HALIN GIRMA 6-10

“Alhaji Khalil barka da warhaka.”
“Dan Allah dan Allah kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan
ne da yarinta wallahi amma ba zan sake ba.”
“Haba Khalil, so soon haka? Ka sani ko sojan gona ne ni,
kasan fa talaka da samun wuri.”
“Wallahi ni dai ba zan sake ba, kayi min rai, mahaifiyta da
ni ta dogara, dan Allah.”
“Calm down magana zamuyi, ka nutsu ka saurare ni, warning
ne me hade da dokoki, ina fatan zaka bud’e kunnuwan ka kaji ni sosai.”
“Ina ji wallahi.”
“Babu kai babu abinda ya zama mallaki na, Ina nufin Fatima,
ko a hanya ka hadu karka taba nuna ka santa balle har magana ta hada ku, a da
nayi niyyar barka ka gwada sa’ar ka akanta, amma kuma a yanzu na gama yanke wa,
baka kai na nemi abu tare da kai ba, dan haka ko son ta zai kashe ka sai dai ka
hakura… “
” Na biyu, a yau ba sai gobe ba zaka wuce in da ka fito, ba
tare da ka bud’e bakin ka kace wa kowa komai ba, ina nufin, bakin ka ya zama
kanin kafar ka, kar naji zancen a wajen kowa ciki har da ita yayarta ka da bata
tsoron Allah. “
” Last but not the list ka koma bakin aikin ka, ka rik’e
mutuncin ka sannan bakai ba wulakanta kowa. “
” Duk abinda ka fad’a wallahi zanyi, nayi alkawari, ni dai
kar ka raba ni da mahaifiyata wallahi bata da kowa sai ni. “
” I’m done with you, gashi nan take him back, ku tabbatar
ya bar Kano kafin karfe shida na yamma. “
Juyawa yayi cikin wani irin taku ya fice daga wajen, yana fita
sukayi kansa
” Ai wallahi ba zaka shigo nan a banza ka fita bamu ci
ladan ka ba. “
Wani soja yace yana kai masa rankwashi.
” Tashi kayi frog jump. ” Dayan ya daka masa tsawa yana
zaro belt dinsa. Da sauri ya hau yi yana hada zufa su kuma suna tuntsura
dariya, sai da suka gajiyar dashi sosai sannan suka fito dashi suka sashi a
mota suka maidashi har kofar gidan suka ajiye sannan suka tafi.
***Abba na zaune yaji text message ya shigo wayar sa, tunanin sa
ma ko alert ne ya bud’e sai yaga sako daga bakuwar number da be sani ba, bud’e
message din yayi ya soma karantawa
_” Dr. barka da warhaka, ya aiki? Allah ya taimaka. Dama
wata magana nake son yi akan fatima, ina rokon alfarmar daka saka ido sosai
akan abinda yake faruwa a cikin gidan, in sha Allah zaka gano wani abu da ya
dade yana faruwa ba tare da sanin ka ba. Sai anjima a huta lafiya. “_
  maimaita karanta sakon ya dinga yi yana kokarin
daidaita tunanin sa waje guda, waye ko wace wannan? Me sakon yake nufi? Me ya
faru da Fatima din? Duk wadannan tambayoyin ne suka shiga yi masa yawo aka, be
san me yasa ba, kawai sai yaji hankalin sa ya kasa kwanciya da abinda ya
karanta. Tashi yayi ya fito zuwa falon gidan, ya k’wala kiran Iman din. Zeenat
ce ta fito
” Ina Ummi? “
” Ina ga tana wajen Gaji. “
” Je ki kira min ita. “
Fita tayi shi kuma ya cigaba da tsaiwa awajen har suka shigo a
tare.
” Ki same ni a daki na. ” Yace yana juyawa tabi
bayanshi, dariyar mugunta Zeenat tayi a tunanin ta wani laifin Iman din tayi
dan sosai yanayin Abban ya nuna bacin rai.
A gefen gadon sa ya zauna, ta samu chan gefe daga kasa ta rakube
tana tunanin dalilin kiran.
” Kina jina Uwata? Kina da wata matsala wacce ban sani ba?
“
Girgiza kanta tayi
” A ah Abba babu. “
” Kalle ni nan, ni ne mahaifin ki, baki da wanda yafi ni
bayan mahaifiyar ki, ki fad’a min gaskiya idan akwai wani abu da yake
damunki.”
Zuciyar ta ce tayi rauni, taji kuka na taho mata, ta k’asa rike
shi kawai ta fashe da kuka. Dafe kansa Abban yayi, ya shiga tunanin me yake
faruwa? Wanne irin abu ne haka da har shi ya kasa ganewa?
“Fatima…” Ya kira ainihin sunan ta a karo na farko a
rayuwar ta
“Na’am.” Ta amsa cikin muryar kuka
“Kowanne bawa da irin yadda rayuwa take zuwar masa, kiyi
hakuri zanyi bincike, sannan akwai shiri da nake yi na kaiki wajen mahaifiyar
ki da zarar maganar bikin ku ta tabbata, nayi mata alkawarin kai mata ke da
zarar lokacin auren ki yayi, mahaifiyar ki na son ki fiye da yadda take son
kanta, ki rik’e wannan.”
” Tashi kije kinji, ki daina kukan haka.”
Tashi tayi bayan tace
” Nagode Abba.” Ta fice ya bita da kallo yana jin
kamar be kyauta mata ba.
Dakin su ta wuce ta tarar da Zeenat na waya har da shewa, juyawa
tayi zuwa store ta zauna a gefen katifar ta, tayi kuka sosai har sai da taji
babu abinda yayi saura a zuciyar ta. Tsawon lokaci ta sauka a ciki har sai da
taji maganar Mama tana fad’a a waya anan ta gane ta dawo dan dazu bata gidan.
Tashi tayi ta fice ta kofar baya bayan ta gyara fuskar ta a sink din kitchen.
***Zama Mama tayi tana sababi akan tafiyar Khalil din babu
sanarwa, sai dai a k’asan zuciyar ta taji dadin hakan domin a kalla hankalin sa
zai dauke daga kan Iman din har a gama magana da shi dayan da yazo. Abba ne ya
shigo ya sameta tana zaune , ya zauna a gefenta sai tasha jinin jikin ta
musamman da ta gama sanin halin sa tsaf.
“Me yasa kika ce min Ibrahim ba da gaske yake akan maganar
Ummi ba, sannan shi kuma yaje ya samu Yaya da maganar.”
Yadda ta zabura yaso bawa Abban mamaki.
“Khalil din ne yaje wajen Yaya? Yaushe akayi haka? Me yayan
yace masa?”
“Duk ba wannan na tambaye ki ba, baki bani amsa ta
ba.”
“Toh toh ai gani nayi shi Khalil ba yanzu zai yi aure ba,
su kuma yaran nan yanzu ne muke so mu aurar dasu, bana so Zeenat ta tafi da bar
Iman tunda kaga tare suke komai, shiyasa nace gwara wanda ya shirya.”
“Haka ne kuma.” Yace yana mata wani irin kallo da ya
sakata tunani sosai
“Toh hakan yayi ai, Ina fatan dai zeenatu ta sallami yaron
nan Bashir ko? Dan ina nan akan bakana ba zan bashi ba.”
“Dan Allah Dr ka bar wannan maganar, tunda tana son shi
kayi hakuri kawai ayi tunda an wuce zamanin da za’a yi wa yara auren
dole.”
Girgiza mata kai yayi yana dakatar da ita
“Wannan maganar taki shirme ce, musulunci mu ya bawa damar
zaba wa yayanmu mazaje na gari, dan haka ban yarda da Bashir ba, idan akwai
wani ta kawo shi.”
Ya tashi ya fice ransa na baci da yadda maganar Bashir din taki
karewa, sam Hajara bata shirya gane abunda yake hango musu ba, eh hango musu
tunda duk in da aka je aka jawo ita uwa sai tafi cutuwa da abinda zai samu
yarta.
***Text message biyu ya tura a lokaci daya, address din sa da
Abba yace ya tura masa ta message sai kuma message din da yayi wa Abban Iman
din, wanda yake ganin shine kadai hanyar da zai bi wajen hana Maman sanin duk
wani abu akan Iman din, ya tabbata daga lokacin Abban zai saka ido sosai, ba
kuma za’a dau lokaci ba zai gano komai, shi kuma sai yayi amfani da wannan
damar ya nemi alfarmar barin komai ya zama sirri a tsakanin su iyaye maza,
domin dama su iyaye maza baa sansu da ratatin zance ba, ba kasafai ma suke zama
suyi ta magana anyhow ba, ya tabbata idan har hakan ta yiwu toh zai samu abinda
yake so, zai kuma tabbatar da Fatiman sa ta samu gatan da bata taba tunani ko
hasashen samun sa ba.
***Tunani Abba ya fad’a ganin address din da Muhammad ya turo
masa a matsayin in da yake,Emir Palace Kano, Emir Palace Adamawa-Yola, me hakan
ke nufi? Kiran Abban su Fatiman yayi yazo ya same shi a part din sa, ya nuna
masa message din sannan ya kira sauran yan uwan su Abba Musa suka hau
tattaunawa akan abinda ya kamata su yi. Dama chan Abba Musan yana siyasa sosai,
sai sukayi shawara akan shi ne zai wuce gaba wajen binciken waye Muhammad din a
cikin kwana uku kachal. Haka kuwa akayi, washegari ya same su da maganar da ta
yi matukar basu mamaki. A yadda suka sani idan wani daga cikin irin wannan yaga
yarinya yana so, kawai aikawa ake iyayenta suzo ayi magana a fadar sarkin, a
matsayin shi sarki dama uban kowa ne, sai suga ga banbanci inda Muhammad din
yazo kai tsaye ba tare da ya nuna shi din waye ba, ba kuma tare da ya nuna
karfin iko na mulki ba, hanyar da ta dace da kowa yake bi wajen neman aure
shima ita yabi.
 A cikin su babu wanda be yi amanna da maganar ba,
musamman binciken da Abba Musan yayi da irin yabon da Muhammad din ya samu daga
wajen mutane da dama musamman mazauna masarautar.
  Shiru Abba yayi bayan kowa ya gama tofa
albarkacin bakin sa, aka bashi dama a matsayin sa na mahaifin Iman din,