JARABABBEN NAMIJI COMPLETE

Kwana biyu da maganar tafiyarsu ,julayb ya dauketa suka tafi yiwa gida sallama…saida suka soma biyawa ta companyn sa ,yabar sallahun komai ,kafin yahau kewayawa da ita ciki,wai ta d’eban masu kayan tsaraba…kunyace duk ta rufeta musamman yanda duk inda tayi ita ake kallo dashi cikeda burgewa
A shagon kayan agoguna dasu turare ta tsaya,da sauri wani ma’aikacin wajen ya kawo mata kujera…”hajia ki nuna abunda kikeso a d’auko maki” jinjina kai tayi kafin tayi walai da ido
Cikin murya k’asa k’asa tace “baby zamu biya abj ne wajen anty jidda in za6ar mata itama?”
Zuwa saitin kunnenta yayi “take care of your self suna ta kallemun ke ,kinsan maza da jaraba”
Bubbuga k’afa tayi a k’asa “kai baby ba haka ba” daga mata gira d’aya yayi.
“Yes da gaske…ina zuwa bari ma in d’akko maki wani abu ,na manta dashi shaf sai yanxu na tuna” saida ya shafo kumatunta kafin ya soma ja da baya.yina kaiwa k’ofan yai kissing tafin hannunsa(palm) kafin yayi blowing mata iskan.
Yi tayi kamar wani abun bazata ya sameta “kafin ta k’ank’ame jiki ,tana jujjuyawa akan kujeran idonta ruf .
Tagumi ma’aikatan sukayi,wato ma su sun manta da mutane a inda suke ,hmmm soyayya ruwan zuma.
Yazo zai wucene ya hango security suna dirganiya da wata mace sun hanata ta shigo.
K’arasawa wajen yayi “kai meye hakan ba na hanaku koran mabarata ba? Ku barta ta shigo”
Barinta sukayi ta shigo tareda cewa “yes sir!”
Ketowa tayi da gudu,tana zuwa ta fad’a jikinsa ta rungumesa…wani k’arnine da hamami ya dokesa ,da sauri yasa hannu ya hanyeta kafin ya k’ank’ance ido “ke baiwar allah lafiya?”
Kuka ta fashe dashi “my love kar kace mun kamance zakiyyarka….oh yes ka sanni a fancy looking babe ko? To ya zanyi abokinka ne ya
yaudareni.ya watsar dani cikin wahala na ga cuta ba kud’in magani…plz julayb ka bari mu dawo kamar da ,karka damu da fatafatan da nayi rashin kud’ine da zaran ka fara sakar mun ‘yayan banki,murjewa zanyi indawo kamar da ko ma infi haka…tunda ji beka …dama ance in maganin ya kar6i mutum har wani k’iba yike dad’a yi da fresh”
Har ta dasa aya kallonta kurum yikeyi ,kamar ta6a66iya sai susan kai take tana dank’washi.
A haka maryam tafito ta tadda su,hannunta rik’e da jakar sark’an da ta siya
Sad’ad’owa ta bayansa tayi ta manna masa kiss a bayan wuya,kafin tasa hannu ta kulle masa ido
Murmushi yayi ya shafo hannunta”baby?” Ya fad’a dad’an zumud’insa
Dariya ta saki tana tafa hannu “yeeh ka canka”
Juyo da ita ta gabansa yayi ,kafin yace “ya bazan gane tattausan le66a da hannun matata ba! Aiko cikin matan duniya ke d’in ta dabam ce”
“Hhh salute your smartness,kaina ya fasu da yawa” jan hannunsa tayi
“Babynah me kakeyi kai d’aya anan?”
“Hummm bae baki gane wannan ba?” Ya nuno zakiyya dake raku6e uwa tsumma cikin tsananin muzanta
Ca6e baki tayi kafin ta girgiza kai
“Hmmm what so ever” ta bud’e jakarta ta ciro kud’i zata mik’a mata.
Da sauri ya rik’e hannunta “baby ba almajira bace ,zakiyya ce ,wai tazo in aureta…ta manta wulak’anci da cin amanar da sukayi mun ita da ahmed….sai ke ‘yar me gadina da muke taruwa ni daita muke hantara kece kika tainakeni …alhamdulillah yau gashi kin gyara mun rayuwata,in moreki k’arkashin inuwar aure,munayi ana zuba mana lada”
Zaro ido zakiyya tayi kafin tahau hura hanci “julayb ni zaka wulak’anta yarinyar me gadin wannan gajan ka aura,ka alkinta rayuwarta har haka?”
A gatsale maryam ta langa6e kanta akan kafad’arsa “baby to ka aureta” dariyan baki da hankali yayi mata.
“Oh???? i see ,saidai baby ko bakisona ni ina sonki,i know care in baki kishina ,ni ina kushinki,kinga ko bazan iya had’aki da wata mace a fad’in duniyar nan kuyi kishiba ,ever!”
“Nagode my man,i reserve 5 for you ,sai munje gida” tafada tana kashe masa ido ,tana wani irin lank’wasa jiki ta nufi motarsu,wani tuk’uk’in kishi na taso mata,karfa ya tausaya mata ya dawo da ita rayuwarsa ko ba da niyyar aure va,don bata manta,itace mace ta daya da julayb baiji kunyarta ba ya yabeta a ranar tare warsu daren farko!
Cikin muryan tada husuma “to vanza kina wani gallatso duma duman takashi,namiji ba d’an goyo bane,gara ki tafi asibitin masu k’anjamau ki fara amsan magani ,don shi yina shan nasa a 6oye,yabarki nan hoto…nima haka ahmed yayi mun gashi can saida yaga nayi kwandem ya samo mata cikin masu k’anjamau d’in ya aura,ya varni nan gahooo”
Fad’awa motar maryam tayi da sauri gabanta na fad’i”innalillahi wainnailaihir rajiun”
Da sauri julayb yabita shima ya shiga motar don yasan yanda yaganta yau ba lafiya!
Driver suna shiga shimaya shiga yavawa motar key,”katsaya wajen security” aikuwa suna zuwa yace “ku fitar da ja’iran can kar ku yarda takuma zuwa inda nike”
Sannan suka fita companyn
Kamota yayi kwantar akan cibyarsa
“Maryam garama kiyi hakuri aikin gama yagama,ko kin sa julayb yarabu dake kece akasa ga zawarci,talauci ga kuma cuta! Julayb kam yina da sauran damar za6o tsala²”
Oum Aphnan
[3/14, 07:13] Bamalli✌️: JARABABBEN NAMIJI
87 – 88
Zuciyarta ne tahau bata wannan shawarin
Tuni ta hau shashek’an kuka
D’aga muryansa yayi “driver to teaching hospital”
“Me zamuje yi a asibiti?”
“A’ah ki tabbatar da we are safe kawai”
“Ni bazani ba mu tafi gida”
“Allah sai mun je, Nari ga da na ganoki tunda if baki yarda da had’ubar shed’aniyar nan ba ,da banga kina mun asaran hawayenki ba a banza”
Gaddaman nan bai k’areba har Saida sukazo asibitin koyarwan dake kusa da company d’insa.
Don dole ta bisa saboda itama tana buk’atar sanin dahir d’insu ko zuciyarta zata natsu.
Saida aka d’auki blood sample d’insu kafin akace suje su jira a reception.
Cikin k’ank’anin lokaci result yayi out, likitan hannu ya kawo sukayi musabiha “congratulations result is negative so bakuda wata matsala… Amma in kuna tantama still zaku iya dawowa bayan wata uku ,sai ku k’ara sakeyi.”
Sayayyar tsarabar da ba ayi ba kenan,tace abarshi in sunje can adamawan a siya.
Tunda suka isa hanyar garinsu take ganin certain changes .
Koina solar ga kwalta shar har rugarsu ,tuk’atuk’a har biyu ,banda wutar nefa da aka jawo masu
Cikeda murna da mamaki take kallon julayb
“Hmmm bae jibi,aikin da mukasamu wannan gomnatin ta tuna damu…mun zama kamar cikin gari ,kai allah ya shiwa wannan gomnatin da albarka”
“Amin ,amin baby gaskiya kam waje yayi kyau”
Suna fitowa mutanen k’auyen sukayi masu caaaa
Kowa nayi wa julayb godiya tareda shi masa albarka.
Kallon rashin fahimta tayi
masa.kawai sai ya kauda Kai,ya mik’a mata Jakarta da ya cika mata da ‘yan dubu² vatareda ta sani ba,don yasan zataso rabon kud’i.
“Kishiga daga ciki ganinan shigowa nima,sai ayi mun iso”
Dalo ido tayi,to ai ba gidan namu
“To ki fita ki tambaya????”
“Na shigesu kardai iyayena sun Mutune gomnati ta gine filin mu????”
“Come on ,nan shine gidan baba nima nasha mamaki da nazo naga ya chanza”
“Kai yaushe kazo baka sanar daniba”
“Baby kije zan gaisa da mutane kinga suna taruwa”
Jan jakarta tayi ,tafito waje sukuku , cikin tsoro da mamaki
‘yan gidansu ne sukaji labarin zuwansu aiko saigasusu fito da gudu ,kaci6is sukayi da ita
Da sauri suka kar6a jakanta cikin d’oki sukayi cikin gidan dashi
Shikuwa saida yagama rabon kud’insa na k’aida kafin ya kirata waya ,wai tazo ta shigo dashi.
Lokacin kuwa an gama koro mata labarin aikin da yayiwa k’auyen Ashe duk shine yagyara garin ya kuma k’era ma babanta wannan k’erarren gidan .
Cikin zakuwa taje ta shigo dashi ,kafin ayi haka angama cika mata gabansa da cimmakatai iri iri ,banda soyayyen naman zabbi da dafaffen k’wai.
Yaci sosai kafin ya bi d’aki d’aki ya gaishesu ,sannan yayi masu sallama with intention gobe zai zo da wuri su wuce.
Har taxi d’in da sukayi tasha ta rakasa dukda bata kai ga yimasa godiya abunda yayi masu ba,kawai she reserve it ,sai sunje gida.
Anyi firar yaushe gamo ,saida suka k’ure a daki da mamanta kafin take shaida mata sun zo yimasu sallama ne zasuje gayar da dangin mijin ta da hutun amarci.
Shiru maman tayi tana jujjuya abun a ranta ,tsoronta d’aya Kar zancen mutane ya tabbata,dasuke cewa sun yi cinakin ‘yarsu sun kar6i kud’in harda canji
Ta6ata tayi “mama akwai damuwa ne?”
“Aah , dama dai inata jin tsorone ,amma kiyi hak’uri zan fad’a maki ,amma karki zargeni da rashin yiwa mijinki adalci watau abun ne yina bugamun kai,mun zama abun tsegumi a cikin karkaran nan ,nima kuma na fara tsoro saidai inda Allah ba komai…watau kinsan meke faruwa…yanzu haka bayan wannan gyaran garin da yayi Mana,ya bud’ewa babanki k’atuwar masana’anta daga wajen gari…ana fidda madaran shanu ana maidashi ta kanti ana d’urewa a buhu…man jikin sa d’inma suna wasu amfanin dasu na davam… Ya zuba masa maaikata harda wainda ba ‘yan kasan nan ba ,wai duk a k’ark’ashin sa suke ya bashi wajen halak malak,yanzu haka babanki gini yike yi daga cikin garin yola wai zamu tashi anan mu koma can yanda zai fi masa kusa da wajen aikinsa.
Anya haka zatayiwu babanki jahilinsa dashi ,ba zaginsa nike son yi ba amma a basa irin wannan waje ,ai dole mu shiga zargi …shikuwa ko a jikinsa fantamawansa kurum yikeyi…amma bakomai na barwa Allah za6insa.
“Ayya mama na yarda da julayb dari bisa dubu ,saidai mugu bayida kama,don haka zan hak’ura da tafiyan nan kurum,ni dama bason zuwa wajen danginsa nikeyiba,don na lura basu sona”
“Akul d’inki…kije ba abunda zai faru inshallah, sannan gameda danginsa zan baki addu’oin tsari da na mallaka amma ki tunamun in zaki tafi zan rubuta maki wannan zantuttuka da mukayi , Ina so suzamar mana sirri”
“Shikenan mama allah ka shige mana gaba.”