JIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaune take a d’an karamin tsukakken tsakar gidan nasu da kwanon tuwonta a gaba sae dai ba ci take ba duk da kasancewar hannunta cikin kwanon, wata matashiya ce xaune cikin daya daga kananun dakuna uku dake D’an tsakar gidan hannunta rike da mafici tayi daurin kirji, xaune a tsakar gidan kan tabarma wani middle aged man ne da baxai wuce 58 ba, daga cikin dakin matar ke cewa “Munafuka algunguma kawai, sae ana magana tayi mukui ta ki cewa komai, a haka xaki kare cikin nukurci da bakin hali, banda haka uwar me ya ci min naira hamsin a kudina, ko da yake dama ae kin saba halin bera, sae dai na yau yayi min ciwooo tunda ko biyar ubanki bai kawo min yace gashi kiyi cefane ba, to a kan me??” Ita dai bata iya ta ce komai ba har lkcn hannunta na cikin kwanon tuwon ta kasa ci, mikewa matar tayi tana gyara daurin kirjin jikinta ta fito a fusace ta janye kwanon tuwon jin almajiri na bara tace “D’an malam shigo ka amsa” Malam Isuhu dake xaune saman tabarma yace “Ita kuma ta ci me Hansatu??” Wani kallo ta jefa masa tace “Sae ta ci wanda ka nemo aka girka yau” tana fadin haka ta juye ma almajiri ta ajiye kwanon tayi shigewarta daki, shi dai bai kuma cewa komai ba, a hankali ta mike ta dau kwanon ta kai wajen wanke wanke ta shiga hada kayan wanke wanken tsakar gidan, sae da ta gama gaba daya ta mike mahaifinta dake tsakar gidan har sannan ya fiddo hamsin a aljihunsa yace “Gashi ki je ko dankali soyayye ki siyo ki ci Jiddah” karasawa tayi ta amshi kudin da ladabi tace “Nagode Baba” bata rufe baki ba Hansatu ta fito da gudu ta warce kudin tana kallonsa da kyau tace “Saura dari hudu da hamsin kudin cefane na na yau” tana fadin haka ta kulle kudin bakin xaninta ta shige akurkin dakinta, Jiddah ta juya a hankali ta shiga dakinsu ba tare da ta yarda hawayen dake makale idonta ya xubo ba.

Washegari da safe wata dattijuwa da baxata haura 55 ba ta shigo wani babban daki ta kulle kofar tana kallon wanda ke kwance yyi rub da ciki saman gado, karasawa ciki tayi ta buga gadon, juyowa yyi da sauri ya mike xaune ganinta yace “Aunty ina kwana?” Tace “Jiya da daddare ina kaje har bayan isha baka shigo ba” yace “Aunty ina gidansu Ahmad fa, kuma tare ma muka dawo nan da shi na xata kin yi bacci shi yasa bamu shigo ba” Tace “Ohk, jiya Ahmad din ya dawo” Yace “Ehh” Tace “Ai na xata tadi kaje” D’an murmushi yyi yace “Tadi kuma Aunty… Ai tana Abuja” Tace “Atoh na sani ko ka kyallara ido ka ga wata ka watsa min kasa a ido??” Bai kuma ce mata komai ba sai murmushi da yayi, ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita ta kulle kofar, mikewa tsaye yyi yana kallon agogo dake nuna karfe tara ya shiga bathroom. Kasancewar ranan asabar ce sai kusan karfe sha daya Abuturrab ya fito daga dakinsa sanye cikin kananun kayan da suka matukar amsar sa, lkci daya kamshin turarensa ya gauraye parlon gaba daya, kanninsa mata ne xaune Main parlor din gidan, duk kallo daya suka yi masa suka dauke kai, bangaren Mahaifiyarsa ya nufa, Ramlah ta bi sa da kallo tace “Ummi ta fita fa” Ya juyo ya wuce side din Stepmum dinsa… A parlonta ya sameta tana yi ma autarta Aisha tsifa, yace “Xan je gidansu Ahmad Aunty” Tace “Breakfast din fa?” Yace “Ni nayi breakfast da asuba fa” tace “Oh ka dawo breakfast din asuban kenan” Yace “Ehh” tace “Kawata xata tafi Lagos ranan Monday daga kano shine nace kilan ma you will be piloting the plane….” Yace “In dai flight din safe ne” Tace “Na safen ne ma ina ji” Yace “Allah ya kai mu” Daga haka ya juya yace “Sai na dawo” yana fita parlon, Hajiya Amina da suke kira da Aunty ta kalli autarta tace “Me yasa baki gaida sa ba?” Aisha ta buda hannu tace “Wllh Aunty ranan ce mana yyi mu daina gaishesa a gidan nan idan yana nan, and he was serious about it” Aunty tace “Me ku ka yi masa?” Aisha tace “Babu komai, ranan Thursday da ya dawo duk muna parlor da su Aunty Safiyya muka gaishesa bai ce komai ba, muka sake gaishesa, har ya tafi ya dawo on a serious note yace mana kar mu sake gaishesa baya so, and since then no one is greeting him again and he is very comfortable with that” Aunty ta ta6e baki tace “Toh ai shkkn” A daki Abuturrab ya tadda Ahmad bayan ya isa gidansu, Abuturrab ya nufi window din dakin ya dage curtains din ya bude windon yace “Allow natural ventilation mana” Ahmad yyi dariya yace “Gaskiya ne bature, to kashe Ac din ko?” Abuturrab ya xauna yace “Aa bar shi, how are you?” Ahmad yace “Fine, ya su Ummi” Abuturrab yace “Cool” Ahmad yace “Are you flying on Thursday?” Abuturrab ya d’an yi shiru trying to recall his piloting schedules, kafin yace “Yea, Kano to Lagos, Then Lagos to Abuja, on Friday kuma Abuja to port harcourt” Ahmad yace “Ohk dama Maryam will be going back to schl Thursday I tot kana nan mu kai ta tare” Abuturrab ya ta6e baki yace “Ahmadu Bello?” Ahmad yace “Ehh” Abuturrab yace “Ka kai ta tasha ka sa ta a mota mana, kawai yarinya karama tayi ta juyaka” Hararansa Ahmad yyi, Abuturrab ya fiddo wayarsa dake ring yana duba me kiransa. Bude kofar dakin aka yi Maimuna ta shigo da tray dauke da warmer din danwake da tamarind drink a jug, ajiyewa tayi ta gaida Abuturrab da murmushi fuskarta yace “Ya kike Moon?” Tace “Alhmdllh, Yaya xan je Abuja fa” Yace “To sae ki xo in makala ki a jirgi ko?” Dariya tayi sosai tace “To ai shi sa na gaya maka” yyi murmushi bai ce mata komai ba, ta mike ta fita, bude warmer din Ahmad yyi, Abuturrab dake ta kallon danwaken warmer din yace “Ya ma abin nan da ka siya jiya a hayin Rigasa? Kamar shi nake gani a nan” Ahmad ya wara ido ido yyi dariya yace “Ohh wannan danwake ne, wancan kuma awara, kamar kuwa kasan yau ma xan je in siya, kaji dadin awaran nan kuwa? Gaskiya sun iya sosai, har Umma sai da ta ci, ni uku kawai naci su suka cinye sauran” Abuturrab ya dinga kallonsa da mamaki, can yace “Har komawa xaka yi kenan ka sake siya” Ahmad yace “Yes, I had intention dama” Abuturrab ya gyada kai bai sake ce masa komai ba. Har yamma Abuturrab na tare da cousin din nasa kuma abokinsa…. Su yi fada su shirya, duk bayan sati uku Ahmad ke shigowa kd yyi weekend daga Abuja don a can yake aiki as a medical Doctor, throughout weekend din kuma tare suke spending dinsa da Abuturrab idan shi ma yana garin, karfe biyar saura Ahmad ya mike yace “Captain mu je ka rakani mana pls” Captain ya kallesa yace “In raka ka ina?” Ahmad yace “Hayin Rigasa” Abuturrab yace “Aa sae dai Hayin banki, kaga malam mu fita tare kawai kayi hanyarka inyi nawa, don gida xan wuce yanxu in sha Allah” Ahmad yace “Ae ko baka isa ba, wllh sae ka rakani” Abuturrab ya dau wayarsa xae dau makullin motarsa Ahmad ya dauke yace “Sae ka tafi da kafa ai” kallonsa Abuturrab yyi, lkci daya ya wani hade rai, Ahmad ya fita dakin yana murmushi. Driving Ahmad yake yi, ya kalli Abuturrab dake xaune gefensa yace “Wai Aneesah fa?” Abuturrab ya gyara xama yace “She’s good, baka ji muna waya daxu ba” Ahmad ya girgixa kai yace “Kai ynxu da gaske mace da idanuwanta suke a bude da sunan wayewa kake so Captain….” Abuturrab yace “Look at you, kai baka san wayayyun sun fi tsafta ba, ni fa I don’t care…. As far as xata yi tsafta 100%, wllh ko haduwa da mace kazama ban son yi a rayuwata, sae inji gaba daya hankali na ya tashi, u know how sensitive I am….” Dariya Ahmad yyi yace “Ita Aneesar tana da irin tsaftar da kake so kenan” Abuturrab yace “Kai ma kasan da ba don haka ba da tuni ae na rabu da ita, kawai sae kaga mace ta ci kwalliya iya kwalliya ta fito amma just check inside, ni in dai mace na da tsafta ko kyanta bai fi 80% ba i will manage her…” Girgixa kai Ahmad yyi yana kallon titin gabansa, Abuturrab yace “Ba ga wajen danwaken can mun wuce ba” Ahmad bai san lkcn da yyi dariya ba yace “Aa D’an gyero ne ba danwake ba” Abuturrab dai bai ce masa komai ba da ya lura u turn yake son yi, dai dai gun awaran Ahmad yyi parking, wata yarinya ce da baxata wuce shekara sha daya ba xaune a wajen tana juya awaran cikin kasko, Ahmad na kallonta yace “Ina me awaran?” Yarinyar tace “Ta je dauko canji a gida shine tace in tsare mata, ae sunanta Aunty Jiddah, a gidansu Bibalo take…” Ahmad ya koma jikin motarsa yace “Gidan ba nisa?” Yarinya ta nuna masa wani rubabben layi dake gefensu tace “Can karshen layi ne, gidansu daya da Bibalo” Shi dai Abuturrab na xaune kujera me xaman banxa yana kallonsu, Yarinyar tace “Lah ga ta can xuwa” Duk suka kalli direction din da ta nuna, Tafe take fuskarta daure hannunta rike da yar karamin bokiti dake a rufe, wanda ke dauke da dafaffen awara, sanye take da hijab ruwan kasa da iyakarsa gwiwa duk man awaran da take tuya yayi staining Hijab din, Abuturrab ya d’an yi tsaki ya hade girar sama da ta kasa yana kallon titin gabansa, tana isowa yarinyar ta tashi tace “Aunty Jiddah gashi xa a siya a awara, da motarsu ma suka xo” Ahmad ya wara ido yace “Aunty Jiddah a bamu kalan na jiya” Ta daga kai ta kallesa tace “Na nawa?” Yyi murmushi yace “Yanda kika sa jiya” Bata ce komai ba ta durkusa ta sa masa awaran sannan ta mika masa ledan, dubu daya ya ciro ya mika mata, tana kallon kudin tace “Yanxu na kai kudi gida na amso canji, ka d’an yi hakuri sai in koma in dauko…” Ya juya ya kalli Abuturrab yace “Ko a siya maka kai ma Captain?” Kallon Abuturrab din tayi ita ma suka hada ido, yyi saurin dauke idonsa yaki cewa komai, Ahmad ya kalleta yace “Toh kinsan abinda xai faru me awara? ki ajiye canjin….” Da sauri tace “Aa ka jira in tafi in dawo ynxu” yace “To tsaya ki saurareni mana, ajiyewa xa ki yi gobe idan Allah ya kai mu na xo sai a bani awara na canjin” tace “Toh” murmushi yyi ya nufi mota rike da ledan awaran, sae da ya shiga motar ta ga ledan yajinsa bata sa masa ba ta mike da sauri tace “Kayi mantuwa” motar ta nufa tana mika ma Abuturrab ledan yajin, da mamaki yake kallonta kamar dai mugun abu take mika masa, yace “Kai!! kinga na siya abu a wajen ki ne?” wani kallon cikin ido tayi masa snn ta xaga ta mika ma Ahmad ta koma gun xamanta tana juya awaran kan wuta, Ahmad ya tada motar suka bar wajen yana hararan Abuturrab da ko a jikinsa. Jiddah na xaune a d’an dakalin kofar gidansu bayan isha, dawowarta kenan daga bakin titi ta gama tuyan dankali da take yi, ta ta takure waje daya cikin hijab din jikinta, wani matashi ne da baxae wuce shekara ashirin da tara ba xaune d’an nesa da ita, yace “Kin yi shiru Jiddah” Ta d’an kallesa tace “Nace babu wata matsala” yace “Kin tabbatar?” Ta gyada masa kai, yace “To ki ci gaba da hakuri kin ji…. In sha Allah idan…..” Kamar daga sama suka ji muryar Hansai, ta rike kugu tana kallonsa da kyau tace “Ta ci gaba da hakurin gyatuminka?” Ya kalleta ya duka har kasa yace “Ina yini Baaba” Ta wani sha kunu tace “Da ban yini ba xaka gan ni algungumi?? Ta ci gaba da hakuri a saboda ana cutarta ko? Sannan ban rabaka da kofar gidan nan ba? Dama tun da naga yara sun shigo da kayan tallanta ita bata shigo ba nasan da walakin goro a miya, shine nace bari dai in leko in ga ikon Allah” shi dai bai ce komai ba ya sunkuyar da kansa, tuni Jiddah ta mike ta makale da bango gabanta na faduwa, Hansai ta cire takalmin kafarta ta jefa mata a mugun fusace tace “Wuce ciki munafuka kawai, dama ban rabaki da wnn yaron mara tarbiya ba, ni xa ki ja ma abun kunya a unguwar nan?” Da sauri Jiddah ta shige ciki Hansai ta kai mata dundu da karfi, sannan ta maida dubanta kansa tana huci tace “Wllh na sake ganin ka tare da yarinyata gidan gayun garin nan yyi mana kadan da ni da kai, idan kuma karya ne mu xuba da kai” Tana kai wa nan ta shige ciki ya mike a hankali ya bi ta da ido….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button