JARABABBEN NAMIJI COMPLETE

Baba dake maƙale tun shigar Mairo tajikin window tana ganin ta na ganin an wurgota itama ta fito daga maɓuyanta tana cizon yatsa.
Cikin sharɓan kuka Mairo take shaidawa baba takai kayan abincin
Cikin munafurci tayi ƙasa da murya ta kamo kafaɗar indon tace “Meya faru naga kina kuka?”
Dariya tasaka kafin tace “laaa bakuka nake ba ,bakomai”
Gyaɗa kai tayi
“Ai na Aza ko dukanki yayi ko wannan shegiyar karuwar tasa laluwa jaraba”
Taɓe baki takumayi kafin ta ƙara girgiza kai
Haushinta ne ya ƙumeta gadai dukkan alamu yarinyar nan zatayi zurfin ciki ina mata kallon wawiya wawiya ,to anya haƙata zai cimma ruwa…?紐♀️
Dawowa tayi daga tunanin da tatafi ganin mairon ta raɓata zata wuce
“Kinga Mairo tsaya muje kicin inbaku abincinki dana babanki ,Ni dama bason shiga hulɗan kwarton nan mike son yi ba , Allah Nagode maka kuku gobe zai dawo ya dawo yakarɓi aikinsa inji da gyaran gidan yafi mun sauƙi ai ƙazantan da baka ganiba tsafta ko Mairo na?”
Fuska ba yabo ba fallasa ta jinjina mata kai
Itama jinjina lamarin yarinyar ta daɗa yi a cikin ranta
Har sukaje kicin tabata kulan abincinsu batayi maganaba
Cikin wasan dare irin na makiran mata tace “Mairo ro,Mairo mairo kunama ga daɗi ga harbi…kinaji kinga Ni kaɗai ce dattijuwa kina zuwa wajena ina koya maki turanci ko ,Ni kuma zansa Alhaji ya barku ku zauna anan ke da babanki , ke harma insa yayi masa ƙarin albashi”
Tsalle tadaka ta juyo ta ajiye kulan agefe fuska fal fara’a take tambayan ta Allah baba?”
“Ina maki ƙaryane ?”
Girgiza kai tayi
“To kitafi kuci abincin ku kuyi Sallah sai kizo bayan ishai muyi kallo a ɗakina ammafa na turancine sunansa evil eyes ,kinga muna kallo ina fassara maki abinda suke cewa”
Kama gaban lebatun rigarta tayi tana taunewa kafin yaje ta sunkuci kulan tana dariyar murna ta ƙalƙala a guje don ta shaidawa babanta.
Muje zuwa a next UPDATE
Tambaya????????
yaya makomar Mairo anya yanda naga julayb yayi fushi zai barta ta cigaba da zama masa a gida? _waye marketing manager ɗin julayb kuma wani rawa zaitaka a rayuwar julayb kai harma da littafin a gabaɗaya ….Hmm Nidai ma hango wani abu dukda masu karatu basu luraba i know
_Naji julayb yina cema Zakiyya no turanci means mene yafara koyon Hausa ne???
While any way????????
Duk kubiyo ƴar
mallawanku zata warware maku zare da abawa????????????????????????
Sai dai kuma kashhhhhhh
GAGAB!????
FREE PAGE YA ƘARE SAURA NA KUƊI NEMI NAKI A FARASHI MAI ARHA DON CIGABA DA ƁARJE GUMUNKI
KINSHIRYA BIYA??? TO BIYA TA WANNAN NUMBERN 09065990265 KATIN MTN NA NAIRA ƊARI ₦100 KO KUMA IN TRANSFER NE KO VTU ₦200 SAI NAJIKU MASOYAN AMANA HASSENART NAYINKU TSAKANI DA ALLAH, THANKS FOR ALL YOUR COMMENTS,FORWARDING, SUPPORT AND MAXIMUM COOPERATION YOU HAVE GIVEN ME TOWARD THIS JOURNEY .THANK YOU ONCE AGAIN????
✍️Oum Aphanan
JARABABBEN NAMIJI
Na…Oum Aphnan????
ALHERI WRITERS ASSO.????️
A .W. A
https://www.facebook.com/groups/524085991963693 /
16 – 17
Tana shiga ɗakin ta tadda babanta yina karatun Alkur’ani ,sallama tayi taje gefe ta aje kular abincin ,itama tafita taje ta bayan backyard ɗin gidan tayo alwala a wajen tank ɗin kafin ta komo ɗakin .
Still yina zaune akan tsohon Morocco (buzu) ɗinsa yanzu yadaina karatun ƙuranin amma yana ƙofe yina jan carbi .
Raɓawa tayi daga gefen sa ta kwanto ɗankwalinta ta shimfiɗa ta yayo wani tsohon zani ta rufa dashi ta tada sallah
Bayan ta idarne itama ta zauna tana jan ƴar madaidaiciyan carbinta ba kamar na babanta ba mai dubu .
Sun jima a hakan kafin ya ɗaga hannu yina koro addu’a a bayyane itama ɗaga hannun tayi tana amsawa da Amin har ya shafa itama ta shafa .
Da azamarta ta janyo kular abincin ta turawa baban gabansa.
“Baba gashi inji baba mai shara”
“To sannu mairamuu…sai dai inaso inja kunnen ki game da gidan nan,wato Allah ya hana bankaɗe bankaɗe saidai kuma shi yace kakare kanka…wato mairamuu Allah ya jarrabe mu da wannan mutumin a matsayin ubangidana saidai hmmm Allah ka shirya, mairamuu inaso ki kauda kai akan irin matan da zasuna zuwa gidan nan don ba nagari bane,kuma haɗuwa dasu ba alkhairi ,don haka ina horonki da ki lizimci zaman ɗaki fiyeda zama a harabar gidan nan , sannan akul ɗinki da shige shige kina jina ko har zuwa in karɓi haƙƙinmu mubar masu gidan su kin fahimceni?”
Jinjina kai tayi masa batareda tace komai ba
“Yawwa ƴar albarka to jawo mana kwanon abincin mu taɓa”
Dakanta ta zuba masa a roba kafin tarage kaɗan ta faraci dukda zuciyar ta a tsinke yake da zaran ta tuno yanda taga ogansu da halinda yasa kansa a take sai gaban ta ya tsinke ya faɗi,ahaka ta cuccusa abincin don kar ace bata ciba bawai don tana son ciba”
Daga ƙarshe ta ture robar ta miƙe.
“Badai har kin ƙoshiba ?”
“Eey na ƙoshi abincin ba daɗi wani wari wari yikeyi mara dadi”
“Ayyah kiya haƙuriy Mairo na ,ga garin kwakinan da sukari ki sha”
“A’ah baba kabarshi sai zuwa anjima”
Duk firarrakinnan da yarensu sukeyi, anan sukayi sallan ishai tayi shafai da wutr ta fara hamma tana gyangyaɗawa
A lokacin har taran dare ya wuce
Daga wajene baba tazo ƙofar ɗakin tana knocking masu
Baba ne yafito yina waye?
Amsa masa tayi daga wajen sannan ta daura da cewa”Mairo nazo kira tazo mu kwanta”
Buɗe ƙofan yayi kafin ya ƙwallawa Mairo kira ,gigif ta farka tana murtsuke ido
Ƙara leƙo da kansa ɗakin ya kuma yi kafin yace “Mairamuu ga babanki tazo ku je kwana”
Tashi tayi tana ƙunƙune tareda turo baki
“Ni baba tareda Kai zan kwana “
“Habawa ke ƴan nan inakika taɓa ganin anyi hakan? Saika ce muna gaidan anna? Kinga zo mu tafi daga yanzu komai naki yina wajena …”
Waigowa tayi ta dubi baba ɗan fillo
“Baban Mairo nayi magana da maigidan yace ya amince ku zauna kafin ayi albashi ƙarshen wata kunemi gidan hayan amma kafin nan Mairo zata zauna a wajena da kayanta da komai”
“Nagode Allah ya bar zumunshi ,yanda kika taimakemu Allah ya biyaki da aljanna” ya faɗa yina matso ƙwalla
Murmushi tayi kafin ta janyo hannun Mairo tana amsawa da Amin.
Duk yanda baba mai shara taso jin cikin Mairo abun ya faskara daga ƙarshe ma kawai sai ta ɓingire a wajen ta kama barci .
Tsaki taja ta babballarawa mairon harara kafin tajata zuwa kan katifarta itakam tuni ta kai London a barcinta so batama san tanayiba.
Gari na wayewa baba ta miƙe ta tashi Mairo sukayo salla kafin ta fara aikin da ya kamaceta itama mairon na tayata a haka sukaje kicin haɗa abun karyawa.
Dukda dai fir ta hanata ta taɓar masu kayan abinci acewarta wai bata wanka ,in takoyi wanka itakuma zatana koya mata girki ko bayan kuku ya dawo
Jinjina kai tayi kurum kafin tace “To in yanzu na je nayi wankan fa zaki koya mun?”
“Eh me ze Hana ,muje innuna maki yanda ake operating kayan toilet ɗin”
Bayin masu aiki takaita ta tsaya tana nuna mata yanda ake haɗa ruwan zafi,plushing ,shaya ,washing machine da sauransu.
“Cif kinsan da innaga wancan tukunyan ɗaukafa nikeyi randan ruwa ne”
Dariya ta saki “a’a Mairo wannan toilet ne ,akwai squart akwai na zama , wannan na zamane amma kinga masu amfani dashi sunada yawa bani baki shawaran kina zama akai kodai kafin ki hau kiyi plushing sannan ki yi squart ko kuma kinemi potty kurum zai fi”
Sosai tayi mata bayanin komai kafin ta tafi ta bata waje tayi wankan
Wasu Yagutsatsen kayan saƙi ta saka sun cuccure waje guda daga gani basu taɓa sanin gugaba
Rigar ɗingilalliyace iya ciki sai taja zani ta ɗaure har cikin .
Ta murtsuke manta basilun ƴar haɗin gida Mai suna dangwali yarɓa taka tafito tana shining ƙafa caɗai caɗai kamar ɗanwake tabi fuskarta tayi masu ɗigeɗigen Fulani tasaka jan jambaki mai green ɗin gida. Ta kuma murtuka gashin kanta waje guda tasaka abun kan ta naɗan goshi.
Abunta dai aca an acaan????
Da murnarta tafito da ƴar sandan ta a hannu
“Baba kinganni?”
“Wai wai wai cancaɗi irin wannan gayu haka saikace zaki ƙwacen miji”
Dariya tayi kafin tasa hannu ta rufe fuskanta????
“To yanzu me zanyi?”
“Kash Mairo nagama girki saura ƙarasawane amma muje ki tayani mop da gyaran ɗakuna”
Take faraarta ya ragu kafin tace “uhm kinji Bara inje wajen babana a get kafin masu gidan suzo fita suna masa ihu”
Murmushi tayi mata kurum
Itako da sauri ta fita kamar za’a janyota
Sarai baba ta gane dalili amma fa hakan bai dameta ba don inhar kere na yawo zabo nayawo watarana za’a haɗe ,kazalika komin wayaun amarya sai anshaa manta