JIDDATUL KHAIR 54

san inda suka je ba” Ya daga kafada shi dai bai ce komai ba, Hajja tace “Yau naga abinda ya isheni, yanxu babu wanda xa mu tambaya me d’an wayo a nan ko an san inda suka koma, ai dole baxa su wuce cikin hayin ba dai tunda dai naga alamar talaucin nasu ba na wasa bane…” Abuturrab yace “An ba ma wani gadinsu ne da xa su fadi inda suke? kinga kawai mu tafi Hajja, ranan nan ya fara damuna…” cike da
masifa Hajja tace “In tafi ina banyi abinda ya kawo ni ba, ko wiwi kake sha ne?? kai da xaka tayani mu baxama neman inda iyayen nata suka koma tunda hayin ba wani girman a xo a gani yake da shi ba xaka wani ce mu tafi, wannan wace irin wiwi ka sha” Yace “Toh Allah ya baki sa’an ganinsu, kin xata hayi
iyakarsa girman dakin ki ne ko gidan Alhaji Usman” Hajja tace “Atoh ni dama wani xagin naka ne ban saba da shi ba, har ubana dake kabari ka sha xagi kuma in hakura inyi shiru tun kan ma in tafi Masar…. Amma dai ni ba mahaukaciya bace baxan kulaka ba, kuma in sha Allahu ina nan har sai na hadu da iyayen nata sannan in tafi…” Hannu ya sa a aljihu ya ciro dubu daya ya sakala mata a katon jakarta yace
“Duk ranan da Allah ya sa kika gansu sai ki dawo gida, ni dai na tafi, kin xata nan Masar din ki ne” Daga haka yayi shigewarsa mota ya wuce, Hajja ta gyara tsayuwa ta bi sa da kallo har yayi nisa. Da sallama Abuturrab ya shigo parlon Abbansa daren ranan, bai yarda ya kalli kowa a parlon ba ya nemi waje ya xauna a kasa sannan yayi gaisuwa, Abba yace “Why did u switch off ur phone?” Ya daga kai a karo na farko ya kalli Abba yace “Wayar ce ta samu matsala” Abba yace “But i told u xa ka raka mu Hayin
Rigasa?” Yace “Abba ni ai ban san gidansu ba…” Abba yace “Sai ina ka sani?” Shiru Abuturrab yyi, Abba yace “Wajen mai anguwa?” Abuturrab ya sunkuyar da kansa yace “Eh” Abba yace “Toh gobe lahadi ka taho da safe ka kai mu wajensa” a hankali yace “Toh Abba, Allah ya kai mu” Abba yace “Ameen” D’aga kai yyi ya bi mutanen dake xaune parlon da kallo, sai kuma ya mike yayi sallama ya fita. Bangaren Ummi ya tafi, Ramlah ce kwance kan kujera a parlon Jiddah na xaune daga gefenta hannunta rike da wayar
Ramlah tana game, duk suka daga kai suka kallesa, kallo daya ya ma Ramlah sannan ya xauna kan kujera, Jiddah dai bata sake kallonsa ba ta ci gaba da game dinta, Ramlah ta mike xaune da murmushi fuskarta tace “Sannu da xuwa Yaya” Yace “Yauwa” Tace “Ina yini?” Yace “Lafiya” Ta koma ta kwanta tace “Ya Aunty Aneesah?” Yace “Lafiya” Jiddah dai taki yarda ta dago, Yana kallon Ramlah yace “Idan akwai abinci
a kitchen ki debo min” Ta kara tashi xaune tace “Toh” sannan ta mike tsaye ta nufi kofa, tunda Jiddah taga haka gabanta ya fara faduwa, tana ganin Ramlah ta bude kofa ta fita ita ma ta mike da sauri, amma tuni ya riga ta mikewa shi ma, tsaye tayi ta marairaice xuciyarta na bugawa tana kallonsa ya karasa gun kofar ya kulle, tana ganin haka ta shige bedroom din Ummi, saboda rudewa ta ma kasa sa makullin ya
tura kofar ya shiga, durkushewa tayi kasa har hawaye ya kawo idonta tace “Don girman Allah kayi hakuri ka kyaleni, don Allah nace maka kar su Ummi su shigo….” Dukawa yayi yanda tayi ita ma ta rufe fuskarta da sauri jikinta na rawa tace “Wllh su Ummi xa su iya shigowa yanxu” Ta kusa minti daya a hakan ganin bata ji yace komai ba kuma bai ta6ata ba ta dago a hankali ta kallesa har sannan xuciyarta na bugawa,
kallonta taga yana yi ganin yanda kirjinsa yake bugawa ta fara ja baya a hankali tace “Wllh su Ummi xa su iya shigowa” Ya fixgota yace “Aure kike so??” Ta xaro ido jikinta na 6ari tace “Ni bance haka ba” kana ganinta kasan a rude take, yace “Toh me yasa baki ce masu baki so ba?” Ta marairaice masa tace “Don
Allah ka bar ni in fita kar su Ummi su shigo su ganmu mu kadai a nan?” Yace “Sai aka yi yaya idan sun ganmu?” Buda baki tayi tana kallonsa ta girgixa masa kai tace “Ai bai kamata ba…” Runtse ido tayi bayan ya kara fixgota har tana jiyo saukan breathing dinsa yace “A wajensu da wajenki ne bai kamata ba….” Rungumeta taji yayi, ita dai har sannan bata bude idonta ba, yanda kirjinsa ke bugawa haka ma nata, taji yayi kasa da murya yace “Tell them u are not interested, tell them….” Sai kuma yayi shiru, haka kawai
taji jikinta yayi sanyi ta buda ido a hankali… babu abinda ta gani a lkcn sai ranan farko da ta fito daga cikin gidansu a hayi ta gansa tsaye kofar gidansu ya xo bata hakuri, a hankali ta daga kai ta ga idonsa a rufe suke, hannunta taji ya kamo cikin nasa, ta kalli hannun nasu sannan ta kara daga kai ta kallesa taga har sannan idonsa a rufe suke, lamo tayi jikinsa tana kara jin bugun xuciyarsa, bata san dalilin da ya sa taji hawaye ya taho mata ba, Saukan hawayen nata da ya ji a jikinsa ya sa ya bude idonsa ya kalli fuskarta suka hada ido, ganin hawayen da take yi ya hade goshinsa da nata murya can kasa yace “A ganin ki ina
takura ki ko?” Ita dai bata ce komai ba har sannan hawaye na sauka idonta, a hankali yace “I want nothing but the best for u, ban shiga rayuwarki da wata manufa na daban da ya wuce taimakonki da inganta maki rayuwa ba, may be i was mistaken… a lot happened and are still happening…” Shiru yayi
sai kuma ya rufe idonsa holding her more closer to him, calmly yace “I don’t know.. i was mistaken at many thoughts then… Things turn out the way they weren’t suppose to” Xaro ido Jiddah tayi jin an bude kofar parlor ta turasa da karfi, a tare suka mike tsaye, yana kallonta kafin yace komai ta bude kofa ta fice
da sauri, Ramlah ce ta shigo parlon da abinci, Ramlah dai sae kallonta take ganinta a bedroom din Ummi, Jiddah ta nufi kofa ta fita don ta ki yarda su hada ido, Ramlah ta xauna kan kujera amma gaba daya kanta ya daure, sae kallon kofar dakin Ummi take, bayan few minutes dai ta mike ta nufi kofar ta bude a
hankali, tsaye ta gansa kusa da window staring into space, Ramlah ta yi yake bayan sun hada ido tace “Dama na kawo maka abincin ne Yaya ashe kana ciki” Yace “Ohk” juyawa tayi ta fita, ta koma saman kujera ta xauna a hankali with different thought in her mind. Ummi ce ta shigo dakin tare da Aunty Nafisah, Ummi na kallonta tace “Ikon Allah baku tafi ba, Ahmad din bai xo ba kenan” Ramlah tace “Bae
xo ba Ummi” Ummi tace “Abuturrab ya shigo nan ne halan” Ramlah ta nuna mata bedroom alamar yana ciki, Ummi tace “Naji kamshin turarensa ne” Aunty Nafisah tace “Nima magana xan yi kenan kika rigani wllh, idan xan koma tsaraban irin turaren kawai nake so a wajensa” Ummi tayi dariya tace “Lallai kam” a nan parlon duk suka xauna, bayan kusan minti goma Abuturrab ya fito daga dakin, Ummi dai bin sa
kawai tayi da kallo, ya xauna saman kujera ya kara gaida Aunty Nafisah, ta amsa tana murmushi tace “Ina Aneesah?” Yace “Tana Lafiya Alhmdlh” Kallon agogon wrist dinsa dake nuna karfe tara saura yayi, ya mike yace “Sai da safe” Ramlah tace “Abincin fa yaya?” Ya kalli abincin da ta ajiye masa yace “Ohk, dare yyi I can’t take heavy food now” Ummi tace “Toh tunda hanya ce ya ajiye ku a gida mana, ko lallai sae Ahmad din ya xo” Ramlah tace “Toh shkkn bari mu bi sa” Abuturrab yyi ma Umminsa da Aunty Nafisah
sae da safe ya nufi kofa ya fita, Aunty Nafisah tace “Na gansa wani iri, what does that mean?” Ummi ta ta6e baki tace “Ae a haka yake kullum” Aunty Nafisah tace “Haka kuma?” Ummi tace “Dama shi bai da