JARABABBEN NAMIJI COMPLETE

Washegari suka wuce Lagos cikin kewar iyayenta ,kwana biyu tsakani suka wuce egypt tanan suka fara ,dama yayi masu scheduling daga Egypt ne su wuce America,sai Australia ,china sai su sauka a dubai daga nan su wuce saudiyya…tunda Egypt yafi kusa damu Africa ne,sai ma su tsaya suyi umrah da aikin hajji kafin su dawo.
Aikuwa maryam ta shana taga gari sun 6arji soyayya ,anan ne tayiwa julayb godiyan duk kyautatawan da yayiwa iyayenta batareda ko sanin
taba.duk ko k’asar da sukaje sai tayi hotuna tayo tsarabar irin abubuwan k’asan da ita kanta… status kam kullum yina kar6an sababbin pix na amarya da ango.
Saida sukayi sati biyu da kwana hud’u kafin suka wuce sa’udiyya ,a lokacin batajin ko shayin turanci , abunda ta gane shine ka kwakwa6a indai zaa gane ai shikenan.
Garin sa’udiyya
‘karfe goma na daren garin suka sauka a k’asar.
Ouk Aphnan
[3/14, 07:13] Bamalli✌️: JARABABBEN NAMIJI
89 – 90
Amma tantarwai ko ina yike kamar rana,ga yara ‘yan k’anana dake ta wasanninsu a k’ofar gidajensu …kasa daurewa maryam tayi saida ta 6ara tayi magana “baby kajibi yara k’arfe nawa na dare suna wasa a waje basu tsoran a sace masu yara,kaf cikan sufa ba mai shekaru bakwai .
Ga gari ko ina duwarwatsu ni tsoroma zanji in na d’aga kaina kalli wainnan bak’ak’en duwarwatsun.”????
“Hhh babe akwai tsokana to aibaki saniba da darana mukazo mutum 1 bazaki ganiva sai masu hidimar gidaje saboda garin akwai bala’in zafi ,bama iya fitowa,anjuyane yanzu shine lokacin mu,tamkar rana muke kallon sa,kuma sa’udiyya ba kamar sauran k’asashe bane akwai tsaro sosai”
Jinjina kai kurum tayi”lallai duniya juyi juyi,haka kowa da kiwon da ya kar6esa.”
Sun samu karramawa ta musamman ilahirin mutanen gidan suna falo zaman jiransu,suna sallama kuwa,d’uuuu sukayo kansa suka rungume kotakan ta basu biba…sai Abby ne ya kamota
“Kun kamo wannan garjejen kun rungume, Kun bar bakuwa sagale da hannu.”
Gabadaya yaranne suka yo kanta ,banda uwar gayyan
“Ayyah anty we are sorry. ..yayan ne mun dad’e bamu gansa ba”
Murmushi tayi tana satan kallan ummy raudha “ayyah bakomai”
Jan hannunta sukayi bayan an gaggaisa suka kaita d’akinsu
“Anty ki zauna anan tare damu ko?”
“Uhm “
Zaro ido sukayi “uhm what? Me uhm yike nufi? Baki yarda ba ” “no i agreed” tsalle sukayi suka rungumeta
“Shikenan munajin dad’inmu…anty kiyi wanka and freshing up,kizo muci abinci mu fita yawo”
“To sarakan yawo ba inda zataje baku ganin ta gajine…yanzufa mukazo k’asar,ai kwa bari sai gobe ….”
Duddurke k’afa suka shiga yi “Yaya mune mayawatan?”
“Yes a ba mata na waje ta kintsa”
Fita sukayi suna tsallen murna kamar k’ananun yara. . ada suna jin haushin ta amma yanzu kallon farko sukaji sonta a cikin ransu
D’aga ido sama tayi tanayuwa Allah godiya
“Nasamu kar6uwa a wajen ‘yan gidan duka ,saura uwar gidan”
Matsowa kusa da ita yayi ya rungumota…”baby ya kika ga family na?” “Hmm sun burgeni ina sonsu”
“Kowa yaganmu sai ya so mu , haka kuma kema kike”
“Aah ni awa? Ga larabawa me za ayi dani bak’ar fata”
“Come on, karki wulakanta mun ke” sassauta murya yayi “baby inaso zan ci?”
“Hmmm zakaci me?”
Kashe mata ido d’aya tayi kafin ya shafo mararta “nan nike nufi”
Zubut ta mik’e “wa? Kai baka gajiya? A gidan mutanen? To bazan iya ba”
Dariya ya saki zai magana aka turo kofan ,dan sunkuyar da kai yayi yina sosa k’eya .
Dallara masa harara tayi
“Sai ka barta tazo d’akina mu gaisa a tsanake kawani zo ka kanainayeta”
“Mom kin daina sona ashe?”
“Eh d’in tafi bani waje,kinga d’iyata zo muje”
A sullu6e ta taso ta biyota.
Rungumo kafad’arta tayi suka wuce can part dinta
K’ulhuwallahu ta tofe ta dashi k’afa uku
Da li’ilafiy
Tambayoyi kam tasha shi Kala da kala ,wani tasan amsa wani tayi murmushi ta duk’ar da kai,saita harbitsa mata ingausan larabci da turanci .
Tayi observing d’inta tas tayi, akwai lack of knowledge a tare da ita saidai tanada kunya da kawaici ,sosai tayiwa julayb sha’awarta…abunda ya Kamata shine a bata training
Don haka dole ta zauna tare da ita kamar yanda bazata bar yaronta ya kuma tafiya ya barta ba
Topah ya kenan,mairo tazo sa’udiyya ba hanyar komowa …….
Oum Aphnan
[3/14, 07:14] Bamalli✌️: JARABABBEN NAMIJI
BONUS PAGE????
91 – 92
Wannan page d’in bonus ne ga kaf masoyan julayb da mairo,ku tayasu murna sunyi abun kai,duk masoyan mairo da julay kai dama littafin jarababben namiji gaba daya ,in wannan fejin ta riskeki ki turawa wasu wainda basu samu biya ba su karanta,ko k’wanyarsu ta fad’a???? din nasan akwai mak’ek’e masu jiran na kyauta….lolz 09065990265
Twins d’insu julayb ne suka shigo Asim da Asib daka gansu kaga kamanni ,saidai shi asir muskiline original asim kuwa warkam sai dai sune ‘yan gayun sa’udiyya…kallon farko dole ya fizgeka dukda komai nasu iri d’ayane saidai banbancin rawar kai
“Hyy mumy we are back” sukaje da gudu suka rungume ta at the same
time.tareda kowa yina rege regen yimata kiss.
Dariya tayi kafin ra riko hannunsu a tare,suka zauna aside to side d’in ta.
“My loves bakuga antynku bane?”
Waiwaigawa sukayi,kafin suka hango ta kan resting chair tana aika masu da sakon murmushi har ranta take k’aunar wainnan ‘yan biyun…saidai ita tambayerta shine laylerh da nihla suma twins ne ,ko ko gwarne momy tayi????? This is difficult to ask????
“Wow what a surprise? Antyyy?”
Suka zo da gudu suka fad’a a jikinta
“Heheheyy stop,manyan kawai girma ba hankali, karkuyi muna asara , have nt you see , she’s conceived”(baku ganin tanada cikine?)
“Wayyo dad’i finally zamu samu baby muna zuwa dashi club da masallaci tare,muna sa kaya iri d’aya komaida shi…sorry anty ina akhy?”
Murmushi tayi ,amma tayi mamakin rudewarsu da murna da sukayi dakuma maganar baby da taji sunayi
Turo kofar yayi dagashi sai gajeran wando da singlet
“Gani abani matana ,in rarrasheta tayi barci,don nasan yau tasha squeezing kowa ya damuk’eta”
“Hooopp bros ka ganka kuwa?…”cewar Asir ,kafin duk su biyun su d’auka magana a tare “you look fresh,giant nice looking handsome,so awesome like your darling wife????”
Wani bok’are baya yayi ,cikin bragging (kuri) “Ah to ya san ranku , Yara aure kenan ,kuma kuyi maza ku k’ara girma ,ku gama makaranta kuzo ku samo mata musha biki…ni kunga na zama cikakken mutum abunda ya rage mun shine madam ta samu ciki …oushhh ta sulluro muna fine fine kids????”
Wurgo masa throw pillow tayi “D’an nema zoka fad’amuna kaid’in matarka nada ciki ,to ai ko baka fad’a ba mun gane ehem …kuma we must to celebrate????”
Zaro ido yayi waje kawai yayi dawara ya kalli mairo data kulle ido da sauri ,????sai yanzu ta gane zancen
Kan ummah raudha yayi da gudu ya rungumeta
“Momy are you serious?…to ya akayi banganeba …uhhhhh rejoice????”
“To yakamata ku gane banbancin tsohon hannu da sabon hannu,ni ku kyaleta ma ta huta hakanan ,duk ku fita zatayi barci”
“Yawwa mom gara ki fad’a masu asim ku barta ta huta ,baby zo muje kinji” yawani denying kamar bai fahimci mai take nufi ba
“Wuce bani waje,har kai nike nufi ,anan zata kwana don baa haik’ewa mai yaron ciki ,kaje kayi mana asara”
“Yawwa fada masa Oumma saidai duk mu tafi mubarta” ganinfa da gaske take yasashi ‘daure fuska,idonsa ya wani kad’a
“Oum da gaske kike, to wa zaki bari da abbey d’in?”
“Aah mai ruwanka, lokacin mu kula da surukanmu ne yanzu oya wuce zo kaimata sallama ka tafi”ta fada tana hankad’a su asim waje.duk dariya sukayi su ka wuce side d’insu nihal su k’yank’yasa masu albishir.
Itakuma ta shige wani corridor dazai linking d’in ta da personal kitchen d’in ta,taje ta hau har had’a mata kayan ni’imarsu na larabawa a d’an k’aramin kofi .
Zallar madarar ruwa ta zuba a kofin amma mai d’umi sai d’an zuma cokali d’aya,ta barbada garin kanunfari shima cokali ,sai ta d’ebo wani magani ta tsiyaya ta hau bugashi da cokali. Sarau sarau yayi kamar tsumi yina tashin k’amshin dad’i.
Julayb kam Zuwa yayi kusa da mairo ya zauna ,da sauri tad’an matsa ,mintsinin ta yayi.
Cikin rad’a yace “kiji tausayi na ki taso mu gudu a matse nake wallahi yanzunnan muke tareda abokina saad yazo muna murna ya bani wani tab nasha ,yanzu haka na fara jina some how bansaniba ko maganin k’ara sha’awane ya bani ,ya fara dissolving a jikina yanzu”
dariya tai masa tareda gwalo , sannan ta nok’e kafad’ arta.ta bude baki zatayi magana kenan saiga su Layla sun shigo da gudu
“Antyyyyyy ?”
Suka k’wala kiran sunanta kafin duk sukayo kanta zasu fad’a mata a jiki
Wani mugun tsawa ya daka masu kafin yace “kuna ta6ata zan shek’e mutum da mari ,bakuda hankaline eheee”
K’am sukaja suka tsaya rik’e da hannu .
Ido yayi rau rau zasuyi kuka.
Mom ce tafito da sauri Jin tsawansa ,tana rayawa a ranta “mai hali bayi fasa halinsa”
“To…to…. what’s going here … haven’t you hear the fines?” Ta kalli julayb tana tambayarsa.shikuwa kya6e fuska yayi tareda girgiza kai.
“Ohk shine zaka fanshe haushinka akan auta da jikalle(tana nufin Layla da take jikan yayarta duk da a Indonesia suke hutune ya kawo ta wajen nihla da kullum suke lik’e da juna in wannan yazo hutu wannan karon wata karon d’ayan ta tafi k’asar d’ayar)
To ba wanda zanbaka fuska ka wulakanta mun inama laifin sunzo tayaku celebration…kinji maryerm taso muje”
Ta jawo hannunta suka wuce hanyar corridor d’in
Buga kansa a lallausan cushion d’in yayi “Ohhhhh shit mum zata k’ure mun maleji”
Dariya suka saki kafin Layla tace “uncle sorryyyy????”
Suka k’alk’ala waje a guje.
Biyosu yayi da gudu yina ciccillo masu throw pillows , bam suka 6amo k’ofar.
Dawowa yayi ya samu waje ya rafka tagumi???? d’insa tana jan ruwa yina dad’a kumbura…zabura ya shigayi abu na tsunguninsa.
“Ai wallahi bazan yarda ba ,bara nasan abunda zanyi” ya mik’e ya nufi corridor d’in da yaga sun shiga ita da umman.
Oum Aphnan✍️
[3/14, 07:14] Bamalli✌️: JARABABBEN NAMIJI
93 – 94
A can d’akin kuwa oum tasa mairo tayi ta shanye maganin da ta had’a mata
“Daughter from now a kowanne dare kina shan wannan had’in da nayi maki ,har zuwa cikin ki yayi k’wari for at least 3 months, inba wannan ba,zuma ma da ruwan zafi kad’ai ya isah banda inserting unnecessary abubuwa da ka iya janyo maki matsala kin jini ko?”
A kunyace ta gyad’a mata Kai.
Yanzu bara in d’akko maki kayan had’in ,ki adanasu kafin nan sai in aiki su nihal su d’auko maki night dress d’ inki.keda had’uwa da julayb sai kun tare a gidanku”
Jinjina kai tayi kafin tace “Nagode ummah” amma ranta na mata rawa,sai mun tare a gidanmu? Bayan gidan da muke dashi a lagos?… can’t understand.
Tana bada baya julayb na shigowa
Yina zuwa ya sureta ,ya d’aga cak kamar ‘yar tsana
“Zaki sani ne yau,kina sane ina jiranki ,kinsan condition d’ina amma had’uwa da ‘yan gidan nan ya koya maki rashin tausayi na ko?”
Cuno baki tayi “ni ka saukeni ko in kira ummah”
“To saime ? Mutum da matarsa a hau yi maka seizing kamar wanda yayi laifi? Kita kiranta”
Haka har suka kai bakin k’ofa,hannu tasa ta Ri’ke k’ofan
“Habawa d’an arziki shirin albarka…kayi hak’uri kar ka jamun abun kunya gidan surukai…kaji d’an kirki na?” Ta fada cikin kalailaya murya , kamar wacce take rarrashin babyn da akeso yayi barci
“Nak’i wayon saki mutafi”
“Kwalla Kiran sunan mumy tayi cikin sigar wasa bata san muryarta zaiyi k’ara ba” aikuwa sai ga mum ta dawo da sauri tana Kiran “Na’am ya akayine ‘yar albarka?”
Kawai sai gashi tayi kici6is dasu a bakin k’ofa
“Kai lafiya cikata mana????”
Sauketa yayi a hankali kamar wanda ya tallafo k’wai kar ya fashe
“Umma plz ki barta tazo muje ,wallahi nagaji da yawane , massage kawai zatai mun ta dawo…just few minutes????”
“Hmmm massage? Lallai julayb ni kake,kallo kana fad’amun zakaje da matarka taima tausa?…yau ka fara dawo wa daga tafiya eheee?….to amma tunda kun nuna mun k’ok’on usuli ,ja matarka ku tafi” ta fad’a tana tafa hannu.
Fyallawa da gudu mairo tayi ciki “Oumma ba ruwana,ni na fi sonki a wajenki zan kwana”
“Kajimun yaran zamani,ni zaku had’awa plan ? Sarai nasan kin fison kwana da mijinki zo ku wuce allah bamu lafiya????”
“Kinji ummah d’in nan ku haka akayi maku?” Ya fad’a cikin k’unk’unai
“Me kace?”
Sosa k’eya yayi “momy i just said thank you” ya wuce yaje ya janyo hannunta ,aikuwa zugwui zugwui tabi bayansa suka fita
“Hmmm i love this couples allah ya k’ara masu zaman lafiya amin”