JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

JIDDATUL KHAIR 56

bace mata ta bi bayansa da sauri, tare suka shiga ciki tana bin wajen da kallo, inda ya ta6a kawota ya mata siyayya Washegarin ranan ta na farko a gidansa ne, cart ya tafi ya dauka tana biye da shi, ya mika

mata handle din yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi ta amshi cart din, ya dau wani ya fara tafiya, bin bayansa tayi tana turawa a hankali, wajen turarruka ya nufa, yace “Pick” tace “Ni ina da turare da yawa” Bai kuma sauraronta ba ya dinga debar mata turaren, ta dinga bin sa da kallo tana mamaki, bayan ya gama ya tafi gun mayukan shafawa da sabulu da shower gel, su ma ya dibar mata, ita dai bin sa kawai

take da cart din hannunta, duk wasu kananun abu na bukatar yau da kullum sai da ya dibar mata, har ta fara gajiya da binsa, don sun siya kaya da yawa, wajen sanitary pads taga ya nufa, ganin uban pads din da ya debo bata san lkcn da tace “Ai basu kare ba na gida” Yana juyowa ta sunkuyar da kanta, yace “Meye basu kare ba” Kasa cewa komai tayi, ya xuba pads din a cart ya bar wajen, ta bi bayansa tana

tafiya a hankali, sai da yaga cart din ya cika sannan suka tafi wajen kayan ciye ciye, nan ma bai jira yace ta dau komai ba, ya dinga debar mata duk wani abu da shi yake ci yana xubawa a cart din da take turawa, har kayan shayi duk sai da ya daukar mata, Jiddah dai sai kallon wani chocolate dake side dinta take ta yi don Ahmad na kawo masu irinsa daga Abuja, chocolate din kuma ba dai dadi ba, ta d’an kallesa taga yayi

backing dinta yana duba wani tsadadden biscuit, kwasan chocolate din tayi kusan biyar ta juyo da sauri xata xuba su a cart din dai dai nan shi ma ya juyo rike da biscuits din da yake kallo suka kusa cin karo, juya masa baya tayi da sauri taji kamar ta nutse ta rufe ido, xata maida chocolates din taji ya fixgota, tayi

narai narai da ido tana kallonsa da manyan idonta, ya amsa ya xuba su a cart din yana kallonta shi ma, ita ta fara sauke idonta, sauran siyayyan duk tana gefe har ya gama, suka tafi wajen biyan kudi, a booth duk aka xuba ledojin kayan siyayyan, eatry din mall din ya shiga ya siyi ice cream da pizza with shawarma sannan ya fito, ita dai tana tsaye bakin motarsa tana jiransa, bayan ya shiga ita ma shiga motar, cikin minti ashirin da biyar suka iso kofar gidan Ramlah. Jinginar da kansa yayi da kujeran motar ita dai jira

kawai take taji ya bude lock din motar ta sauka, amma sai taga yaki budewa, bayan five minutes, taji muryarsa calmly yace “Xan mu fita Dubai gobe in sha Allah, from there xa mu tafi Uk…” Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya kalleta…. ta sunkuyar da kanta tace “Allah ya kiyaye” ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Xan yi few months a can” Bata ce komai ba, yace “Kina da bukatar wani abu ne??” Ta girgixa masa kai

tace “Wani abu kamar me bayan su Umma na yi min komai ni” Ya dinga kallonta yace “Wannan ne amsan tambayar da na maki?” Kin cewa komai tayi, yace “Bude baki kiyi min magana” Tace “Bana bukatar komai” shiru duk suka yi, ita dai wata magana ce ke cinta amma ta rasa ta ina xata fara masa, ji tayi yace “Do u have anything to say to me?” Ta kallesa da sauri, sai kuma tace “Ehh..” yace “Ina jin ki” cikin sanyin murya tace “Ranan Hajja tace wai kunje hayi an rusa gidanmu, ba kowa yanxu” Ya dinga

kallonta yace “Sai aka yi yaya?” Ta fashe da kuka tace “Baabarmu da Bibalo fa?” Yace “Kina son xuwa wajensu ne yanxu??” Hawaye na sauka ido ta ta kallesa tace “Ehh ina so don Allah” Yace “Me xaki yi masu idan kinje” Cikin rawan murya tace “Ina son in gansu mana, saboda nayi kewarsu… Ban taso na gan ni da kowa ba sai su, and it’s been long… Nayi kewarsu sosai” Tada motar yayi bai kuma ce mata komai ba yayi reverse suka bar layin. The journey was so silent, bayan tafiyar kusan minti talatin suka iso

titin hayin rigasa, tunda suka shigo hayi Jiddah ta dinga bin anguwar tasu da kallo, ta rasa wani irin farin ciki xata yi a moment din, farin cikin nata bai bayyana a fili ba sai da ta gansu kan layin gidan Babaarta, ta kallesa da farin ciki amma ta rasa abinda xata ce masa, she looks so happy… shiga layin yyi da motarsa

xuciyarta na bugawa tace “Don Allah ko xaka tsaya in fara shiga gidan Iyah in gaisheta???” Ya kalleta sannan yayi parking kofar gidan Iyah, sauka tayi daga motar da sauri ta shige gidan a guje, ya sauka ya jingina da motar tasa ya bi ta da kallo, Iyah na xaune tsakar gida da rediyonta a hannu, tana ma jikokinta dake kwance saman tabarma fifita sun yi bacci, Jiddah ta wara ido cike da murna tace “Iyah!!!” Fadawa

jikinta tayi ta rungumeta, Iyah ta matsar da ita tana mata wani kallo daga sama har kasa, sai kuma tace “Jiddah????” Rungumeta Jiddahh ta kara yi lokaci daya hawaye ya kawo idonta tace “Nice Iyah, nayi kewarku wllh” Iyah ma ta fashe da kuka tace “Ashe rai kan ga rai Jiddah, ashe xan sake ganin ki a rayuwar nan?” Jiddah ta share idonta tana murmushi tace “Gashi kin gan ni Iyah” Iyah ta mike tsaye tana

sake kare mata kallo don tabbatar da ita din ce kuwa, sai ta saki salati tace “Daga ina kike haka Jiddah?? Kece kika dawo haka kamar balarabiya Jiddah??” Jiddah tayi murmushi ta kasa ce mata komai tana kallonta, Iyah tace “Ke da waye yanxu haka? Daga ina kike?” Jiddah tace “Yana kofar gida, ince ya

shigo?” Bata jira me Iyah xata ce ba ta tafi da sauri kofar gidan, har sannan Abuturrab na tsaye ya rungume hannunsa, tace “Wai tace ka shigo” kallonta ya dinga yi ta juya ta koma ciki da sauri, shafa kansa yyi ya bi bayanta… Har kasa Iyah ta durkusa tana gaishesa bayan ya shigo gidan, hakan yasa ya

xauna saman darduma yana d’an murmushi calmly yace “Ina yini??” Iyah ta rushe da kuka tace “Wllh da kasan irin taimakon da Allah ya baka ikon yi da ladan da Allah xai baka da ba haka ba bawan Allah, ka

taimaki rayuwar Jiddah a sanda take tsananin bukatar taimakon, ka cece Jiddah a dai dai lkcn da take bukatar ceto, Allah ubangiji ya sa ka samu me maka abinda kayi ma marainiyar Allahn nan duniya da lahira, Allah ya biyaka da aljanna, ya yalwata maka arxikin ka, Allah ya baka ikon ci gaba da riketa da amana, Allah kuma ya baku xaman lafiya tare na har abada ya bada xuri’a dayyaba” Kuka kawai Iyah take kamar jininta ce Jiddah, Jiddah dai duk jikinta yyi sanyi ta sunkuyar da kanta jin maganganun Iyah, shi ma

kawai murmushin karfin hali yake yana kallon tsohuwar a hankali ya ce “Ameen nagode Mama” Iyah na kwalla tace “Wllh ki rikesa Jiddah, kaf duniya a yanxu dai baki da kamarsa, shine uwarki shine ubanki, ya maki abinda a cikin kashi dari na mutane baxa ki samu kashi biyu da xa su iya maki ba, ya fidda rayuwarki

cikin kunci, maraici, tsanani, da bakar wahala, yayi maki duk wannan abun a lokacin da kike tsananin bukatarsu, to me xai janyo maki butulce masa a rayuwar nan, kiyi masa halacci yanda ya maki Jiddah, ga shi wai yau kece sai da na maki kallo kusan uku sannan na gane ki, ba don muryarki ba wlh baxan yarda ke din ce ba” Sosai jikin Jiddah yayi sanyi wanda bata san lkcn da hawaye ya dinga sauka idonta ba tana

kallon Iyah, kallonta kawai Abuturrab yake babu ko kiftawa, Iyah tace “Ki rikesa, kiyi masa biyayya, ki rike yan uwansa da duk wani nasa Jiddah, da abinda xaki iya biyansa kadai kenan ki ji in gaya maki, nace kiyi
masa biyayya, wllh kiyi masa biyayya, Allah kadai yasan sadaukarwan da yayi sabida ke, Allah kuma ya baku xaman lafiya na har abada, nasan baku ma kai ga shiga gidan Hansai ba, amma idan xa ku ji ta nawa

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button