JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

JIDDATUL KHAIR 56

ba sai kun shiga ba kuyi tafiyarku kawai, Hansai bata canxa ba dai daga yanda kika santa… Sai ma dai abinda ya faru” Jiddah sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, Abuturrab ya ciro kudi aljihunsa ya ajiye ma Iyah yace “Kiyi hakuri Mama babu yawa wannan, in sha Allah xan sake dawowa gaisheki,
sannan xan daukeki in kai ki inda mu ke” Iyah tace “Wllh gaisuwan da kuka xo min ma ya isa ya wadatar ba sai ka bani kudi ba Yarona” mikewa yayi yana kallon jiddah da ta kasa daina kuka, a haka dai Iyah ta rakasu kofar gida tana cewa “Ba sai kun je gun Hansai ba, kuyi tafiyarku Allah yayi maku albarka ya baku

xuri’a dayyaba…” Cikin sanyi Jiddah tace “Iyah baxan iya tafiya ban shiga na gaisheta ba” Iyah tace “Toh shkkn Jiddah, Allah ubangiji ya kareki daga duk sharrinta ku shiga kawai, akwai Allah” Abuturrab ma bai hana Jiddah ba suka karasa kofar gidan nasu da kafa, gabanta na faduwa ta shiga gidan ta ma kasa ko

sallama saboda fargaba, Hansai na xaune tsakar gida tana fiffita ga kwanon abinci a gabanta tana cewa “Yo ba gwara ma ya mutun ba ko xa a rage mugun iri, duk fa da hadin bakinsa da uban kudi da aka dinga

lafta masa aka siyar min da ‘ya ban ji ba ban gani ba, yau wata dai dai kusan biyar kenan, kuma wllh gaya maki ne kawai banyi ba amma so nake na hada yan kudaden wankauna, na kai gidan malam Hamisu a sake danne tsinanne kada Allah ya mikar da shi, kaf bani da makiyi irinsa a duniya yanxu kam…” Zulai

dake kwance tsakar gidan da daurin kirji tace “Ai ko dai ance yana can shika rai a hannun Allah baya gane duk wa enda ke kansa, aiki ma xa a masa sai kuma jikin ya dada sususcewa kinga bbu xancen aikin ai sai ya farfado kuma” Jiddah ta kasa shiga gidan gabanta sai faduwa yake ta dinga karanto addu’o’i a ranta, Zulai ce ta hango shadow tace “Waye tsaye nan, ko Bibalo ce” Hansai tace “Bibalo ai sai karfe sha biyu kila, wani shegen ne ya tsaya min bakin kofa yana min la6e?” Jiddah ta runtse ido ta karasa shiga

tsakar gidan, duk suka tsaya kallonta don akwai hasken wata sosai tsakar gidan, Hansai ta ajiye maficin hannunta tana kallonta daga sama har kasa tace “Waye wannan?” Da kyar Jiddah tace “Ni ce Baabarmu” Zulai ta mike a gigice tana sake gyara daurin zanin kirjinta tace “Ke wa??” Hansai dai hangame baki tayi tana kallon Jiddah daga sama har kasa, can ita ma ta mike ta nufeta tana sake kare mata kallo kamar

taga aljanna, Hawaye ya shiga sauka idon Jiddah ta durkusa kasa cikin sanyin murya tace “Baabarmu” Hansai ta fashe da wani matsanancin kuka tace “Toh Alhamdulillahi, yanxu saura in kai ma Badalan kan dutse cikon kudinsa, aiki kam ya ci Alhmdlh… Allah ya maido min ita gida da kafafuwanta” wani shewa Zulai ta saki da karfi tana gode ma Allah ita ma, Jiddah dai sai kallonsu take, Hansai na sharban majina

tace “Tashi mu shiga ciki, tashi” Jiddah tayi karfin halin cewa “Ba ni kadai ba ce Baabarmu” Hansai ta kalli soro da sauri tace “Ke da uban waye??” Jiddah ta sunkuyar da kanta tace “Ni da shi ne” Dai dai nan Abuturrab ya shigo cikin compound din don gaba daya hankalinsa ya ki nutsuwa shigan Jiddah gidan ita kadai, Hansai taji mugun faduwan gaba ganinsa tace “Ya xaka afko ma mutane gida haka kanka tsaye, kai waye??” Yana kallon Jiddah yace “Idan kun gama gaisawan taso mu tafi… It’s getting late” Hansai ta

gwalo ido tace “Ku tafi ina?? To wllh wllh karyarka ya sha karya Malam, babu inda ‘ya ta xata daga tsakar gidan nan, ko taku daya baxata yi daga nan ba wllh, ku je ina?? Lallai sannunka….” tana huci ta kare maganar ta dago Jiddah da xumar shigar da ita daki tana cewa “Tashi don ubanki, idan kin sake fita ko nan da kofar gida Allah ya tsine min albarkan da yayi min….” Daga kasa har sama Abuturrab ke kallon Hansai da wani expression, can yace “Kin manta ita din matar aure ce?” Hansai ta mulmulo wani uban

xagi tace “Fadi duk uban da ka kashe ni me iya siyar da gidan nan ne in biyaka, a gidan ubanwa ta xama matar aure?? Ka dau min ya ka tafi ka lalatata kace min matar aure ce??” Abuturrab na kallon Jiddah yace “Zo mu tafi” Jiddah hawaye na sauka idonta ta kallesa sannan ta kalli Hansai dake kokarin janta

xuwa cikin daki, cikin kuka tace “Baabarmu….” Hansai bata saurari me xata ce ba ta wanka mata wani mummunan mari da yasa taji diff, ta kuma kai mata wani tana huci tace “Rufe min baki don ubanki” bai san lkcn da ya karasa compound din ya fincike Jiddah a hannunta ba yace “Kinyi na farko kinyi na karshe, kin kuma ci albarkacin ki na matar babanta da wllh sai na rama mata” Daga haka ya nufi soro da Jiddah,

Hansai ta lafta wani uban ihu ta bi bayansu tana kunduma xagi tace “Idan Jiddah ta sake barin gidan nan shegiya aka haifeni, wllh babu inda xata je kuma ka cika min ‘ya ta” Ganin ta yo kansu Abuturrab ya kwasheta da kafa sai gata wanwas a kasa, ya bude front seat ya saka Jiddah dake ta kuka a ciki sannan ya kulle ya xaga ya shiga driver seat, Xulai ce ta fito da katon tabarya tana ihu wai jama’a su kawo masu

dauki, Hansai ta mike a rikice ta amshe tabaryan, da duk karfinta ta buga glass din bangaren da Jiddah take, ihu Jiddan ta fasa a tsorace ya fixgota jikinsa tayi lamo, don sai da glass din yyi tsawa, Hansai ta shige gaban motar kamar mahaukaciya tana cewa “Da dai ka tafi da Jiddah gwara ka kasheni, ka kasheni nace d’an banxa… xan ga ta inda xaka bi ai, sai dai ka takeni, babu inda xaka kai min ya ta d’an yankan

kai…” Abuturrab yyi reverse sosai sannan ya taho a guje, wani uban tsalle Hansai tayi ta kauce sai gata da Zulai kwance a kasa, ya ja motarsa a guje ya bar layin, kuka kawai Jiddah take kamar ranta xai fita, har suka fita titin hayi bai ce mata komai ba….

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button