JIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it’s 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788… Thank you

Mîkyããj_Sããdy Beauty Soap

Hy my beautiful people ina gaisuwa????????‍♀️ku karka’de kunnuwanku da kyau ku ji????????ina mai sanar muku da cewa akwai gara6asa me kyau ta musamman ga wanda suka saba sayen sabulunmu da ma wanda zasu fara saya????, akwai ragin kaso 20% bisa dari 100% ga wanda suka saba saye, sannan akwai ragin 10% bisa ga masu sha’awar fara saye??, akwai farashi mai sauki ga ‘yan sari, me yapi wannan dadi kam????ki sayi guda 4 kanana a baki kyautar daya, ki sayi guda uku manya a baki kyautar karami daya, ki sayi bucket biyu a baki kyautar babban rubber daya???? kema da kike da burin saya ku’dinki bai kai ba????to ga naki, ki kawo customers uku ki karbi naki kyautar Sabulun????????

Kawata ‘yar ‘kwalisa me kike jira,ita mace fa kullum cikim yin ado da ‘kãwa take???? ya kamata ki yunkuro wajen ganin kin rabu da wannan kurajen da tabo tabon fuskan nan haka??, kinga kema sai a saka ki a layin masu ‘kwalisa da bajakolin ado????????????uwar gida a daure ayi gyaran jiki, sbd karbar goron a wajen me gida????,, ina amaren bayan sallah ku pito ku sayi naku Sabulun kuje kuyi ta wanaka hmmm ????kamshi kawai zaku yi tayi kaca kaca????????, laushin fata Baja baja????????????a yunkuro azo a karbi kayan gyaran jiki tare da sabulun gyaran fata a wurin Mîkyããj_Sããdy????

Duk wanda suka gwada Sabulun mu sun san babu ‘karanta a ciki????in dai fannin gyaran jiki ne to sabulunmu shine amsarku,, shi ke mai da fata ta zama babu Pimples, Acne, Spot, Stretch Mark, da Duk wata matsala da ta shafi fata,, akwai lightening, nd glowing????

In kina son jikinki yai su6ul da shi, fata tai santsi da sul6i, ki yi haske me aji, ‘kamshi kaca kaca ko ta Ina, ki ta fresh abunki hankali kwance ki zama Wankan madara yauqin zuma????????????Anty madam????To ki mallaki 3d (Extra Whitening Soap, Ko da kudinki sai da rabonki hajiyata)????????????????????????????????

Akwai hadin:
Mai da tsohuwa yarinya
Uwargida ta koma amarya
Amarya ta koma tamkar ‘yanmata
‘Yan mata su koma ‘yan dagwai²

Ga masu bu’kata sai su tuntu6emu ta kafar sadarwa kamar haka;
Call/WhatsApp:08061570778
IG@mik_yaaj_saady

Mikewa Jiddah tayi tsaye tana kallonta, Aunty da har ta nufi kofa ta juyo ganin Jiddah bata biyota ba ta hade rai tace “Ba magana nake maki ba” Jiddah tace “Ban saka hijabi ba” Aunty tace “Nan nan ne ba nisa muje baxa ki rasa mayafi a tsakar gida ba” Jiddah bata ce komai ba ta nufeta, Umma ce ta shigo parlon da sallama, Aunty ta koma gefe tana yake tace “Sannu da xuwa Hajiya Ramlah” suka gaisa Umma tace “fita xa ki yi halan” Aunty tace “Ehh wllh sako xan amso nan bakin titi, da har nace mu je da Jiddan tace min Hijabinta na sama” Umma ta kalli Jiddah tace “Toh ki tafi saman ki dauko hijabin naki” Aunty tace “Aa bari kawai inje ae nan bakin titi ne” bata jira cewar Umma ba ta fice daga parlon tana jin wani mugun takaici, Umma ta kalli Jiddah tace “Kin ci abinci kuwa?” Jiddah ta girgixa masa kai, Umma tace “Toh saboda me, ke ba sai ki je ki diba ba, Ummi na sama ne?” Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace “Mu je” Jiddah ta bi bayanta suka wuce sama, Bangaren Ummi suka shiga, bayan Umma ta gaisa da yayarta tace “Yaya wai bata ci abinci ba” Ummi ta kalli Jiddah tace “Ae nayi tunanin tana tare da su Ramlah ne, kuma an kai masu abinci tun daxu, taje can dakinsu ta diba” Umma ta kalli Jiddah tace “Ki je ki deba abincin a can” Juyawa Jiddah tayi ta fita, Umma na kallon yayarta tace “Naga kamar baki saki jiki da ita har yanxu ba yaya” Ummi tace “Aa ko daya, baki ganin ita ma ba maganar take ba” Umma tayi murmushi tace “Ae kam ni muna hira da ita” Ummi tace “Did u know what is baffling me Ramlah?” Umma ta girgixa kai tana kallonta, Ummi tace “Yanda Aliyu ya mayar da mu shashashai ya maida mu wasu ‘yan yara, kinsan da gangan yaje yyi ma kansa aure da yarinyar nan?” Ummi tace “Me yasa kika ce haka yaya” Ummi tayi wani murmushi tace “Ai ni na haifesa ba shi ya haifeni ba, bai kuma isa yyi deceiving dina ba, he intentionally did what he did, abubuwan da nagani game da shi da yarinyar bai yi kama da abun da mutum yyi ba da son ransa ba, kinsan satinsa nawa rabonsa da gidan nan yanxu?” Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Nima ae ya daina xuwa min yaya…” Ummi tace “Toh yayi kyau… Xai gane bashi da wayo” Umma tace “Amma duk da haka akwai ayar tambaya fa a kan xaman da suke, don duk inda kika ji kishin kishin din magana da akwai kamshin gaskiya, ina jiran Ahmad ne yanxu inji matsayin auren nasu” Ummi tace “Ni ma dai nayi shiru ne kawai, amma ban aminta da xaman nan ba” Umma tace “Toh kin ga, don dama da bakinsa yyi ta cewa xae rabu da ita, na dinga hanasa tare da Abbansa to wa ya sani ko watsar da xancenmu yyi” Ummi tace “Ni kuma haka kawai naji ina son rabuwan nasu Ramlah” Umma dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta sauke ajiyar xuciya tace “Allah dai yyi mana me kyau, kuma bana tunanin ya sa ta a karatu har yanxu, and she doesn’t look happy always….” Ummi tace “Sannan ina ma son xanyi magana dake tun kwanaki, kinga lamarin rayuwar Aliyu? dama ina son in cire idanuwana da komai na a kai, sai yaje ya kara rike warce yake ganin ta fini daraja da hannu bibbiyu, ita yake ga xai iya komai na sirrinsa, ita yake ga xai fi ji da yarda da maganarta, to suje su karata, ni gaisuwan da yake min duk sanda yaga dama ma ce masa xanyi na yafe masa ya daina” Umma tace “Wannan ba magana bane yaya, tun farko ke kika xuba ido aka janye maki shi, Ahmad ya sha kawo min wannan same complain din, idan baki manta ba akwai wani lkci da na maki magana a kan hakan kika ce min ai ba komai duk daya ne, wnn mata ni ban ta6a ganin makira irinta ba…” Ummi ta girgixa kai tace “Aa ba ruwanta, ai shi ba yaro bane ya kuma mallaki hankalin kansa, he knows what is right from wrong, kawai dai hakan yake ga yafi masa alkhairi, sai yaje ya karata, amma ina dab da yi masa wankin babban bargo a gidan nan” Umma ta sauke ajiyar xuciya tace “Ki dai yi hakuri yaya, Allah xai ganar da shi, wankin babban bargo kuma sai dai ki hada har Kishiyarki don munafuka ce” Bayan kusan minti talatin Umma ta gama abinda ya kawota, sallama tayi da yayarta har ta nufi kofa tace “Toh in tafi da Jiddar ne don can ya kai ta” Ummi tace “Aa wannan kuma ban sani ba” Umma tace “Naji xa su fita saloon gobe, kawai su tafi tare ita ma tayi gyaran gashin idan ya so ko driver sae ya maido min ita goben” daga haka tayi ma yayarta sallama ta fita dakin. Kwana dayan da Jiddah tayi gidansu Abuturrab ta fadi ma yan garinsu gashi gidan ya cika da mutane yan biki, Aunty tayi mugun saka ta gaba tun da garin Allah ya waye, ko wani aiki da aike ita ake sa wa, da ta xauna xata tasota gashi abincin kirki ma bata samu ta ci ba, da rana yan matan amarya duk suka yi shirin tafiya saloon, dama kafin Ummi ta lura da Jiddah balle har tace mata ta bi su, aunty ta hada kayan wanke wanke a bakin pampo ta turata taje tayi, yawanci duk masu girki ranan sun xata ma mai aikin gidan ce Jiddah, ko mai aikin gidan bata yi aikin da Jiddah tayi ba tunda gari ya waye, cikin ruwan sanyi Aunty ke gallaza mata, duk tunanin Ummi kuma har da Jiddah aka tafi saloon don tun bayan da suka gaisa da safe bata ganta ba, a gajiye Jiddah ta fito daga kitchen wajen karfe hudu ga wani yunwa da take ji, wata tsohuwa ce ta mika mata purse tace “Yan mata ki kai min daki wajen Hajiya Hauwa ta adana min, kada a yasheni a gidan biki, dubu daya da dari biyar ce a ciki” Jiddah ta amsa tace “Toh” lkci daya Jiddah ta gane warce take nufi wato Ummi, bangaren Ummi ta nufa ta bude kofar parlon da sallama, Ummi da frnds dinta Uku ne a parlon sai wasu yan uwa guda uku, Jiddah ta gaishesu gaba daya, Ummi dai sai kallonta take da mamaki, Jiddah ta sunkuyar da kanta ta duka gefenta tana mika mata jakar tace “Ummi wai ajiya aka ce a kawo maki” Ummi ta amshi purse din tace “In ji waye?” Jiddah tace “Ai ban santa ba” Ummi tace “Dama baki je saloon din ba ke” Jiddah ta gyada mata kai kawai, Ummi tayi shiru tana son nuna ma yan uwan mai gidanta da kawayenta cewar ita ce matar Aliyu amma ta kasa, can dai tana kallon jiddah tace “Toh gobe sai a kai ki ke” a hankali Jiddah tace “Toh” daga haka ta mike, dai dai nan Abuturrab ya fito daga bedroom din Ummi, sosai gaban Jiddah ya fadi bayan sun hada ido, amma kuma sai taji dadin ganinsa ba kadan ba, duk yan parlon suka juya suna kallonsa, Ummi ma kallonsa tayi don tun daxu take fama da shi ya fito ya gaisa da yan uwan Abbansa su uku sun iso daga Damaturu amma ya ki fitowa wai ya gaji, gwara frnds dinta a parlon ya samesu da ya shigo, Hajiya Zuwaira ta rike ha6a tace “Dama Aliyu na ciki?” Ummi ta kirkiri murmushi tace “Eh bacci yake, saukansa daga kano kenan ko awa biyu ba ayi ba” Tuni Jiddah ta fita daga parlon, gaishesu Abuturrab yayi yana yake ya nufi kofa ya fita parlon Ummi ta bi sa da kallon mamaki har ya kulle kofar, har Jiddah tayi nisa yace “Keee” tsayawa tayi ta juya tana kallonsa, ya karasa inda take yana kallonta daga sama har kasa, gaba daya ta wani susuce, yace “Yaushe kika xo gidan nan” Ta sunkuyar da kanta tace “Umma ce tace mu taho…” ya kara kallonta daga sama har kasa sannan ya sa hannu ya ciro makulli a aljihunsa yace “Dakin dake ta can bangaren inda babu mutane, ki je can ki jirani” Tana kallon makullin tace “Bude kofar xan yi?” Ya hade rai yace “Aa kullewa xa kiyi, bakya jin hausa ne?” Juyawa tayi ta bar wajen don ta gane dakin da yake nufi babu wanda ke xuwa ta wajen, bata yarda ta kalli kowa ba har ta nufi bangaren ta sa makullin ta bude dakin sannan ta shiga, babban daki ne sosai babu abinda babu a ciki, sai dai abubuwan ciki ba masu hayaniya bane, sannan ba a wani cika kaya a dakin ba, xaunawa tayi kasa ta jinginar da kanta kan babban katifar dakin don gaba daya ta gaji, Bayan kusan minti sha biyar taji an bude kofar dakin ta daga kai da sauri, Shine ya shigo dakin, ya kulle kofa yana kallonta yace “Baki cin abinci ne?” Ta girgixa kai tace “Aiki nake yi shi yasa ban ci ba” Yace “Wani aiki?” Tace “Nayi wanke wanke da safe na share duk tsakar gidan, sannan na taya masu girki wanke naman kaza, wani wanke wanken ya taru na kara wankewa, kuma naje siyo ledan kwasan tuwo sau uku wajen da nisa sosai almajiri ne ya rakani, da na dawo kuma wani wanke wanken ya taru na sake yi, sannan na share tsakar gidan da aka bata….” Katseta yayi yace “Duk wa yake sa ki?” Ta sunkuyar da kai tace “Aunty” Bai ce komai ba, bayan kusan minti biyar yace “Tashi ki shiga bandaki ki hada ruwa kiyi wanka” Mikewa tayi ta nufi bandakin she looks so tired and worn out, ya juya ya fita ya sa ma dakin makulli ya cire ya tafi da shi, a parlor ya tadda Aunty na welcoming din bak’in da suka shigo da mugun fara’arta, ido hudu yayi da mahaifiyar Aneesah, Ya sauke kansa kasa sannan ya karasa cikin parlon ya gaisheta da ladabi bata ko kalli inda yake ba balle tayi kamar ta ji, Aneesah ce ta shigo parlon da jakar kayanta, Aunty ta rungumeta tace “Sannunku da xuwa manyan baki, ya hanya?” Aneesah na murmushi tace “Alhmdlh Aunty don ma dai jirgi muka biyo ai da sauki wahalan” Kofa Abuturrab ya nufa don ko hada ido bai son yi da Aunty, Babu yabo bbu fallasa yaji tace “Aliyu get them something meaningful to eat, kasan sha’anin abincin biki, ba lallai yayi suiting taste bud dinsu ba” Toh kawai Abuturrab yace ya fice daga parlon. Parking Abuturrab yayi bakin gate dai dai lkcn da driver ya sauke su Seeyama bakin gate din, duk suka nufi motarsa, bai amsa gaisuwar da suke masa ba, ya dau leda biyu na abinci yace “Ku kai ma Aunty” Seeyama ta amsa sannan suka wuce ciki, bayan few minutes ya bude motar ya sauka ya shiga cikin gidan rike da leda daya, direct part dinsa ya nufa, ya ciro makulli ya bude kofar ya shiga sannan ya kulle, Jiddah na kwance kan carpet idonta kulle, karasawa yayi yaga bacci take, ya buga katifar kusa da ita, firgit ta mike xaune, ya ajiye ledan hannunsa ya hade rai yace “Baki ce ma Ummi baki ci abinci bane duk yau?” Ta girgixa kai tace “Ban ganta ba tun da safe sai daxu da naje kai mata sako” Yace “Toh wa ya kawo ki gidan nan?” Tace “Nace maka Umma tace in taho tare da su seeyama” ajiye ledan hannunsa yyi ya mike ya koma can karshen katifar ya xauna ya fiddo wayarsa dake vibrate a tunaninsa Ahmad ne don yana restaurant ma ya kirasa, amma sai ya ga akasin haka don Aneesah ce ke kiransa, silencing wayar yyi, Jiddah ta bude abincin da ya ajiye mata ta fara ci. Mikewa yayi ya fita dakin ya kulle, kiran Aunty ne ya shigo wayarsa ya daga ya kai kunne bai ce komai ba yana tafiya, cike da fada tace “Amma walakancin ka da yawa yake, kasan bakin nan takanas daga Abuja suka xo, ba sai ka tafi ka samesu a masaukinsu ka xauna a nutse ka gaida su ba, amma ka wani gaishesu a tsattsaye ka fita kamar mara gaskiya, ko baka san mahaifiyar Aneesar bace?” A hnkli yace “Yanxu nake tahowa” Tace “Toh suna can uwar dak’ana” Yace “Alright” daga haka ya katse wayar ya nufi bangaren Aunty a ransa yana tunanin har ta huce kenan, or did she have anything in mind to punish him with, bude kofar parlon yayi, ya gaida frnds dinta dake xaune parlon, sannan ya nufi bedroom dinta, sai bayan da aka amsa sallamarsa sannan ya shiga, Mahaifiyar Aneesah na xaune tare da kanwarta sai Aneesah a dakin ga abinci iri iri a gabansu bayan wanda ya siyo masu, xaunawa yayi kasan carpet ya gaishesu da ladabi kansa a kasa, kanwar mahaifiyar Aneesar ce kawai ta amsa masa a dakile, uwarta kuwa sai cin abincinta take, Aneesah dai na xaune kan kujera sai kallonsa take ko kiftawa babu, kananun kaya ne jikinsa da suka yi matukar amsarsa, ga kamshin turarensa da ya cika ko ina na dakin, Kanwar mahaifiyar Aneesah Hajiya Maryam tace “Allah ya sanya alkhairi a bikin” Ya amsa da “Ameen” Ya d’an saci kallon mum din Aneesah dake fama da kaza, Mikewa Aneesah tayi ta fita daga dakin, Bayan few seconds ya mike yayi masu sai anjima ya fita shi ma, Hajiya Maryam ta tabe baki tace “Kaga mutum kamar shi yayi kansa, sannan ga nera, shi yasa Aneesah duk take daga ma mutane hankali, to in sha Allah komai ya kusa karshe ynxu ai” tsaye Abuturrab yaga Aneesah corridor tana jiransa, ya shafa kansa yace “U didn’t tell me tare da su Mumy xa ku xo” Tace “Ehh ai baka tsaya ka gama saurarata ba daxu kace ana kiranka ka katse wayar” Yace “Ohk, kinci abincin?” Tace “Bayan leda biyu ka siyo me xan ci a ciki?” yace “Ehh ai banga Hajiya ba i only saw u and mum” Ta tabe baki tana gyara siririn gyalenta, ya rungume hannunsa yace “Toh yanxu ya xa ayi?” Tace “Xuwa xa mu yi ka siya min abincin” Ya d’an yi shiru sai kuma yace “Toh ki jirani wajen motar xan dauko makulli a dakina” Tace “Ohkk” daga haka ta fara tafiya, ya bi ta da kallo sannan ya sauka xuwa dakinsa, makulli ya sa ya bude kofar xai shiga yaji muryar Aunty tana kiransa alamar tana biye da shi a baya, da farko niyyar kulle dakin yyi da makullin amma sanin xata yi suspecting abu sai ya fasa ya shiga dakin kawai bayan ya amsa kiran nata, Jiddah na tsaye bakin window ya nuna mata alamar ta shige bandaki, ai da gudu ta shige ciki ita ma jin muryarta, ta kulle har da sa makulli hakan ya kusa basa dariya, dai dai nan Aunty ta shigo dakin, ya xauna gefen gado yana shafa kansa yace “Ya gajiyan aiki Aunty?” Maimakon ta amsa sai ta sa makulli dakin ta shigo, shi dai kallonta kawai yake, ta kalli ledan abincin tace “Wannan fa?” Yace “Ni na siyo na ci” Kujera ta ja ta xauna tace “Abuturrab!!” Ya daga manyan idanuwansa ya kalleta, sake kiransa tayi murya can kasa yace “Na’am….” Tace “Dama Abuturrab ra’ayinka ne xuwa hayi kayi aure ban sani ba? Dama haka ka mayar dani gantalalliya ban sani ba” Ya girgixa kai yace “Wllh ba ra’ayina bane Aunty” tace “To son yarinyar ka fara all of a sudden? Da ka toxarta ni gaban ubanka?” Ya girgixa kai yace “Ko daya wllh Aunty” tace “Toh kawai xubar min da mutunci da walakanta ni gaban iyayenka ka so yi??” ya sauke wani ajiyar xuciya yace “Ba haka bane Aunty, kiyi hakuri” tace “Inyi hakuri?? Dama shirga ni kayi baka saketa ba Aliyu??” Da kyar yace “I’m finding it hard to confide in u anymore aunty…” Tace “Why??” Yace “U did what i never expected, kema kin san na kowa me sauki ne kan na Abba, how will u expect him to take it cewar na saketa da gaske? Wllh he can even disown me, kin fa san waye Abba, kin fi kowa saninsa, amma kika yi exposing dina wajensa” Da karfi tace “Karya kake, wllh baka saketa ba ni xaka mayarda sha sha sha yanxu? Are u stupid?” Yayi kasa da murya yace “Xa kiyi kaffara Aunty, nace maki ba aure tsakaninmu da yarinyar nan amma kuma bai kai har ki je ki gaya ma Abba ba, i trust u shi yasa na sanar maki” Shiru tayi tana kallonsa tana huci tace “Toh dadin xama kake ji da ita ne da kaki rabuwa da ita har yanxu???” Yace “Ko daya, idan na rabu da ita bata da wajen xuwa Aunty, Aunty da xa ki kwantar da hankalinki ki xuba min ido xaki ga me xai faru in sha Allah, i have plans wallahi, ba haka nan kawai na ajiyeta gidana ba, the house isn’t meant for her…” tace “Which nonsense plan Aliyu, dubi fa yanda yarinya tayi wani kyau ta kara uban haske fatarta lui lui kamar a latsa jini ya fito, a haka ne xan amince da kai baxan sa shakku a raina ba? Dubi fa yanda tayi fresh alamar bata da wani damuwa ta samu gida kawai, sbda ita ko weekend ka daina dawowa gidan nan sai dai ka sauka can kayi yanda kaga dama da ita, don wllh ban yarda baka harkanka da ita ba” Kallon Aunty ya dinga yi ba ko kiftawa, sannan yace “Inyi harka da ita fa fa kika ce Aunty” Tace “Toh eh mana, kana xaune da budurwa irin wannan a gida baxa kayi yanda kaga dama ba?” ya girgixa kai yace “Ba yanda kike tunani bane aunty, amma dai yanxu ya kike son ayi?” Aunty tace “Kawai ka dawo da ita gidan nan gaba daya da xama, she will be very useful wllh” Kallonta kawai yake yi, tace “Ko baka ji abinda nace ba?” Yayi murmushi yace “Na ji” tace “Wato baxa ka yi ba kenan??? Wato wllh ban ma yrda cewar babu abinda ke shiga tsakaninka da yarinyar nan ba da ya sa kaki rabuwa da ita har ynxu duk da ba auren” Ya girgixa kai yace “No plss, Wllh babu wani abu Aunty ai kinsan ba haka nake ba” Tace “Toh ka maidota gidan nan nace idan na isa da kai, tunda already tana nan kawai kayanta xaka debo gaba daya ka maido su nan” Ya shafa kansa yace “Toh Aunty amma sai mun yi magana da Ummi ko….” Wani kallo ta jefa masa tace “Sai kun yi magana da Ummi? Ni ban isa da kai ba kenan da xaka yi involving Ummi??” Yace “Kin isa” tace “Toh ba sai ka sanar mata komai ba, kawai taga ta dawo nan din, idan tace don me, sai kace ita kadai ce a gida kuma aiki ya maka yawa” Yace “Ohkk” mikewa tayi tace “Xan koma wajen bak’ina, bayan bikin xa muyi magana a tsanake” Daga haka ta bude kofa ta fita ya bi ta da kallo, mikewa yayi ya karasa ya kulle kofar dakin sannnan ya dawo ya bubbuga kofar bandaki, bude kofar Jiddah tayi ta fito tana kumbure kumbure tace “Don Allah kar ka dawo dani gidan nan kayi hakuri” sai kuma ta sakar masa da kuka, dariya abun ya basa, ya dake yace “Gidan namu kike kuka kar in dawo da ke??” Tace “Don Allah kayi hakuri” yace “Dole ma ki xauna nan din ki samu saiti sosai” Durkushewa tayi gabansa ta hade hannayenta tana kara rushewa da kuka tace “Aa don girman Allah kayi hakuri” Xaunawa yayi gefen gado yace “Kin fi son xama tare da ni kenan, duk da kince ni ba muharraminki bane?” Ta gyada masa kai a hankali tana share idonta, ya kauda kai yana murmushi, tuna Aneesah dake jiransa bakin mota yyi, da sauri ya tashi ya dau makullin motarsa ya fita ya kulle dakin ta bi sa da kallo. Har Aneesah xata shigo parlor suka hadu bakin kofa, sai da ya fara surveying wajen yaga ba mutane ya riko hannunta yace “C’mon dear, am sorry Aunty ce ta bata min lkci wllh” hararansa kawai take, yayi murmushi ya ja hancinta sannan yace “Mu je” duk abinda tace xata ci ya siya mata a eatry din da suka je sannan suka dawo gida, ta tafi bangaren Aunty shi kuma ya tafi dakinsa, bude kofar yayi ya tadda jiddah yanda ya barta, ya kulle kofar ya shiga bandaki yayi wanka ya fito ya sauya kayan jikinsa xuwa pajamas sannan ya kwanta…. Tun magrib Aunty ke ta neman Jiddah bayan wanke wanke ya taru amma bata ganta ba, har dakinsu Seeyama ta shiga ta tambayesu suka ce bata shigo ba, cikin dubara ta shiga bangaren Ummi nan ma bata ganta ba, kaf sai da ta xaga duk gidan har da leka kofar gida amma bata ga alamarta ba, wani abu ya dauke hankalinta ta ci gaba da harkar gabanta, sai wajen goma da wani abu ta farga har lkcn fa bata ga Jiddah ba, ta sake xagaye gidan ta koma dakinsu Seeyama da bangaren Ummi duk babu alamarta, mamaki ne ya cikata, to ko Abuturrab ya tafi da ita ne daxu da ya xo?? Wayarsa ta shiga kira xuciyarta na tafarfasa, Abuturrab dake kwance har ya fara bacci vibration din wayarsa ya tadasa, bude ido yyi a hankali ya jawo wayar, ya daga ya kai kunne ganin Aunty ce ke kiransa, daga daya bangaren tace “Abuturrab kana gidan nan ne?” Bin dakin yyi da kallo, lkci daya yace “Aa ina tare da Ahmad” Aunty tace “Au haba??” Yace “Ehh a nan xan kwana, da wani abu ne?” Ta girgixa kai tace “Aa tunda baka nan sai da safe kawai” Daga haka ta katse wayar tayi wani murmushi, dama so take ta ta66atar da cewar ba shi ya dauketa ba, addu’a ta shiga yi a ranta na cewar Allah yasa karawa gaba jiddah tayi kawai… Abuturrab ya kalli kasan carpet din dakin ya ga jiddah kwance ta gaji da kukan bacci ya dauketa, har ya koma ya kwanta ya mike ya bude press dinsa ya fiddo da xanin gado ya rufa mata sannan ya kwanta saman gado ya kashe wutan dakin. Karfe takwas din safe, Abuturrab ya gama shiryawa saboda Ahmad dake jiransa, babu abinda ya ta6a na breakfast da aka kawo masa ya bar ma Jiddah da ke bacci ya fita ya kulle kofar ya tafi da makullin, babu wanda ya lura da shi har ya bar gidan. Karfe tara da rabi Ummi ta shigo dakinsu Ramlah da frnds dinta tana kallon Ramlah tace “Wai Jiddah fa??” Ramlah tace “Na xata ta bi Umma, ai bata kwana gidan nan ba” Ummi tace “Umma kuma? Umma ta xo gidan nan ne jiya?” Shiru Ramlah tayi, Ummi ta juya ta fita taje gun su siyama su ma same reply da Ramlah ta bata suka bata, nan taji hankalinta ya fara tashi, Aunty ta samu, Aunty tace “Jiddah kuma?? Ai ni ban ma san tana gidan nan ba” Ummi ta juya ta koma bangarenta ta kira yar uwarta, bayan Umma ta daga Ummi tace “Ramlah…. Jidderh ta koma gidanki ne??” daga daya bangaren Umma tace “Jiddah?? Aa bata gidana” Katse wayar Ummi tayi ta ajiye da mamaki, Abuturrab ne ya fado mata, to ko jiya ya tafi da ita ne?? Hankalinta ya d’an kwanta tuna hakan da tayi, dialing numbersa tayi bayan ya daga tace “Ka dau matarka ne?” Abuturrab dake tare da Ahmad da wasu frnds dinsu ya d’an yi shiru, kunya yake ji yace mata ai tana dakinsa, kuma baya son ya daga mata hankali, don yana ce mata bai dau Jiddah ba hankalinta xai tashi sosai, ya d’an yi kasa da murya yace “Ehh Ummi” Tace “Sae ka kai ta ina??” shiru yyi bai ce komai ba, Ummi tace “Na lura da kai baka da kirki, baka da kara, ba kuma ka da hankali, Kawai ka dau yarinya kayi tafiyar ka da ita without anyone’s knowledge, duk ka bi ka daga min hankali, are this stupid? yarinyar da kake ikirarin ka aura ba da son ranka ba kamar yanda kake raina ma kanka hankali, Don wllh ba ni kake raina ma hankali ba, a sannu abinda ka kulla xai bayyana, did u think i am happy and relaxed with this ur marriage idan ba xuciyar musulunci ba?? duk ina lura da take taken ka a kan yarinyar nan kuma ko kaffara baxan yi ba da gangan kaje ka aureta ka xo nan kana raina ma ubanka hankali ba ni ba, to bari kaji, daga yau dama kada ka sake kawo ta gidan nan balle ka min rashin kunya yanda ka so, kaje can ka xauna da matarka a gidanku na yafe xuwanku wajena, duk da dama tun bayan da kaje kayi auren ka ba xuwa gidan uban naka kake ba, so just remain in ur house with ur so called wife” Tana kai wa nan ta katse wayarta, Abuturrab ya ajiye wayar ya jinginar da kansa da kujera yana tunanin abinda yasa yanxu kowa ke tunanin da gangan yaje ya auri Jiddah kawai pretending yake right from day one of the incident, to me yasa kowa ke ganin haka bayan shi ba da gangan ya aurota ba, mikewa yayi ya fita daga dakin, Ahmad ya bi sa da kallo…. Karfe sha biyu saura Abuturrab ya isa gida, face cap ne a kansa don bai son gaida kowa, kansa a kasa har ya nufi bangarensa ya ciro makulli ya bude kofar, Jiddah ta mike daga kwancen da take, ya shigo ya kulle kofar, ya xauna gefen gado ya dau wayarsa ya shiga kiran Siyama, tana dagawa yace ta xo dakinsa yana jiranta, ba a dau lkci ba Siyama ta xo, ya mike ya bude mata kofa, ta shigo ta gaishesa, duk da mamakin da ta yi ganin Jiddah a dakin amma bata nuna ba, sai murmushi kawai tayi mata, yana kallonta babu yabo bbu fallasa yace “Kaya xa ki dauko mata da Jilbab with ur Nikab now….” Siyama tace “Toh” sannan ta fita, sai ga ta babu bata lkci ta kawo ma Jiddah ankon da xa su saka ranan da Hijab da nikab, ajiye mata tayi gefen gado sannan ta fita, Jiddah ta tashi ta dau kayan ta shiga bandaki ta saka, bayan ta gama sakawa ta fito rike da nikab din tana kallonsa a hankali tace “Ban iya sakawa ba” Ya wani daure fuska yace “A haka xa ki saka, ko waye xai sa maki??” Kokarin sa wa ta shiga yi amma ta kasa, mikewa yayi ya fixge nikab din, ta runtse ido a tunaninta dukanta xai yi, ya shiga daura mata nikab din, bude ido tayi suka hada ido, da sauri ta rufe nata, har ya gama daura mata nikab din, yace “Fita ki jirani wajen motana” Ba musu ta nufi kofa ta bude ta fita, har ta isa tsakar gida kanta na kasa ta fita kofar gida gun motarsa, ya fito dakinsa ya kulle sannan ya fita shi ma….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button