da ya shiga
“I said come out!” Ya daka masa tsawa da ta saka shi
saurin fitowa
“Dan Allah Oga kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da
rashin hankali, duk abinda na farfada ba wai har zuciya ta bane wallahi.”
Ya hau magiya yana kallon Moh da yayi kamar baya wajen, damtsen
hannun sa sojan ya kama ya shiga jan sa har zuwa wata kofa in da ya hangi
sojoji sun fi su ashirin suna tsalle tsalle a wajen.
“Oga dan Allah ka bawa oganku hakuri Dan Allah!”
“Kasan waye oga kuwa?”
Da sauri ya girgiza kansa
“Ban sani ba wallahi, rashin sani ya jawo nayi masa abinda
nayi amsa amma dan Allah na tuba yayi hakuri.”
Dariya sojan ya saka sosai
” Baka da hankali amma, ka zo har nan wajen kayi tunanin
zamu kyale ka, ka tafi free? Nah sai mun dan sassamaka yadda gobe ba zaka kara
ba. “
” Dan Allah nace fa? Ka tayani bawa ogan hakuri. “
” Naka wasa ne. “
Yayi gaba yana rik’e dashi, yanayin rikon da yayi masa da yanayin
jikin Khalil din zai baka dariya sosai, dama bashi da wani jiki sosai gashi
kuma a hannun manyan maza, wani daki ya kaishi sannan ya sake shi yana masa
dariyar mugunta
“Zaka kwashi kashin ka hannu yau, wallahi Oga zai iya sawa
a batar da kai a k’asar nan, kasan waye kuwa? Tab.”
Jawo masa kofar yayi ya rufe ta har da key yana kwasar dariya.
 Chan karshen dakin yaje ya tsugunna yana jin dana sanin
barin zancen da yayi, dama a maida baya da ya goge duk abun da yace ma Muhammad
din cikin rashin sani. Ji yayi cikin sa na kara alamar ya lalace, ya tabbatar
bala’in tsoro da firgicin da ya shiga ne ya saka cikin nasa lalacewa. Mikewa
yayi da sauri ya hau zagaye a dakin yana maimaita
“Innalillah wa inna ilaihi rajiun.”
Ji yayi ana murda key din dakin, ya tsaya yana kallon kofar
cikin tsoro. Captain Moh ne ya shigo sojoji biyu na biye dashi a bayan sa, daya
rik’e da kujera yazo ya ajiye masa ya zauna yana wa Khalil murmush