NOVELSUncategorized

KWARATA 52

KWARATA

???? —— 52           Ina zamu je yanzu ? Al ‘ Ameen ya tambaya ? Muje gidana Momy tana can tana jiranmu , juya kan sitiyarin yayi muka kama hanyar gidan Dikko , babu wacce nayi ma magana a cikin su kuma banyi ta wani fizge² ba kawai na tsaya ne naga iya gudun ruwansu nasan dai bana kasuwa a wurinsu saidai su dakeni , murmushi nayi mai sauti tare da binsu dukansu da kallon rainin hankali ,

       Jiddah harararki takeyi , wacce aka kira da Jiddah ta juyo tare da yankamin wani irin lafiyayen mari harsai da gefen bakina ya fashe , murmushi nayi cikin takaici nace wallahi kinyi sa’a rayuwa taimani duka amma da yanzu²n nan na kifar da motar nan kowa ya mutu , me nayi muku kuka shigo rayuwata a dai² lokacin da nake kukan mutuwar mahaifina ?

     Ɗayar tace munafika ji tana nuna kamar bata san komai ba , idan kin manta bara a tuna miki , ai kinsan Dikko ko ? Wannan matarsa ce ta nuna Jiddah ke ɗin banza ɗiyar mashayin giya jikar matsafi ki haɗa ƙirji da mijin ɗiyar masu wankakken asali , da sauri na rufe idona amma kafin ta rufe bakinta tuni nakai mata kaina da ƙarfi hancinta ya fashe jini yaci gaba da kwarara , cikin tsananin ɓacin rai nace ita jakar da kike magana itace baƙuwar Dikko ,

       Da tun farko kun faɗamin ko suwaye ku da ba’asha wahala ba , domin ido na a buɗe yake inga macen da zata kalli mai girma Dikko in tsiyaye mata kwayar idanuwa ke dan ganganci ma aurenshi kikayi ko ? Hmm hawan doki ba linzami muguwar kasada ne domin in baka faɗo ba kasha wahala , idan kin isa ki kira Dikko a waya na kirashi dani dake a ga wayar waye zai riga ɗauka , matar sadaka dake ,

      Gaba ɗayansu suka rufeni da duka a dai² lokacin da muka iso cikin harabar gidan , dukana suke tun daga cikin mota har waje suka jawoni , matar Dikko ta bugamin kai a jikin mota sai dukana sukeyi babu ji babu gani kamar an kama musulmin ɓarowa a chochie , murmushi nayi cikin wahaltuwa nace kinji haushi ko ? Nace miki matar sadaka ! 

     Kiyi haƙuri mace ɗaya ce a zuciyar gwarzon namiji idan har akwaita to ba kowa bace nice , haka yake faɗamin kullum rana , kuma yacemin babu wata mace a duniya saini domin zuciyarshi da idanuwan basa ganin kowa saini , kunnen sa bayajin maganar kowa sai tawa ,

A dai² lokacin da Umar ya iso wurin yana ranki ya daɗe lafiya ya tambayi matar Dikko , sai kuma ya kalleni yace Sultana ya akayi kika zo nan ke kuma ? Goge hawayen baƙin ciki nayi sannan nacewa Umar Al ‘ Ameen ne yaje har gida ya ɗaukoni da ƙarfin tsiya , a gigice Umar ya kalli Al ‘ Ameen tare da zaro idanuwa yace da kanka ?

    Wayarshi ya ciro daga aljihu yana wallahi saina faɗa mishi , ka kamo An mata da tsiya² ka rungumar mishi An matar shi ? Hmmm lallai akwai matsala dan nasan idan har naga mala’enka mutuwa tabbas nasan tafiya tazo wallahi yau babu abinda zai hana mai gida dawo katsina cikin daren nan , 

      Jiddah tace ka kirashi ka faɗa mishi ni banajin tsoronshi , Umar yace yau zaki fara ji ki jirayi zuwanshi a dai² lokacin daya fara cewa ranka ya daɗe Al ‘ Ameen yaje har gida ya ɗauko Sultana kuma da ƙarfin tsiya ya jawota gata nan sai dukanta sukeyi kamar agola yaci zarafin ɗan masu gida !

      Banji yadda Umar da Dikko suka ƙare ba suka jani mukayi ciki , a gaban mahaifiyar Dikko suka gurfanar dani tare da cewa Momy gata nan , kallona tayi sosai irin yanayin kallon da Dikko yakeyi irin kallon takeyi , itama dai kyakkyawa ce kamar buzuwa hutu ya tabbata ga kyakkyawar matar nan ,

       Ɗan zamowa tayi daga cikin kujera tace yarinya ya sunan ki ? Ɗan kauda idona nayi dan bata girmanta nace suna na Sultana , meye tsakaninki da ɗa na ? Cikin ladabi nace babu , miye dalilin da yasa ya ɗauki mota ya baki ? Shiru nayi dan banda ansar bata , dake nake , nayi shiru , tace tou saurara kiji da farko zaki bada makullin motar nan aka kawomin shi , na biyu kuma ki fita daga harkar Dikko idan ma yana miki ƙarya yana sanki tou ƙarya yake miki baya sanki , ya faɗamin bakina da nashi yace halakar dake zaiyi da soyayyar shi ya kaiki ya baro ki , kuma tun yanzu ya kaiki ya dawo domin kin tafi kuma Dikko ya dawo , dama in banda baki da lissafi ya za’ayi a haɗa doki da jaki ? Siga ko a faɗar sunan ba iri ɗaya ne ba , ina ke ina zinari ? Matsayin Dikko ya wuce naki ki tuna idan kin manta , gidajen da kuke haya gaba ɗaya ya tattara ya siye ya mayar dasu gidan kiwon dokunan shi , 

        “Yar talaka waye ya kaiki kiwon doki ? Jidda tace kuma ita ba jinin sarauta ba , Momy tace duk dinari sunanshi dinari akwai na talaka akwai na masu kuɗi wallahi Dikko babban zinari ne koda kuɗinka saida rabonka kuma ba’a saka irin kaɗɗararshi a caca tsaftatacce ne shi baida sirki ba’a haɗashi da komai ba ko goro baya ci bare yasha sigari ke ko naki uban kwalbewa yakeyi kuma saiya raba titi biyu tirrr da sanin zuri’ar da ubansu baya ciyar dasu ,

     Tadai wulaƙanta ni sosai ta faɗi duk wasu sirrika na gidanmu abun dai babu daɗin ji , ta tozartamin Babana bawan Allah da yana can lahira duk a gaban Jiddah tayi min wannan wulaƙancin sannan ta rufe da cewa in tattara inbar garin katsina saboda jahar mijinta ne idan taji labarina kusa ² wallahi zata ɓatar dani , Al ‘ Ameen maida banza ka taho da makullin motar ɗana ,

         Jiki a sanyaye na miƙe na kalli Al ‘ Ameen dake gefena nace mu haɗu gidanmu in baka , Momy tace ku haɗu a ina ? Ki bishi ku tafi tare , ko inda take ban kalla ba nayi gaba abuna yau banda inajin mutuwar Babana tana yagarmin zuciyata da babu abinda zai hanani na faɗawa matar nan miyagun kalamai masu zafi . 

       Da sauri na fita daga gidan zuciyata tana tafarfasa kamar zata zubo ƙasa saboda azabar zafi , nayi tafiya mai nisan gaske sannan na samu abin hawa , gashi banda ko sisi kuɗina an sace su duka , a ƙofar gidanmu na samu Al ‘ Ameen nacewa mai napep in ya jirani ina zuwa yace to ,

      Gida na shiga na ɗauko mukulin mota na bawa Al ‘ Ameen ya tafi , shi kuma mai napep nace masa kana san katifa ? Dan gidan babu kowa duk kowa ya kama gabanshi , mai napep yacemin hajiya siyarwa zakiyi ne ? Nace Eh idan na samu masu siya dan siyar idan ban samu ba sai na bayar kyauta tashi zamuyi ….

    Dame ² zaki siyar ne ? Nace katifa labulaye sai gas sai tukunya ɗaya bokitin wanka da dai sauran tarkacenmu na mata idan kuma kana da kuɗi kawai ka bani dubu 3 ka kwashe duka , da sauri ya warwaro 3k ya bani , muka koma dashi gida har ledar tsakar ɗakin saida ya cire ganin katifar mai mutunci ce yace hajiya bara na ƙara miki ɗari biyar nace ngode ,

       Yana cikin kwashe kayan wayar Mamy ta fara ringing da sauri na ɗauka cikin wahalalliyar murya tace Mamy mu haɗu dake general yanzu ² tafiya za’ayi dani gida a daren nan , wane ɗaki kike ne ? Emargency da kinzo ki kirani amma karki daɗe nace tou , a wurin nabar mai napep na fice daga anguwarmu ina mai cike da kewarta.

        Napep nahau babu ɓata lokaci muka isa general a lokacin har an fiddo matar za’a sakata a mota ina kiranta ta ɗauka na faɗa mata na iso , tace ta ganni itace aka kamo in matso inda suke , da sauri na matsa wurin duk na gaishe su suka ansa tacemin ina Mamyn take ? Cike da damuwa nace mata Aunty ta rigamu gidan gaskiya , ni nice Sultana , salati matar tayi tare dayin kabbara tace tou Sultana shiga mota muje , nace tou babu wani wasi² ko kokonto na shiga mota ahalinta suka shiga muka fice daga asibitin bansan garin da zamu ba….

      01:30am ihun Al ‘ Ameen ya karaɗe kaf ilahirin girman gidan gwamnati , a ɗakinshi ya farayi mishi wata irin azzalimar shaƙara bayan an ƙwaƙwale Al ‘ Ameen daga hannunshi dakel , shine Al ‘ Ameen in ya fito da gudu ya nufi inda zai haɗo da Dady dan yasan duk girman gidan nan babu wanda ya isa ya hana Dikko yayi mishi wani abu saishi , kuma duk Umar ne ya ƙara zuga Dikko yadda ya kamata kuma duk zagi dacin zarafin da akayiwa Sultana saida ya laɓe yaji kuma ya faɗawa Dikko , tsakanin Abuja da katsina ji yayi tayi mishi nisa yaci titi yadda ya kamata Allah dai kawai ya kawoshi katsina dan Ashiru ma baiyi tunanin zaizo katsina da rayuwa….

       Ihu Al ‘ Ameen yakeyi a taimakeni zai kasheni yayin da Dikko ya koma mota cikin ɓacin rai yabi Al ‘ Ameen da gudu , na bani na lalace gefe² ya riƙe hayewa inda mota bata hawa amma hankalin Dikko ya fita daga jikinshi duk mai lumfashin dake gidan nan babba da yaro babu wanda bai fito , cikin tashin hankali Dady ya tunkari motar yana Babana meye haka kakeyi wai ? 

     Da gudu Al ‘ Ameen ya ɓoye a bayan Dady cikin tsananin ɓacin rai Dady yace meya haɗaka dashi ne ? Al ‘ Ameen yace babu abinda nayi mishi kawai ina ɗaki kwance yaje yaita dukana da ya gaji kuma shine ya shaƙeni ,

       Dikko da aka fito daga mota dakel yace babu abinda kamin ko ? Dady yace Babana wai meke damunka ne ? Cikin tsananin ɓacin rai yace saifa na kasheshi matsalata kafin na gano kanamun munafinci ne amma da zaran na gano ka tou babu sauran amfaninka a duniya da ƙarfin bala’e zan shaƙeka saina kashe ka hankalina zai kwanta ,

      Momy data iso yanzu tace ka kashe tunda kai mahaukaci ne , kamar jira yake tayi magana ya fizgo Al ‘ Ameen yayi mishi kyakkyawar shaƙa yana zaka sake shiga sabgata ? Ina makullin mota ta dan ubanka ? Dady yace sakarshi Babana ! Dikko yaci gaba da cewa tunda kake kaga ina shiga sabgar wani a gidan nan ne ? Ubanka ne ya bata motar ko ni ? Har kaine ka isa ka taɓa An mata ,

       Saida Al ‘ Ameen yayi fitsari a wando saboda azaba kuma anyi a cire Dikko daga riƙon da yayi mishi an kasa , saida Dady yasa hannu aka ciroshi dakel bayan Al ‘Ameen ya suma , wani irin ihu Dikko yayi mai tada hankali yayi wata irin jijjiga ya sake tattaka Al ‘ Ameen zaiyi magana lumfashin ya tsaya ,

Su Ashiru suka ɗaukeshi aka shiga dashi ciki kamar yadda Dady ya bada umarni , cikin bedroom aka kai Dikko saman gado aka kwantar dashi , koda Momy ta shigo Dady cewa yayi ta fita baisan ganinta kuma wallahi idan bata fita harkar Baban shi da yarinyar nan da yake magana wani abu ya sameshi wannan Jiddah da kika matsa kika auro mishi wallahi saina sashi ya saketa , Dady yaci gaba da cewa ai nima ina da “yan uwa kuma suma suna da”ya “ya sai yaje ya auro yarinya mai ɗa’a da tarbiyar.

     Kullum kina gidan yarinya ke ko kunya bakyaji kin hana yarinya ta zauna ɗakin mijinta kullum tana gidan surukai , tou kayi mata gori tazo ta kwana kuma ko Dikko baya aurenta nan gidan uwarta ne saita kwana kaje ka koreta tana can ta kwanta , tsoki Dady yayi mai nuni da bata da hankali ,

       Nan yabar Momy tsaye ya ɗauko maganin Dikko ya zuba mishi a baki , da sauri ya buɗe idonshi maganar Umar taci gaba da dawo mishi wai Jiddah ta bugawa An mata kai a mota , ta daketa har ta fasa mata baki , kuma ka faɗawa Dikko saboda ni banajin tsoronshi , murmushi yayi ciwon mugunta ya tashi da sauri ya diro daga saman gadon ya fita Momy tabi bayanshi da sauri , kafin ta fito harya ɓace mata ya nufi part inta ,

       Kwance ya samu Jiddah saman gado tayi ɗai² tana shan iskan A C bata da wata damuwa hankalinta kwance , ƙafarta ya riƙo ya jawota ƙiyyy a firgice ta buɗe idonta wayyo Allahna Yaya me nayi maka ? Dake da waye kuka je gidansu An mata ? A tsorace ta nuna mishi ƙanwarshi dake kwance gefenta tana bacci , kallon ƙanwar tashi yayi sannan ya sake kallon Jiddah yace bana dukanki amma ki tattara ki kama gabanki ki tafi gidan babanki babu wanda yaji babu wanda ya gani har sai na gano An mata ,

        Idan baki tafi ba na rantse da Allah sakinki zanyi kuma saki na wulaƙaci da tozarci amma in kika haɗa ya nayi ² sai ki ɓace abinki babu wanda yaji babu wanda ya gani , idan wani ya kirani ya bani haƙuri zan sakeki ne , idan kika sake dawowa gidan nan ba tare da An mata ta dawo ba saki ne , idan har kika bari Momy taji ta zageni ko tamin faɗa saina sakeki ya ƙarasa maganar yana fizgo ƙanwarshi itama da sauri ta buɗe idonta wayyo Allahna na shiga 3 tasan haukan Dikko Yaya wallahi Momy ta aikeni itace tace naje , wani irin mari yayi mata saida ya bata kashin bala’e yace idan ta aikeki gobe sai kije ,

       Kuma a gidan nan An mata zata dawo da zama idan akwai wanda ya isa saiya hanata zama na gani , wasu kwashe ² ma sunzo bare kuma matar ishashsshe , wallahi idan dai na ganta a daren nan saita kwana gidan kallon banza ko harara wani yayi mata saina makantashi har abadan duniya , Momy data shigo yanzu tace da Allah rufemin baki sakaran banza ka kawota gidan nan kaga yadda zanci mutuncinta a gaban idonka , baiba Momy ansa ba yace ma Jiddah kuma ki anso mata makullin motar ta kafin kiji babu daɗi ,

     Momy tace makullin mota yana hannuna Jiddah zata riƙa hawa motar , taɓe baki Dikko yayi yace ba komai An mata dai ta hau ta bata kwance yana faɗin haka ya fita yaci gaba da kiran wayar An mata…

      Dikko na fita Jiddah tace Momy idan Allah ya kaimu gobe zanje gida , Momy tace lafiya ? Jiddah tace tunda muka dawo daga america nake cewa zanje ² Allah bai bani ikon zuwa ba , Momy tace sai kuma cikin dare zaki faɗamin zaki ? Jiddah tace kiyi haƙuri Momy ai kwana biyu zanyi in dawo , Momy tace tou Allah ya kaimu , sun dai daɗe suna ɗan firarsu sannan kowa ya kwanta yayin da Jiddah tayi ƙudirin warware soyayyar Sultana daga zuciyar Dikko ,

       Wurin Dady ya koma har yanzu yana kiran An mata amma taƙi ɗaukar waya ita ai dole tayi fushi , shi kuma bai daina kiranta ba , a gaban idona kiranshi yake shigowa kuma a gaban idona yake tsinkewa dukan kiraye ²n da yayi min ina ganin su,

        Dan sai 10:58pm muka iso garin Daura , kuma tun muna hanya Dikko yake kiran wayata har yanzu kusan biyu da rabi yaƙi daina kirana , ni ɗaya ce kwance a ɗakin da aka bani gidan “yan gayu komai dai yaji bakin gwargwado matar da ta taho dani tace na kwanta da safe zamuyi magana ,

       Hawaye ya cikamin ido tausayin Dikko ya kamani sosai dan abinda na lura idan za’a kwana a haka bazai daina kirana ba haƙura nayi na ɗauki wayar cikin kuka nace ka daina kirana mayaudari mai yaudararin kalamai , Dikko yace An mata wai mi yasa ke birkitaccen tunani gareki ne ? Kaine mai birkitaccen tunani ashe da kake cewa ka ƙagara gari ya waye kazo gareni duk yaudara ce , ka shirya munafircinka shine kasa aka wulaƙantani aka tozartani aka zage Babana da baisan irin rayuwar da nakeyi ba a halin yanzu , to na bar katsina sai ka zuba ruwa ƙasa kasha kuma daga nan gaba naci kada Allah yasa na sake ganinka ko a mafarki na , a haka dama kake tunanin zance ina tsanka ? Tou bana sanka na tsanake ׳ ,

      Cikin hayani Dikko yace kada Allah yasa ki soni An mata idan baki so ni ba zan mutu ne ? Sai lallaɓaki nakeyi kin ɗaukeni kamar wani sakarai sai gagari nake tsakanin rayuwata da taki , baki saurarawa kiji abinda zan faɗa miki kije kiyi duk abinda kika ga dama idan kin tashi ma kibar Nigeria ƙarewar katsina nima kada Allah yasa na sake ganinki a barci na sai me , ƙaramar yarinya dake , sassauta murya yayi yace kiji tsoron Allah An mata domin ubangiji yana iya jarabtarki da irin soyayya da ya jarabeni da ita taki , me nayi miki haka kika tsaneni don Allah ? Haba An matana nasan kina san Dikkonki kuma kina tausayina kiyi haƙuri yanzu kina ina inzo ?

         Fashewa nayi da kuka idan har nace bana san Dikko nayi ƙarya ina sanshi ׳ amma nasan babu yadda za’ayi gidansu su bari ya aureni saidai kawai mu dawwama muna soyayya , duk soyayyar da babu aure a cikinta ta zama shirme ni haka rayuwata zata ƙare tsanin sama da ƙasa ? Saina hau sai na sauko ? Me yasa zuciyata ta cuceni ta koyi soyayyar wanda tasan yafi ƙarfinta ,

        A gajiye Dikko ya kwanta saman kujera 2siater yace inajinki kina ina ne ? Ina ina sai kuma nayi shiru , kina ina Nidai kayi haƙuri bazan faɗa ba , cikin sigar lallashi yace ai nasan zaki faɗa irin ɗan jan ajin nan ne na mata kuma duk a rasa wanda za’aja ma aji saini An mata ni ko bana iya ja miki aji wallahi saboda baida wani anfani inja miki aji ince na jawa wa aji ? Da kinsan yadda na ɗaukeki wallahi da baki fara tafiya kika barni ba , amma nasan kema wasa kike kina katsina ,

        Ina katsina amma bana cikin katsina , yace ai na sani saboda wallahi inajinki kusa dani amma zaki ɓatamin rai a daren kuma dole sai kinyi saboda yarinta , baza ka sake samuna a waya ba , kuma baza ka sake gani na har abadan duniya ba , murmushi yayi tare da cewa ƙarya kikeyi , zaka gani shima yace kema zaki gani , yana faɗin haka na kashe wayata gaba ɗaya ,

       Koda Dikko ya sake kiran wayar Sultana yaji ta kashe cikin ihu yace Dady ta kasheni , dan dama a gabanshi yake wayar , wallahi idan bata buɗe layin nan nima zan rufe rayuwata kowa ya huta ,

     Cikin tashin hankali Dady ya dafe zuciyarshi yace Babana idan dai ka kasheni ka huta , shima Dikkon yace nima idan na mutu kowa ya huta wallahi idan bata buɗe wayar nan ba zan zama shafaffen a cikin “yan kwanakin nan , cike da iskanci ya sauko daga saman kujerar yana layi kamar yasha giya ya ƙoshi wurin firij ya nufa yana Allah kasa inyi kyakkyawan ƙarshe ashe iyakar ibar da nayo kenan ,

       Da sauri Dady ya tashi ya nufi wurinshi a lokacin harya ɗauko ruwan sanyi ya fara sha hawaye na fita daga idonshi Dady ya riƙeshi yana cewa Babana wai miye kakeyi haka ne ? Ɗora rober ruwan yayi saman firij yace kaima ka fara jiyo ƙanshi mutuwar ne Dady ? Ka riƙe wannan daren domin zai riƙa ebe maka kewa idan bana raye , riƙeshi Dady yayi yana cewa baka dai so ka bar in zauna lafiya ko ? Dikko yace gangar jiki kaɗai ake tattali ba ruhin ba , idan akwai wani wanda ba’a so ya zauna lafiya to ba kowa bane nine ,

      Wai me An mata tayi muku ne kuka tsane ta haka da yawa ? Naga shege ma mara uba ana aurenshi bare ita ba shegiya bace ba , kuma nasan namiji yana zuwa gidan karuwai ya auro mata ita a gidan wane karuwan take zaune ? Caca ² kowa saboda Babanta yayi caca sai ace bana aurenta ? Tou nima zan zama ɗan caca kuma na fara neman matan na sha giya shikenan sai ta zama matar mashayi , sassauta murya yayi cikin kuka yace na wahalar da An mata na bata azabar da duk lokacin dana tuna abinnan sai naji kunyar kaina….

     Cike da damuwa Dady yace a , a Babana da hannu Dikko ya dakatar dashi bai sake magana ba ya ɗauki robar ruwan daya fara sha ya matsa wurin kujera ya ɗauki makullin motarshi ya fice , a lokacin har 3 na dare yayi , shida Ashiru suka fita daga gidan suka koma g r a gidan Dikko ,

        Fitar Dikko Dady ya zauna ya zabga tagumi yana tunanin da bashida da gaira bare dalili ,

      Ni kuma bayan na kashe waya na fashe da kuka nima wanda bansan dalilin yinshi ba , ji nake kamar in taho katsina in haɗu da Dikko zuciyata ta tabbatarmin cewa Dikko bazai taɓa wulaƙantani ba har abadan duniya , kwana nayi ina kuka kafin gari ya waye fuskata tayi jajir saboda kuka , idanuwana sun kumbara saboda rashin bacci , ko kalaci kasa cin komai nayi ina ta tunanin Dikko ,

         Kwance yake yayi ruf da ciki ya kifa kanshi a katifa shi kaɗai yasan masifar da yakeji , bayan wani lokaci kuma ya juyo shima dai yaji masifar so yayi kuka har ya gode Allah , shi mamakin da yakeyi duk girmanshi a shekarunshi wai yake ma mace kuka , macen ma “yar ficiciyar yarinya wahalallen murmushi yayi mai ciwo a bayyane yace An mata baki da adalci kanki kaɗai kika sani , kema Allah sai kamaki bazai barki ki huta ba tunda kika hana marawuta zaman lafiya ,

          A hankali ya lumshe idanuwan shi ya fara tunanin tun farkon haɗuwar shi da An mata , da abinda yayi mata da gishirin daya zuba mata ya korashi da ruwa , wayyo Allahna me yasa nayi haka ? A lokacin ina hankalina ya tafi ? Ina tunani na ? Dama baya zata dawo dana gyara wannan kuskuren wayyo Allahna , me yasa ² ? Wai me yasa sai nine aka zaɓa ? Wai wane hauka ya kani ? Kai An mata me ya sa kin cika taurin kai haka da yawa insha Allah ubangiji bazai barki kimin wasa da rayuwa ba wallahi sai kin nemo Dikko ina nan ina jiranki bazan sake zuwa ko ina ba sai kin dawo kuma sai kin kirani nima bazan sake ɗaukar wayarki ba sai kinzo kin bani haƙuri , yafa san baya hanani kuma baya ɗaga murya shine yakeyi ,

      Ashiru yace mai gida dan girman Allah kayi haƙuri , Dikko yace kai baka da hankali na cuci yarinyar nan babu wanda yasan abinda ke tsakani na da An mata daga ni sai ita sai Allah , murmushi yayi yace An mata manya duk duniya inba ita ba waya isa ya mari Dikko ya kwana lafiya sai ita ta ɗaga hannunta mai daraja ta zabgagamin mari kuma nace ina santa tace na tsanake Dikko inba Ubangiji ba waya isa yayi wannan tsarin ? Saishi ubangijin samman da ƙassai , a hayaniyance yace sai kin dawo wallahi…….. Tari yayi yaci gaba da cewa kema Allah ya zargeki tunda na dawo daga america na gani sama lumfashin ya farayi , a wahalce yace kuma wallahi bazanyi shiru ba saina faɗa , riƙeshi Ashiru yayi cikin damuwa yace mai gida don Allah , idon Dikko cike da hawaye yace shitttttt???? ya karasa yana fiddo kyawawan idanuwanshi , Ashiru yace don Allah , cikin hayani yace kaimin shir bai ƙarasa faɗa ba lumfashin shi ya ɗage.

            Ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe Al ‘ Ameen ya ɗauki Jiddah suka fara laluben hanyar kaduna ranta a ɓace amma babu yadda za’ayi ta faɗawa wani ayi ma Dikko magana kuma tasan wallahi kamar yadda yace zai saketa zai saketa addu’ar ta Allah yasa aga Sultana da wuri , kuma ko ta ƙarƙashin ƙasa saita shiga ta fita ta raba wannan tarayya…… Murmushi


Zaune nake a gaban matar da tazo dani , kwalbar data faɗin a waya ajiye a gefenta babu abinda ke cikinta sai tsutsotsi da wasu irin mahautan layu mataccen ƙwaɗon da Babana ya faɗa gashi ina kallo , gyara zama tayi tare da cewa jira Yayata tazo tacemin ta kusa isowa , cike da ladabi nace to Aunty , ji nake dama Dikko yana tare dani shima yaga abinda nake gani yana tayarmin da tsikar jiki…….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button