JIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

All thanks to Allah SWT for the chance, privilege and ability to start this book, my special greetings goes to my lovely Mum Hajiya Hajarah and my sweet aunties (Small mums) my siblings/Cousins aren’t excluded also… I love them all, Hajiya Adama (Mrs Garban kauye) gaisuwa da fatan anyi sallah lafiya, Chamo da tawagarta su ma duk na gaishesu kyauta???? and My Sophiee I know you won’t see this but get this.. jiddo Love’s you dear, Lovely fans and Friends ina maku fatan alkhairi da fatan gamawa da iyaye lafiya

kafin dai in fara post din book din nan i want to let everyone know this…. Although most of my fans sun san i am a final year student, to cut it short… 2 month to our final exams aka tafi strike, so if God should touch Fg’s mind by letting dem do d needful i have no choice then to take a break and face my final exams… Balle ma nasan xamu gama in sha Allah before then, coz i have written and keep enough…. thanks for understanding????

???? Jeedderhh????

By Khaleesat Haiydar????✍????

1…..

Slowly yake driving din idonsa a kan titi yana sauraron abokinsa, amininsa, kuma d’an uwansa dake xaune kujera me xaman banxa cikin motar, can dai ya ja tsaki ya girgixa kai, speaking calmly yace “Ni fa da ma ka canxa labarin nan naka Ahmad, in anyway ban ga amfaninsa ba…” Dariya abokin nasa Ahmad yyi yace “Toh ai ni yana da amfani gareni sosai tunda ina sonta and i want to marry her, look Captain don Allah ka cire son xuciya ka gaya min meye aibun Maryam let me know” Wanda ya kira da captain ya shafa lallausan gashin kansa yace “Kasan mene?” Kallonsa kawai Ahmad yake yana jiran jin abinda xai ce, Captain yace “Ina son ka sanar dani me yasa ku Hausawa baku da xancen da ya wuce na soyayya, ga dai abubuwan ilimi iri iri masu ma’ana da mutum xai karu da su duniya… Amma ku dai soyayya kadai ku ka sa a gaba, did u know that it’s just of recent ina wani karatu nayi discovering cewar Airplane water is riddled with bacteria, not even that, jiya jiyan nan na gano cewar….” Ahmad dake masa wani kallo ya dakatar da shi ta hanyar cewa “Wannan kai da masu tunani irin naka ya shafa, what u are saying now will add no value to people like me gaskiya” Captain ya maida hankalinsa gaba daya kan tukin da yake, Ahmad yace “Duk sanda na kawo maka maganar Maryam you always have a way to get rid of the discussion ko me yasa?” Captain yace “Ohk you asked me of her flaws if i am not mistaken, right?” Ahmad yace “Yes so” Captain yace “To xaka ji ynxu…. first of all she is local, secondly she gat no qualities da xai sa ka makale mata dude, just imagine an undergraduate fa?? And worst of all she isn’t even beautiful enough, ga dai big babes a garin da ka baro Abuja, sannan….. her hygiene is nothing to write home about, i mean nothing…. Shine ma babban damuwata ma ni” Da mamaki Ahmad ke kallonsa, da farko kasa ce masa komai yyi, can kuma yace “Wani rashin tsaftar kaga tayi??” Captain ya saci kallonsa yace “Oho, wataran xaka gani” Ahmad ya girgixa kai yace “You are talking off hook, Maryam tana da qualities din da ni nake so, I think that’s all? Kuma dama kai idan baka son abu to fa baxa ka ta6a son abun ba, ka dingi discouraging mutum a kai kenan” Captain ya gyada masa kai yace “Ehh haka ne, plss close the chapter” Ahmad xai yi magana ya hango inda ake tuyar awara a gefen titi, da sauri yace “Captain plss ka d’an tsaya, I want to get this, na mance yaushe rabon inci awara, tun kafin in tafi Uk fa…” Captain ya d’an kalli wajen da ake tuyar awaran ya kara ma motarsa gudu yace “Allah ya kiyaye, domin na je dauko ka a railway station doesn’t mean xa ka mayar da mu gantalallu a hayi…. Meye kuma awara?” Ahmad yace “Toh ka ajiye ni, ai bance sai ka xo ka daukeni a tasha ba dama, you offered to do so” Captain yyi kasa da murya yana rage gudunsa yace “Yanxu Ahmad kasan ta ynda suka yi processing abun nan da xaka ci? Hayi ne fa nan, ka bari kaje gida kasa ayi maka mana, ni Allah bana son locality din nan naka” Calmly Ahmad yace “Su ‘yan hayin ba mutane bane Abuturrab?” Captain yace “Aa ba haka nake nufi ba, I mean… hygiene din, they don’t value it, ka gane ai” Ahmad yace “Kai komai sai kace hygiene, to sannu sarkin ‘yan tsafta, a haka kuma nake son in siya, ba ruwanka kuma” Captain bai kuma ce masa komai ba ganin wani waje da ake suyan yyi parking kafin ya karasa wajen yace “To sai ka sauka kaje ka siya, amma gaskiya you ain’t worth being a Dr wllh, very careless Dr that looks down on Hygiene” Ahmad na hararansa yace “Ae ba dankali nace maka xan ci ba malam, Awara nace kuma nan dankali ake siyarwa” Captain ya kalli wajen masu tuyan yace “Toh ai ban san yanda Awaran yake ba, ba shi bane wnn din?” Ahmad yace “Ba shi bane” Captain ya ja motarsa yana tukin a nutse, can underneath his breath ya ja tsaki, Ahmad is just too local for his liking, Ahmad yace “I think ga wani wajen can” ta gefen wajen da ya nuna masa Captain ya gangara yyi parking yana kallon yarinyar dake tuyan awaran yana yamutsa fuska shi wnn ko yunwa xai kashesa xai iya cin abinda take yi kuwa, Ahmad ya bude motar ya sauka ya tafi gun ta, ita kadai ce xaune sai yara da almajirai dake tsaye suna jiran a siyar masu awara, Ahmad yace “Me awara nawa nawa ne awaran naki?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Daya Ashirin” Ahmad ya buda ido ya rike waist dinsa yace “Ikon Allah, kamar dai muna fada da me awara irin wnn amsawan” Still bata kallesa ba ta ci gaba da sallaman yaran da ke gabanta, ta mota Captain ke kallonsu, shi dai Ahmad na tsaye bai sake ce mata komai ba ganin mood dinta, sai da ta sallami yaran gabanta ta daga kai ta kallesa tace “Na nawa xa’a sa maka?” Ya daga kafada yace “Na dari biyar kawai” Tace “Baxai kai ba, sai dai in xaka jira a soya wani” Yace “Toh ba damuwa xan jira a mota” Daga haka ya juya ya nufi motar ya bude ya shiga yana kallon Captain da ya kauda kai da sauri yana kallon daya side din. Leda biyu tayi masa sannan ta hadasu gaba daya a wani ledan daban, yajin ma ta xuba masa a wani ledan snn ta mike ta nufi motar ta mika masa ta glass dake bude, amsa yyi yana kallonta da murmushi fuskarsa yace “Kamar dai an 6ata ma me awara rai” Ita dai bata ce masa komai ba, dubu biyu ya ciro a aljihunsa ya mika mata yace “Toh gashi” ta daga kai tana kallon kudin tace “Na dari biyar kace” Yace “Ehh sai ki rike sauran canjin ai ko” Ta sauke idonta kasa tace “Aa ka dai bani dari biyar din dai kawai” Ya bude ido yace “Dama ana maida hannun kyauta baya” ta girgixa masa kai tace “Ban san wa xance ya bani ba a gida” Cikin sanyin murya ta karasa maganan, yayi murmushi yace “Sai ki boye kayan ki” Daga haka ya saki kudin nan kasa yace “To sai anjima me awara, Allah ya kawo kasuwa” captain da ya ki kallonsu ya tada motar suka bar wajen. Sai da suka kusa fita titin hayi Ahmad yace “I imagine may be condition ne ya sa yarinyar tuyan awara a rana ko, the country is getting tougher and tougher for the less privileged everyday…..” Captain dai bai ce masa komai ba, Ahmad yyi kasa da murya yace “On a serious note ina jin tausayin poor masses a kasar nan, yanxu banda situation me xai sa iyayenta su barta bakin titi tana wnn sana’a? Allah dai ya rufa ma kowa asiri” Still Captain bai ce masa komai ba har suka shigo Unguwan Sarki, yana kallon Ahmad yace “Mu je can gida ne kawai?” Ahmad ya gyara xama yace “Aa kai ni in ga Ummata tukun, da yamma xan shigo in sha Allah” Captain bai ce komai ba yyi driving har xuwa gidan kanwar Mum dinsa Hajiya Ramlah warce ita ce mahaifiyar Ahmad… A kofar gida yyi parking Ahmad na kallonsa yace “Baxa ka shigo ba?” Captain yace “Aa ni fa ko jiya na xo gidan nan” Ahmad yace “Sai dai idan Ummi ce ta aiko ka ba dai xuwan kanka ba” Captain ya shafa kansa yana xare manyan idanuwansa ya kasa cewa komai, Ahmad ya ta6e baki ya bude motar ya sauka, da sauri Captain na nuna masa ledan awaransa yace “Heyy ga kullinka ka mance min a mota” Juyowa Ahmad yyi ya jefa masa wani kallo ya dau ledan awaran ya nufi cikin gidansu, Captain ya bi sa da kallo yana murmushi, can ya kashe motar ya sauka ya bi bayansa walking slowly… Siyama ta sake yayanta da ta rungume ganin Captain da ya shigo parlon, tana murmushi tace “Yaya sannu da xuwa” Yace “How are you Siyama” tace “I’m fine” Yace “Ina su Maimuna?” Tace “Sun tafi islamiyya” Yace “Ke fa” Tace “Ka manta nace maka bani da lafiya jiya?” Yace “Ohhh ohk na tuna, Allah ya kara lafiya, Umma fa” Tace “She’s in her room” Tuni Ahmad ya nufi dakin Mahaifiyarsa, Captain ya bi bayansa. Sai bayan Magrib Captain ya bar gidan tare da Ahmad xuwa nasu gidan a Malali, Babban gida ne duplex me wadatattcen tsakar gida…. Captain yyi parking a daya daga parking lot biyu dake katon compound din, suka sauka motar tare da Ahmad suka shiga ciki Ahmad na cewa “Amma Abba baya gari ko?” Captain yace “Ehh baya nan”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button