JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 50

matsanancin kuka ta girgixa kai tace “Amma ka bani mamaki, yanxu so kake kace min maxa nake bi ko me?? Dama ashe baka fi kowa sanin halina ba Captain? Bayan kai ka ga alamar akwai wani wanda nake

kulawa har muka yi aure?” Sai kuma ta kara rushewa da matsanancin kuka tace “Tunda nake ban ta6a zina da wani d’a namiji ba Allah shaida, idan ina yi kai ma da ka sani ai don irin wannan abun baxai boyu ba, bani da wanda nake kulawa da ya wuce kai, me na maka xaka saka min da haka a ranan da ka kusance ni…” Abuturrab bai ce mata komai ba ya juya ya fice daga dakin ta bi sa da kallo tana hadiye abu da kyar.

Bayan ya shirya ko sallama bai mata ba ya fice daga gidan cikin motarsa, yana driving ya kara dialing number Ahmad, bayan Ahmad ya daga yace “Ahmad i still have more questions” Ahmad yace “Alright go on” Abuturrab yace “Kace not everyone ke shedding blood due to reasons u listed…. haka ko?” Ahmad yace “Yes” Abuturrab yace “But how about if u just find ur self in without any stress, me hakan ke nufi, or ana samun irin wannan cases din gun warce bata ta6a sex ba?” Ahmad yace “Noo!! if u should go in

freely, to ko ma wacece ta ta6a sex wllh, continuously ma kuwa, and probably for long take abunta shi sa ma kayi noticing hakan lkci daya….” Abuturrab dai yayi shiru yana sauraronsa, Ahmad yace “And let me tell u something, in dai mace ta sa6a sex before marriage to memory din wanda ta sa6a da shi din will remain in her brain, da kyar ta iya rabuwa da shi duk da fa ga mijinta, yawancinsu basa iya tsayawa a

matrimonial home dinsu without following men outside, it’s just like a curse, ko da sun dau vow din repenting to ina gaya maka na yan shekaru ne… xa su koma idan ba Allah ne ya so su da Rahama ba” Shi dai Abuturrab bai ce komai ba, Ahmad yace “Are u okay now?” Abuturrab yace “Sure nagode, i am on my way to kano, thank you… Sai anjima” Ahmad yace “Alright safe trip” Katse wayar yayi ya ci gaba da

tukinsa. Tun da Aneesah taji fitar motarsa a gidan ta hau kiran Aunty, Aunty na dagawa ta fashe da kuka tace “Aunty na shiga uku…” Aunty dake kwance kan gadonta ta mike xaune da sauri tace “Me ya faru?” Cikin kuka tace “Wllh kawai daren jiya Aliyu ya far min, duk yanda nayi kokarin stopping dinsa hakan bai yiwu ba har sae da yayi” Aunty ta bude baki tace “Yayi?? To sai aka yi yaya ynxu?” Tana kuka tace “Tun

jiyan ya ki kulani bai ma kwana dakin ba, sae yau da safe ya xo daukan kaya yake ce min i betrayed his trust, kinga wllh ynxu ma haka ya tafi kano ko sallama bai min ba” Aunty ta saki salati tace “To garin yaya hakan ya faru, garin yaya kika yarda kinsan halin da kike ciki Aneesah?” Kuka kawai take tace “Wllh he forced him self in me Aunty, nayi kokarin preventing hakan amma ni ba karfinmu daya ba” Aunty tace

“Tabdi, to ni yanxu me xance??” Aneesah ta dinga goge idonta ko da wasa bata ce ma Aunty turaren da ta bata ne ya fashe ba, Aunty tace “Toh abinda xai faru duk inda xaki nemo kudi ki nemo a samu a rufe bakinsa kawai” Aneesah tace “Sai in dau zinarina in siyar, I can’t imagine Aliyu yace xai rabu dani sabida haka, wllh ina sonsa sosai Aunty” Aunty tace “Ya rabu da ke?? Ji wani mugun alkaba’i, ke fata kike ya rabu

dake ma kenan? Akan wannan d’an abun xai rabu dake kamar warce ta kashe mutum? Mata nawa ne aka aurar bbu budurcinsu kuma suna xaune qlau da mazajensu? Rabu da d’an iska xai ma sakko ne, ke dai kawai ki siyar da zinarin ki turo min kudin a tura benue” Aneesah tace “Toh Aunty, ynxu xan fita kasuwa in siyar sae in tura maki kudin” Aunty tace “To yi maxa, kar ki wani damu abunki, ubansa ma yayi hakuri da hakan balle shi gantalalle, shaff mancewa xai yi idan na sa ayi aikin…” Aneesah tace “Toh nagode Aunty,

bari inje, xan kiraki” Aunty tace “To yi maxa” daga haka ta katse wayar, ko wanka Aneesah bata yi ba tun daren jiyan balle aje ga sallah, ta saka doguwar rigar atamfa ta xumbula hijab dinta sannan ta saka zinarin a jaka ta fita daga gidan. A ranan Ahmad ya kai Jiddah makaranta kamar yanda ya ce da Umma, Tunda yyi duk registration din da komai ya tafi ya barta kawai ta fara karatu Monday din… Da yamma karfe hudu da kansa yaje daukota daga school din, amma sanin halin Ummarsa sae ya wuce da ita can gida kawai,

Umma tayi farin cikin fara makarantar Jiddah sosai, ita dai Jiddah na xaune kasa kan carpet tana murmushi, Umma tace “Toh tashi kiyi sallah ki ci abinci” mikewa tayi ta wuce dakinsu, Ahmad ya kalli Umma yace “Kince daga nan xata dinga tafiya ko Umma?” Umma tace “Eh xata dinga xuwa daga nan” Yyi murmushi yace “Ga dai sauki amma ke baki so Umma” Umma tace “Saukin me?” Yace “Kashe transport” Umma tace “Kai yanxu ka bada shawarar a bar kamarta da Ramlah a gida kai kana can gun aiki, to wa xai

dinga gaya masu gaskiya ko ya sa su kan hanya, shiririta kenan kawai” Yace “Kema dai kinsan Ramlah bata da shiririta Umma, sannan Jiddah ma na da hankali da nutsuwa sosai, kinga from monday to Friday idan taje schl sae ta xo nan Friday din da yamma ta maki weekend, ina ga xae fi wllh” Umma tace “Shkkn kuma babu me sa mata ido kan karatun?” Yace “A nan ma kinsan bbu me sa mata ido amma take yin karatunta

wholeheartedly” Umma ta ta6e baki tace “Toh ae shkkn, sae ta tafi can din, amma friday ta dawo nan tayi weekend” Yace “In sha Allah Umma” Sae kusan biyar da rabi suka bar gidan suka koma gidan Ahmad, a hanya yake bata hakuri kan gidan Iya da bai kai ta ba tunda ta koma schl, Jiddah tayi murmushi kawai tace “Toh Allah ya kai mu wani lkcn” Ranan friday Abuturrab na shigowa garin kaduna gidan Umma ya nufa

direct, yana parking a kofar gida ya shiga cikin gidan, Umma ce xaune parlor suna hira da Huraira, yayi sallama ya shiga parlorn, sanye yake da fararen shadda da suka amshesa sosai, sae da Huraira ta gaishesa sannan ta bar parlon, Ya xauna saman kujera yana kallon Umma yace “Ina yini” Umma na kallonsa tace “Lafiya lau, daga ina haka?” Yace “Daga gida” Tace “Madallah, ya kwana biyu?” Yace “Alhmdlh…” Sallama

aka yi bakin kofar Umma ta daga kai tare da amsa sallaman, ta shigo parlon sanye da hijab dinta gogagge har kasa da jakarta a hannu, ta gefen ido yake kallonta har ta karaso cikin parlon ta nufi Umma ta durkusa nan kasa kusa da ita a hankali tace “Umma ina yini” Umma tayi murmushi tace “Lafiya lau Jiddah ya

karatun?” Ta sunkuyar da kanta tace “Alhmdlh Umma” Abuturrab dai kallonta kawai yake, Umma tace “Ya su Ramlar” Jiddah na wasa da fingers dinta tace “Tana gaisheku…” Umma tace “Ahmad din ya shigo ne?” Jiddah ta girgixa mata kai tace “Aa” tunda ta lura da cewar Abuturrab ne xaune parlon duk da ba wai

kallonsa tayi ba taki yarda ta dago kanta gaba daya, Umma tace “Toh yayi kyau, kije ki xuba abinci ki ci” Tace “Umma na ci abinci” Umma tace “Ohk to kice ma Huraira ta kawo ma Aliyu ruwa” Mikewa Jiddah tayi still bata yarda ta kalli direction din da yake ba ta wuce kitchen din, satan kallonta yake har ta shiga kitchen din, sai kuma ya kalli Umma yaga wani kallo da take masa…

[/indeed-social-locker]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button