JIDDATUL KHAIR 49
sudden from who I knew her to be, kamar ana xugata kullum, kinga bata mutunta ni bata kunyar gaya min ko wani magana ya xo bakinta, sannan i wish u can come one day ki ga yanda ta mayar min da gida, kawai fa sai dai tayi wanka ta fesa turare abinda ta iya kenan, tsaftace muhalli Zero, girki Zero, ibada Zero, kullum sai nayi fama da ita a kan sallah, I’m so tired and fed up Mum, ko wata biyu fa ba ayi ba, har xullumin dawowa weekend nake wllh Ummi” Ummi da tayi shiru tana kallonsa taji tausayin d’an nata
amma taki nunawa, can tace “Toh me yasa baxa ka daukar mata mai aiki ba?” Da sauri ya kalli Ummi yace “House help kuma Ummi? Warce ta xauna kafin ita a gidan duk da karancin shekarunta da rashin wayewarta ai ban daukar mata mai aiki ba, kuma komai na gidan ita ke yi, sannan ni ban ta6a dawowa weekend naga ba dai dai ba” Ummi dake kallonsa kasa kasa tace “Wacece ta xauna kafin ita?” Shiru yayi bai ce komai ba, Ummi tace “Wai Jiddah kake nufi?” ya daga kai yana kallon Ummi amma bai ce komai ba, Ummi ta tabe baki tace “Ni a iya sanina warce ta xauna kafin ita ai ba matsayin mata ka dauketa ba a
lokacin ko? Wannan kuma matarka ce ta sunna….” Shi dai bai ce komai ba, Ummi ta ci gaba tace “Don haka sai kayi hakuri da duk abinda ka gani, da yanda ka gani, na farko dai ba wani ya nemo maka yarinyar nan yace ka nemeta ka aura ba…” Ya marairaice mata yace “Ummi to ai ni da muka hadu da ita da farko ba wai soyayya muke ba, kuma ni ban ta6a tunanin xan ma aureta ba, kawai dai ta kan kirani mu gaisa ne time to time, sai kuma WhatsApp chat, a airport din Abuja muka hadu taje gun uncle dinta, ni kuma mun
sauke jirgi, and she requested my digit na bata kawai don ban iya walakanci ba, sai kuma coincidentally na dawo wani weekend na ganta a gidan nan ta xo gun Aunty da aunt dinta ashe Mum dinta close frnd din Aunty ce” Ummi dake ta kallonsa tace “Sai aka yi yaya? Sai aka ce ka so ta dole har ka aureta?” Yace “Aa Ummi but Aunty ce ai…” Sai kuma yayi shiru, Ummi ta tabe baki tace “Kaga Aliyu rabani da wannan labarin da na sani, yanxu dai kawai kayi hakuri ka nema mata house help, da xata dinga tsaftace maka
gidan ka, sai kuma ka ci gaba da hakuri da sauran halayen nata tunda dai auren soyayya ku ka yi ba auren kiyayya ba” Bai iya yace komai ba, Ummi dai sai kallonsa take, amma can kasan xuciyarta tausayinsa take, she understands what he is going through, barin shi da yayi detesting kazanta with passion, ita har ta mance rabon da ya shigo dakinta balle har ya dade haka yana xance da ita kai tsaye, Ya d’an ja tsaki
underneath his breathe yace “Karamar yarinya ma da ta kusa doubling age dinta warce ta tashi a ghetto bata irin abinda take yi na kazanta wllh, tun daga balcony nake jiyo kamshi lkcn da yarinyar ke gidan idan na dawo gida, for once ban ta6a shiga kitchen naga dirty utensils ko daya ba, ni har kunyar wani nawa nake ya xo gidana yanxu, dama a garin nake sai in dinga gyarawa ni kullum, kawai ita abinda ta sani sai
tayi wanka ta fesa turare ta xauna tana danna waya, sai tara kawaye a gida” Ummi tace “Toh wai ita kuma wannan karamar yarinyar da kake sa wa a baki kake comparing da matarka meye hadinka da ita ne, why don’t u face ur life ka daina mentioning dinta a lamarin ka, did she have anything to do with u again xaka sa ta a bakin duniya” Ya kalli Ummi amma bai ce komai ba, Ummi tace “Ni ka tashi kaje ka same matarka ka bata hakuri ka dauketa ku tafi gida, Allah ya ci gaba da daidaita ku, ba ruwana da matsalar cikin
gidanku, it’s something u should have known before marrying her” Abuturrab yace “But how mum, kullum fa fes fes xaka ganta a titi, waye xai san xata yi haka?” Ummi tace “Allah ya kyauta” Ya kwanta saman gadonta yace “Ni sai na ci abinci Ummi, kuma ba yanxu xan tafi ba sai after isha, kullum fa sai nayi takeaway din abinci bata girki” Sharesa Ummi tayi ta mike ta nufi kofa ta fita, Aisha ce ta kawo masa
abinci dakin, tana ajiyewa ta juya ta fita, shi kam ko kallonta bai yi ba, can ya mike ya sauka kasa ya dau plate ya fara dibar abincin. Aunty ce tsaye bedroom dinta tare da Aneesah dake xaune gefen gado tana kallonta, bata dade da dawowa gidan ba tun fitar da tayi bayan Hajja ta tarwatsa meeting din daxu, Aunty ta xuge jakarta bayan ta dau abinda xata dauka a ciki sannan ta dawo kusa da Aneesah ta xauna ta ajiye mata kwalaban turarruka uku a gabanta tace “kinga wannan, sai bayan mun koma asibiti ko xuwa gobe sun kara tabbatar maki babu wata matsala sannan bayan kin koma gida sai kiyi amfani da su” Aneesah
tace “Aa kawai gwara ayi sabon dinkin Aunty, ni ina ji a jikina ba dai dai nake ba” Da mamaki Aunty tace “Kamar yaya?” Aneesah tace “Ni dai kawai ayi hakan, ko nawa ne xan biya ai” Aunty ta tabe baki tace “Toh shkkn, amma wllh Aliyu yayi mugun raina maki wayo, sannan ni banga laifinsa ba kece babbar wawuyar da kika yarda wai yana da matsala, a gidan ubanwa yake da matsalar mutumin da har gidansa kin sha xuwa ki kwana? Ko ke duk xuwan da kike gidansa a Abuja kin ga alamar yana da matsala?” Aneesah ta tabe baki tace “Ban ta6a ganin haka ba wllh, kawai shi dai baxai yi intercourse ba sbda gudun sa6on Allah amma ba don bashi da lafiya ba ko wani abu, amma babu abinda baya min ai, ce min yayi of recent ya samu matsalar” Aunty tace “Wllh ni ban yarda da kanwar uwar nan tasa ba don ita ma waye bai san tana shige shige ba kilan taje ta hango aikinmu ne tasa aka lalata, shine yake ta maki hanya hanya…” Aneesah tace “Toh ai da kin tambaya inda kika je daxu” Aunty tace “Wllh na manta shaff ban tambayi mutumin ba, amma akwai wani da xan kira anjima a benue, xai sanar da ni komai, yanxu kuma sai ki kirgo dubu talatin na turaren nan ki bada” Aneesah tace “Ina na gansu Aunty, har yau fa nace maki kudin nan da kika ce in tambayesa sai min yawo da hankali yake, yace yau yace gobe” Aunty tace “Rabu da shi don ubansa, xa
muyi maganinsa nan ba da dadewa ba, muna nan dake sai account dinsa ya dawo hannunki gaba daya” Kwankwasa kofar dakin aka yi, Aunty ta jawo pillow ta ture kananun kwalaban turaren a karkashi da sauri, Aka bude kofar Abuturrab ya shigo da sallama kansa a kasa, Hade rai Aunty tayi ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta shimfida darduma ta hau sallahn isha, Aneesah dai sai wani cika take tana batsewa tana danna waya, ya ja stool ya xauna ya fiddo nasa wayar yana dannawa, yana ta xaune har Aunty ta idar da sallah, sannan ya kalleta yace “Ina yini Aunty” a takaice Aunty tace “Lafiya lau, sai yanxu ka ga damar
shigowa bayan ina ganin sanda ka shigo gidan tun kafin magrib?” Yana kallonta yace “Dakin Ummi nake ai” Aunty tace “Toh yayi kyau, ai da baka fito ba ka dauwama a can din” Shi dai bai ce mata komai ba, ta dau carbinta tana ja, bayan few seconds yace “Dama xuwa nayi in baku hakuri Aunty a kan abinda ya faru, ni bana nan lkcn da Aneesah suka samu matsala da Hajja, ban ma san me ya faru ba har yanxu, na kuma bata hakuri tun a daren jiyan amma taki saurarata tayi wucewarta” Aneesah ta katse sa a fusace tace “Wllh karya ne Aunty, da bakinsa ya umarce ni da in tafi” Kallonta Abuturrab ya dinga yi yace “Ni nake maki