INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH Last Page

Tashi Inayah tayi zaune tana son gasgata zancen Neesah Dan itama sai yanzu da Neesah din Tai magana tafara hasaso hakan amatsayinta na likita.

Cikin kasala tace”

Kumin scanning nakeso na tabbatar banason wani test.

Kamata Neesah tayi ta tashi tsaye da kyau suka nufi office dinta sbd na office din Dr farhat ya samu matsala.

Kwantar da ita tayi a nata consulting office din tafara Mata scanning….

Dr farhat datai suman tsaye da mamaki da firgici bin bayansu tayi
Itama Amal da Inayah da Neesah da basuma lura da itaba bare su ganet tashi tayi tabi bayan Dr farhat cikin nata tashin hankalin sbd tana cikin tsananin damuwa da tashin hankalin son samun ciki kafin Zaid ya rabu da ita akan hakan sbd yanzu da hakan yake Mata barazana da sakinta,
Tunda sukai aure no Bari bata taba yiba bayan uban cikin dasuka ringa zubarwa kafin aure gashi sunaso yanzu dasukai auren Amma Babu cikin.

6 weeks pregnant suka gani….
Cikin tsananin farin ciki Neesah ta rungumeta tana cewa”

A big congratulations to you babes,
Finally Zamu Zama mummies..

Ita kanta Inayah kasa cewa komai tayi sbd wani sanyi Daya mamaye zuciyarta lokaci Daya
Kaunar cikin sosai sbd shi din jinin Abbinta ne,
Daga qarshe dai jininsu ya gauraya.

Shigowar Dr farhat yayi daidai da AA MAJEED din idonsa akan Inayah dake kwance da ciki a bude da aka Gama scanning din Bata tashiba.

Dr farhat bayanan Dake rubuce a screen ta karanta tana sake shiga babban rudu da firgici tace”

Inayah ciki fa ake magana a jikinki???

Abbinki idan yasani kinsan abinda zai iya biyowa Baya kuwa?

Langabar dakai Inayah tayi tana kallon bayan Dr farhat din cikin Yar narke fuska tace”

Abbi wai idan kaji inada ciki ya zakayi Inji Dr farhat??

Da Ido yayi alaman” wat???
Cikin kasa fahimta ko yarda Kai tsaye da abinda tafada din zuciyarasa na dakuwa da zancen.

Cikin farin ciki Mara boyuwa Neesah tai Masa nuni da screen din scanning dasuka Gama lokacin
Ya saukar da idanuwansa akai yana dubawa.

Bai qarasaba ya waiwayo da sauri ya kalleta cikin wani irin yanayi Daya Gama tona asirin zuciyarsa yau din Dan kuwa idanuwansa Yi sukai Kaman zasu zubo da kwallan farin ciki Mara misaltuwa.

Takowa yayi Yana kallon cikin tsakiyar idanuwanta da itama shi take kallo a marairaice baice komaiba sai kawai ya rankwafo ya Kama fuskarta yakai bakinsa kan nata yayi Mata wani fitsararren kiss ya dago ya kalleta cikin wata ratsatsiyar murya yace”

I love you baby Inayah.

Daga Dr farhat har Amal da zaid da Babu Wanda yasan da isowarsa yabiyo matarsa dayaga tayo Nan duk mutuwar tsaye sukayi,

Dr farhat da Zaid na rige rigen sauko da hawayen tashin hankali da baqin ciki akan fuskokinsu,

Dukkaninsu sunji labarin cewan angano bashine ya haifeta tsintarta yayi Amma Basu taba hango wata alaqa bayan ta uba da ‘yaba a tsakaninsu sai yau dasukai mugun gani,
Gashi dai batareda anmusu bayaniba sun tabbatarda cikin jikinta nasane Kuma na aurene bana shegeba ko daga yanayin farin cikin fuskokinsu Dana Neesah.

Neesah ce tafara lura da Zaid da matarsa a kofar
Ta juyo ta kalli Dr farhat dake hawaye ba boyewa a fili…

Tadan dauke Kai daga kallonsu Zaid tace”

Dr farhat patients dinki kaman suna jiranki kila emergency ne Naga harda kuka sukeyi
Ki taimaka ki dubusu kada ciwon yayi musu tsanani.

Kasa aiki kwakwalwar Dr farhat tayi ta juya kamar wata zararra qafafunta kawai taji suna janta suka fitarda ita daga office din Suma su Zaid sukabi bayanta kowanne qafafu a mace.

Bayan fitarsu Suma su abbin da baima lura da mutane ba tun shigowarsa sbd hankalinsa akan Babynsa kadai yake
Suka fito suka nufi gida yanajin kaman zai hadiyeta sbd jinta a zuciyarsa.

MAMUH

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button