JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JIDDATUL KHAIR 55

weekend chef salmah ta xo ta min varieties in xuba a deep freezer, sai dai in ciro inyi warming, kuma wllh yana ci yanxu, gida kuma kafin ya dawo nake sa almajirai su shigo har sama da dakinsa su share tsaff, in basu batattun kwanuka ta can bayan gidan su wanke, iyaka in kunna burner in cika turaren wuta… ” Aunty tace “Toh kun kara hada shimfida kuwa?” Aneesah tayi wani dariya tace “Na fa ce maki

Aunty Safara’u ma ta yo min sako me yawa last week bayan wanda kika kawo min, lafiya lau komai ke tafiya yanxu” Aunty tace “Toh madallah haka nake son ji, ni kuwa kinsan har yau ko xuwa gaisheni a bangarena baya yi, to amma ni nasan tun bayan da ya rabu da tsinanniyar yarinyar nan da naji ana ce ma Jiddah hakan ya faru, duk gaba daya ya canxa min ke kyace ni makiyarsa ce” Aneesah tace “Ikon Allah, to

ita Jiddar haka xaki xuba mata ido Aunty??” Aunty tace “Ahaf ashe wasa da ni kike… Anjima dai ina nan shigowa in amshi kudin nan na ranan…” Aneesah tace “Aa Aunty ki bari ko jibi don nasan kafin ya tafi dole xai ban kudi me yawa” Aunty tace “Toh shkkn Allah ya kai mu, xan je anguwa ne dama da yamma,

so duk da haka xan biyo din dai” Aunty tace “To sai kin xo” Daga haka ta katse wayar…. Ramlah na kwance parlor da yamma taji sallaman Hajja, mikewa xaune tayi don kofar ma a bude yake tun bayan da Jiddah ta tafi Islamiyya, Hajja ta shigo tace “Sannu, a nan ana ta fama ko, ai uwarki ma lokacin da take da cikin Aliyu haka ta xabga uban laulayin nan dai kamar baxata yi ba, to ke gwara naki naga kina narkan

abinci abun ki, kawai sai dai yawan kwanciya kamar ruwa, cikin na kwari duk xaki daina jin haka wllh”
Ramlah dai sai murmushi take tace “Sannu da xuwa Hajja” Hajja ta karaso tace “Yauwa, sannu ina mijin naki?” Ramlah tace “Ya fita baya nan” Hajja tace “Toh gwara hakan, Jiddah fa? na samu labarin a nan take abunta yanxu” Ramlah tace “Ehh amma ta tafi Islamiyya” Hajja tace “O’o kullum dai ace taje

Islamiyya, irin wannan xuwan Islamiyyan nata haka ai ya ci ace ta sauke, kullum fa tana hanyar Islamiyya kamar dai a Masar, to Allah ya bata ilimi me amfani, duk da dai tana da gaskiyarta” Hajja ta ajiye ledan hannunta a hankali kan center table tace “Har gida aka kawo min wannan ledan in gaya maki, ni dai sai riritasa nake kamar kwai abunka da kayan amana, to ynxu karfe nawa suke tashi daga wannan Islamiyyar

dai?” Ramlah tace “Ta ma kusa shigowa, tun biyu ta tafi” Hajja tace “Atoh wannan kuma wani irin karatu ne kamar su suka fi kowa tsoron Allah” Ramlah dai ta tashi ta tafi kitchen, Ruwa ta kawo ma Hajja a kan tray da lemo da cup, ta dibar mata jollof din spaghetti da yaji hanta da beef wanda Jiddah tayi ta daura fork a kai da soyayyun kaji, duk ta daura kan tray sannan ta fito parlon ta ajiye kusa da Hajja tace “Ga

abinci Hajja” Hajja tace “Kina wannan tofe tofen yawun xaki kawo min abinci Ramlah? Aa ni dai Alhmdlh sai da nayi nak kafin in fito daga gida” Ramlah ta tafi tayi kwanciyarta bata ce mata komai ba, Hajja ta sa hannu ta xare goran ruwan tace “Gwara gwara wannan din dai, dama har gidan Aliyu nake son xuwa

saboda naji labarin safaran turarruka yake, sai ya bani ko guda uku ne, Nafisah ma naji wai ta rokesa turaren ai” Ita dai Ramlah kallo kawai take, Bude kofar aka yi Jiddah ta shigo da sallama, Hajja na ganinta tace “Toh Alhamdulillah, sannu da xuwa Jiddah” Jiddah na ganinta sai da gabanta ya fadi, ta karasa

parlon ta xauna saman carpet a hankali tace “Ina yini Hajja?” Hajja tace “Lafiya lau, ga sakonki nan tun daga bauchi aka kawo, babu wanda yasan meye a ciki banda ni da aka gaya ma, nima din dai ba budewa nayi ba tunda ni ba yar boko bace” Jiddah ta dinga kallon fancy leda din, Hajja tace “Toh dauka ki duba mana” Dauka Jiddah tayi ta fiddo abinda ke cikin ledan, kwalin latest Iphone ta gani cikin ledan, Ramlah ta xaro ido ta mike xaune tace “Hajja wa ya siya mata wannan?” Hajja ta kalleta tace “Aa kuma ai

wannan ba ruwanki Ramlah, ke dai kawai ki mata fatan alkhairi, da fatan kashewa lafiya” Ajiye wayar Jiddah tayi tace “Toh ai ni Umma basu ce xan rike waya ba yanxu” A fusace Hajja tace “Waye kuma Umma?? Yar bakin ciki ce fa matar nan fitowa fili ne bata yi ta nuna, ita ta isa tace baxa ayi abinda nace ba, banda Aliyun da ya tsinto mana ke a can hayi kina galantoyi, wanda ma da muka je gidan naku shekaranjiya gani muka yi an rushe d’an kuturun gidan da baldoza ba komai sai fili, ai ina ga babu wani

da ya isa ya hanaki amfani da wayar nan a yanxu dai, don ko Usman yayi yunkurin yin hakan xan nuna masa bacin raina ainun balle wata mata can da ta narka uban kiba, da Masar ne ita wannan dama da tuni an kwantar da ita a asibiti baxa ayi shawara da yan uwanta ba ma, toh wacece kuma Umma a

wajenki banda dai tana kanwar Uwar shi Aliyun da yayi sanadin kawo ki cikinmu, ni dai ba ruwana a dinga yin abu bisa tsari, ina ma laifin kice inje ince mata xaki fara amfani da waya” Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, Ramlah sai kallon Hajja take daga kwancen da take, Hajja ta sharce xufar da ta hada

don fitina tace “Balle ma jikana ne ya bada wayan nan a kawo maki, toh ina ruwanta kuma banda dai fitina take son ja ma kanta ita Ummar, yo fitina mana… daga masarautan bauchi fa wayar ta fito ba ma kasuwa ba, to tayi ta kanta don babu wanda xai duba cewa kanwar Hauwa ce ita, hukuntata xa ayi yanda ya kamata” Babu dai wanda ya tanka Hajja, Tana bude goran ruwan hannunta tace “Yanxu ki tashi ki cire

uniform mu je ki rakani gidan Aliyu, shi kuma ina ta jin jita jitan xai fita waje da wani babba a jirgi amma kun ga ni ai ya ki gaya min, ko da yake dai baxan biyesa ba, titin ma da ya yasar dani a hayi shekaranjiya ban gaya ma kowa ba, bakina alekum na dawo gida na shige daki na, tinda mu ‘yan Masar dai da hakuri aka san mu…” Jiddah da duk hankalinta ya tashi ta dinga kallon Hajja ta ma rasa abinda xata ce, yanxu

abu biyu ne ya dameta a rai, na farko Hajja tace wai an rushe gidansu, to me yasa xa a rushe gidansu su da ba a kan titi suke ba, ina babaarsu da Bibalo suka koma kenan yanxu?? Tunanin hakan yayi mugun

daga mata hankali, na biyu kuma rakiyar da Hajja tace xata mata gidan Abuturrab, Ramlah ta mike ta tafi bandaki Hajja ta bi ta da kallo tana yamutse baki, tana dawowa daga bandakin ta kalli Jiddah da sauri tace “Tashi muje kada magariba tayi mana kin ji” Ramlah tace “Amma Hajja ai Ya Ahmad bai san xata fita

ba, kuma babu kowa gidan sai ni kadai…” salati Hajja ta rafka tana kankance ido tace “Waye kuma Yaya Ahmad? Ina ruwana da shi? Me na hada da shi?? Kanin uban jiddan ne shi ko ko? Ku dai kun cika daukan magana wllh, shi yanxu ya isa hanata ta bi ni” Ramlah tace “Toh ai wajensa take dai yanxu” Hajja tace “Ja can ki ji da tsamin yawunki, ina ruwana da ke da Ahmad din, gashi nan ai ya hadaki da wahala kullum

yana hanyar Abuja…” Jiddah ta kalli Hajja tace “Hajja ni fa ina da karatu gobe muna da jarabawa” Hajja ta dinga kallonta, can tace “Ni xaki walakanta ina yabonki sallah xaki kasa alwala?? Gidan jikana fa nace

ki rakani ba gidan wani 6are ba, gidan nan kuma na samu labarin kin kusa wata uku a cikinsa, to meye don nace ki rakani xaki gatsa min wannan magana haka ba dadi” Jiddah dai ta sunkuyar da kanta a ranta tana tunanin no amount of words can allow her go to Aliyu’s house this evening, mikewa Hajja tayi ta

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button