JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 49

karya?” Tace “Toh tunda baka ji kunyar yin karyan ba nice xan ji kunyar karyata ka Aliyu” Aunty na kallon Abuturrab tace “Ni tambayar da xan fara yi maka a nan shine me wancan dabbar taje yi gidan ka tare da Hajja?” Da mamaki yace “Dabba kuma, ai Allah ma bai ce a siffanta mutum da dabba ba Aunty, dabba fa kika ce” Aunty tace “Ohh ni xaka ma wa’axi? To nace mata dabbar sai kayi yanda xaka yi yanxu, kanwar uwarka ce ita din ko ta ubanka?? Ko uban meye hadinka da ita xaka ce kar in kirata da dabba? Ka bani amsar tambayata uban me ya kaita gidanka Aliyu?” Cikin tsawa ta kare maganar, Ya sauke idonsa kasa yace “Nima ganinta kawai nayi tare da Hajja i don’t know how” Aunty ta mike tana tafe hannu tace “Toh tayi xuwan farko tayi na karshe, duk ranan da kauyancinta da gidadancinta ya sake kadata ta bi wani ma

ba Hajja ba xuwa gidanka dama nace tana shigowa Aneesah ta kirani, xan kuma dau makullin mota in fita inje gidan sai kuma nayi mata abinda har ta koma ga Allah baxata manta ba don ubanta, duk ranan da ta sake gigin xuwa gidan Aneesah wllh wllh sai na lahira ya fi ta jin dadi, sai na walakantata walakanci mafi muni, sai na mata toxarcin da har jikokinta sai ta ba labari wllh” Abuturrab kallon Aunty kawai yake ko kiftawa babu, can dai ya dauke kansa, Cikin bacin rai Aunty ta ci gaba tana cewa “Idan ba kwadayi da

jakanci ba uban me xai sa tayi sha’awar komawa gidan da aka saketa ta fito, me xai kai ta?? To wllh ta kiyayeni bani da kyau, idan ta ci gaba da shiga gonata sai na sa ta bi duniya ni ba imani ne dani ba al-qur’an, su Ramlah yan iyayi da suka ga xa su iya riketa su ci gaba da riketa din, amma duk ranan da gidadancinta ya fada mata karya ya kaita gidanka to kuwa ranan xata yi da ta sanin haifota da matsiyatan iyayenta suka yi” mikewa Abuturrab yyi ya nufi kofa Aunty tace “Gidan ubanwa xaka ina magana Aliyu?? Aliyu ba da kai nake ba??” bude kofar yayi ya fice ya bar masu a bude ko kullewa bai yi ba, Aunty ta bi sa da kallo baki bude har ya fita kofar parlor gaba daya. Abuturrab na fita bangaren Ummi ya koma, Ummi na kallonsa tace “Kaje ka bata hakurin?” Kasa ce mata komai yayi saboda yanda xuciyarsa ke tafarfasa,

Ummi ta lura da yanayinsa ta ci gaba da aikinta da take yi kawai, bayan kusan minti uku yace “Ummi ki kira Aneesah kice ta sameni a mota, idan kuwa bata fito ba xan yi wucewata” Ummi tace “Ka kira uwar dakin taka ka gaya mata mana, ba ita tafi kusa da Aneesar ba, sannan ina ce ma a bangarenta take” Abuturrab ya mike yace “Next weekend idan na dawo xan xo in dauketa in sha Allah, sai da safe” daga

haka ya nufi kofa Ummi tace “Aliyu” tsayawa yayi, sai kuma ya juyo tace “Tell me what happened” Yace “Ummi kawai ni bana son abinda Aunty take yi ina raga mata ne kawai saboda Abba but idan ta ci gaba da shiga gonata i can go to d extent i am not suppose to, she is getting me pissed off” Ummi ta rike ha6a tana kallonsa da mamaki a ranta kuwa cewa tayi yau kuma?? Can ta d’an yi murmushi tace “Toh me ya

hadaka da uwar dakin taka, dama ana jin kanku ashe” Abuturrab yace “She should just stay away from my personal life nd issues, that’s all, xan jira a mota ki kira ki gaya masu idan kuma bata fito ba wucewata xanyi, sai da safe” Daga haka ya fice daga dakin Ummi ta bi sa da kallo, daukar wayarta tayi ta shiga kiran Aunty, Aunty na dagawa tace “Hafsah ki turo min Aneesah” Aunty ta wani kyabe baki tace “Aneesah

kuma?” Ummi tayi shiru bata ce komai ba, Can Aunty tace “Toh dama sallah take bari ta idar” Ummi ta katse wayarta, sai bayan minti shidda Aneesah ta shigo parlon Ummi ta xauna saman kujera ta gaida Ummi, Ummi ta amsa tace “Ki je ki saka hijab dinki ki dau jakarki mijinki na jiranki a mota, sai kuma ayi ta hakuri, shi dama xaman aure d’an hakuri ne, kowa hakuri yake, ke kuma sai ki gyara duk abinda baya so,

shima xai gyara in sha Allah, Hajja kuma ba lallai xaki sake ganinta a gidan ba ma, kiyi hakuri ki bi mijinki ku tafi kin ji” Aneesah tayi kasa da kanta, bayan wani d’an lokaci tace “Toh” sannan ta mike ta nufi kofa, Ummi ta bi ta da kallo har ta fita, tana komawa ta sanar ma Aunty yanda suka yi da Ummi tana tabe baki, Aunty ta ja wani dogon tsaki tace “Toh baxa ki je ba wllh, ita a wa xata tsomo baki cikin lamarin nan? Ina

ruwanta! A cikin kayan miya wacece ita a lamarin Aliyu??” Aneesah dai sai ta6e baki take, can tace “Kinsan me Aunty tunda har kirana tayi ta min magana ki bari kawai inje kar ta saka ni a baki” Aunty tace “Ta saka ‘ya yanta a baki dai ba ke ba wlh, kamar tana wani tabuka abun kirki a kan lamarin Aliyun da xata wani tsomo baki a wannan case din, ta ma ji da mugun abinda ke cinta kullum a xuciya mana da shiru shirun da take na algungumanci” Aneesah ta mike tace “Ko kayana ma baxan dauka ba Aunty xan dai tafi da

turarrukan cikin hand bag” Aunty tace “Toh ya xancen xuwa asibitin gobe, ni fa dalilin da yasa nace baxa ki tafi yau din ba kenan” Aneesah tace “Sai in taho idan ya koma aiki gobe da safe, nasan da sassafe xai wuce kano ai, yawanci yanxu haka yake yi, ni bana son wancan matar tace nayi disrespecting dinta ne amma da sai in tsaya” Aunty ta ja tsaki ta xauna gefen gado tace “Dama goben ki xo da wuri, Kinga dai

dai kenan kafin ya dawo wani weekend din anyi duk abinda xa ayi an wuce wajen” Aneesah ta saka hijab dinta ta xuba duk turarrukan a jaka sannan tayi ma Aunty sai da safe ta fita. Har suka isa gida Abuturrab bai ce ma Aneesah komai ba ita ma haka, banda danna wayarta babu abinda take, ta sauka motar ta bi

bayansa xuwa cikin gidan, xaunawa parlor yyi yana kara regretting furnitures da aka xuba ma Aneesah a bangarensa, ko kallonsa bata yi ba ta haye sama ta wuce bangaren nasa, kwafa yyi ya mike ya haura sama ya bude dakin da su Hajja suka sauka ya shiga ciki, tsaf Hajja ta gyara dakin kafin su fita neman jiddah

daxu da safe, don cewa tayi babu inda xata tafi bata gyara dakin ba haka kawai ta shiga hakkin tsafta, har bandaki sai da ta wanke, banda kamshi kuma babu abinda dakin yake, cire kayansa yayi ya shiga bandaki dake cikin dakin, bayan yayi wanka ya jima xaune dakin kafin ya sauka downstairs ya shiga kitchen, har sannan kitchen din fess tun gyaran da Jiddah tayi masa, ya dinga bin kitchen din da kallo kafin ya dau mug ya tafasa ruwan xafi ya hada shayi ya fito, a parlor ya sha shayin, yana ta xaune har kusan sha daya

kafin ya mike ya wuce sama, babu yanda ya iya ya nufi bangarensa don daukar jallabiyarsa, Aneesah ce durkushe dakin hannunta rike da karamin towel tana goge turarrukan da suka fashe da sauri, har wani rawa hannunta yake, jakarta ta dauka xata ciro charger bata san a bude yake ba duk kayan ciki suka jirkice ciki har da turarrukan da aunty ta bata daxu wanda nan take biyu suka fashe wani kamshi ya gauraye dakin, tana ganinsa ta mike da sauri ta wuce bandaki da towel din, ya bi ta da kallo….

[/indeed-social-locker]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button