INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 61-65

Wani Gigitaccen ihun kuka Inayah takuma saki tana Kiran sunan Abbi da umma yaganah tana cewa bataso Dr Anna ta barta.

Ihun nata ya sanyashi fitowa daga palonsa zuciyarsa kaman Zata Fado waya yakeyi Amma Baima kasheba ya ajiye wayar ya fito.

Ganinsu Haj umma na rarraba Ido Musamman ma ita tana tsoron kada MAJEED ya kashe ‘yar mutane sai ganinsa sukai ya fito daga palonsa Yana kallonsu zuciyarsa na tsalle
Take haj umma tasaki ajiyar zuciya a boye kafin tasamu karfin halin cewa”

To meya samu yarinyar Nan kuma da safiyar Nan?

Bai tsaya jinsuba ya wuce dakin Kai tsaye tareda bude kofar yashiga
yana ganin abinda Dr Anna ke Mata ya dakata agurin tareda juyar da Kai Dan bazai iya ganin baby Inayah cikin wannan azabar ba..

Ya Salam” yafada cikin tsananin damuwa da kaunar Babynsa
Hankali tashe yace”

Dr ba wani abinda ya kamata ne se wannan?

Dan dakatawa Dr Anna tayi sbd Inayah din Tama kasa tsayawar ayi abinda ya kamata ta dago ta kallesa tace”

Dole sai anyi Mata dinkin Gaskia,
Amma takasa tsayawa ko zaka Dan rarrasheta ta tsaya.

Qarasowa yayi ahankali batareda ya iya kallonsuba ta gefenta ya zauna tareda daukan tissue Yana goge Mata zufa cikin kulawa yace”

Baby Inayah ki Dena kukan Zata Miki ahankali….

Kuka takeyi sosai tace”

Baayi ahankali Abbi azaba ne dashi sosai nidai banaso abarni haka bazan Karaba,
Abbi bazan Karaba wlh ko dakinka Ni bazan Kuma zuwaba..Dan Allah abarni haka.

Hawayenta yake sharewa Yana rarrashinta Amma takasa denawa duk tabi ta rikice.

Kasa riqeta yayi sbd bazai iya ganinta cikin wannan halinba yace abar dinkin kawai shima bayaso.

Dr Anna kuwa tace aa wannan Dinkin shine daidai dole se anyisa.

Bazai iya ganinta cikin azaba ba Dan haka ya fito Dole umma yaganah ce ta riqeta akai Mata dinkin,

tayi ihu,tayi kuka,tayi mutsu mutsu da barin zance kala kala na cewa bazata sake yarda da Abbin ba,bazata sake barinsa yazo dakinta ba nasa dakinma bazata sake zuwaba.

Sulalewa Haj umma tayi Takoma daki sbd kunnuwanta Dake Neman kurumcewa
kala Bata samu Daman fadaba ga MAJEED din da alama ko kansa baya ganewa sbd halinda take ciki.

Kallon umma yaganah Dr Anna tayi Bayan tagama Tai Mata wasu alluran bayan na farko tace”

Kada tashiga ruwa masu zafi sosai sai dinkin ya warke
Kuma please kada ta koma gurinsa saita warke gabaki daya.

Maganunguna ta bawa umman ta fito tana kallonsa Yana zaune palon a lame saidai a zahirinsa kaman zai cire kansa yakeji tsabar Neman bugawar dayake da halinda Babynsa ke ciki.

Murmushi ta sakar Masa tareda sake fada Masa abinda ta fadawa umma yaganah ta wuce.

Bayan tafiyar Dr Anna ta jima jikin umma yaganah tana kuka da ajiye zuciya kafin akasa zubbi ta hado Mata tea da Dan chips shima daqyar taci Tasha magani ta kwanta sai bacci.

Tana yin bacci umma yaganah ta sauke ajiyar zuciya tana miqewa tsaye tareda kallon curtains din dakin dasuke qasa kaman fizgesu akai kokuma riqewa akai da qarfi suka balle.

Bata tsaya wani dogon kalle kalleba a dakin ta fice Bayan ta rufe Inayah din da bargo.

Tana fita ba jimawa yashigo dakin ganin tasamu bacci yayi kissing idanuwanta dasuka kumbura ya sake gyara Mata rufarta ya fice.

MAMUH

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button