JIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

07087865788….✍???? Almost done with free pages

???????? Jiddatul Khair????????

By khaleesat Haiydar????✍????

7…..

Fitowa Hansai tayi tsakar gida jin ana sallama, ganin aminyarta Zulai ta ce “Aa ashe Zulai ce, shigo daga ciki mana” Zulai tace “Ina ta addu’ar Allah ya sa in sameki wllh” Hansai tayi dariya tace “Ai ko kin ci sa’a, don yanxu haka shiri nake xan fita kasuwar tasha in saro kayan sana’ata” Zulai ta rike ha6a tace “Kin fara wani sana’ar ne banda awara?” Hansai tayi shewa tace “Ai ni na kwan biyu ma banyi awarar ba, amma kilan idan na fita yau dai in siyo har da waken suyan, yanxu su maggi, kubewa, kuka, daddawa… Kai duk dai mahadin miya da kika sani nake siyarwa, ko kwana hudu ban yi da farawa ba, sannan ina sa ran fara dillalanci kwanan nan” Zulai dake ta kallonta tace “Ikon Allahhh…” Hansai ta shiga d’an dakinta tana murmushi, Zulai na biye da ita a baya, bayan sun xauna Zulai tace “To ina yaran?” Hansai tace “Bibalo yanxun nan ta shiga makota, Ita kuma warcan gantalalliyar na can kwance wai ba lafiya” Zulai tace “To Hansai wani labari dai nake ji a gari, shine nace bari dai in sa6o gyale in taho…” Hansai ta gyara xama tana kallonta tace “Me ke faruwa? Wani labarin kika ji?” Zulai tayi kasa da murya tace “Yawo ake da ke wai bayan an kawo gaisuwan wannan yarinya jiddah har an saka rana kina turata gun wani me katuwar mota kullum sai ya xo kofar gidan nan, meye gaskiyan lamarin nan?” Hansai ta saki salati tana tafe hannu tayi mici mici da ido tace “Amma dai Allah ya tsine ma duk wani me sa ido a duniya, da yaushe da yaushe na turata gun me mota? Yau naga lalacewa, Jiya ne fa bata da lafiya shine ya siyo mata magunguna, kai ni Hansatu jama’a basu da gadonka amma suna da gadon maganarka…” Zulai tace “To waye shi me motar ma dai tukun” Hansai na huci ta lafto wani uban ashar tace “Duk wanda ya fasa sa min ido bai haifu cikin uwarsa ba a garin nan, tunda isuhu ya rasuwa wani shege ne ya ta6a kawo min kwayar masara balle shinkafa ko man kulli yace gashi ki ci kanki Hansai?? kawai sai don bawan Allah ya ga muna cikin matsatsi da yanayin rayuwa yana xuwa yana taimaka mana domin Allah sai a sa mana ido a hau mana bakin ciki da hassada a anguwa? Ni wllh ji nake kamar in siyar da gidan nan in bar gantalallen anguwar nan ko xan samu ci gaba” Zulai tace “Ke ni duk ba wannan ba tsoho ne mutumin nan ko yaro?” Hansai ta ja tsaki tana gyara xama tana huci tace “D’an yaro ne fa Zulai, ina jin ma saurayi ne bai ta6a aure ba, baki gansa ba bawan Allah wllh….” Zulai tace “Gun jiddar yake xuwa?” Hansai ta kalleta da sauri tace “Waye kuma jiddah? ita a wa xai xo wajenta? kema dai da wani xance wllh, xuwa fa yake idan yaga tana tuyar awara bakin titi ya mika mata kudade masu yawa ta kawo mana, ai ya san halin da muke ciki, d’an gayu ne fa sai kin gansa me kuma xai yi da wata jiddah kamar warce uwarsa tace masa je ka ka gani?? Haba Zulai, wllh da kyar ma idan ba daga Habuja yake xuwa ba don d’an gaye ne” Zulai ta d’an leka waje a hankali tace “Bacci jiddar take?” Hansai tace “Oho….” Daga haka ta mike ta fita, bude labulen dakinsu jiddah tayi ganinta a kwance tace “Wannan shegen kwanciyar baxai fissheki ba idan xa ki tashi ki kwashi bokitai ki fita gashi can an kawo famfo bakin titi ki jido mana ruwa ko na alwala ina jin babu a gidan nan, tun safe kin wani makale daki a kwance kamar ruwa” daga haka ta fice daga dakin ta koma nata, jiddah ta mike xaune daga kan darduman da take a kwance bayan tayi sllhn azahar, duk da jikin nata ya mata sauki, amma idan ta tashi jiri take gani ga yunwa dake dawainiya da ita, tun safe kunu kadai ta sha kosan da aka siyo ma bata ga idonsa ba balle a bata ta ci, sai da Jiddah ta bar gidan da bokitai sannan Zulai ta rike kunnenta daya tace “Anya ba son jiddah mutumin nan yake ba kuwa Hansai, banda haka hidimar uban me xai maku, ku da ku ke gida, ga almajirai can a titi, ga gidajen marayu a gari” Hansai tayi kasake, sae kuma tace “Sonta kuma? Ta ina xai so ta Zulai, babban mutum ne fa, kudi yake bata ta kawo min mu kula da kanmu tun bayan mutuwar Isuhu fa….” Zulai tayi wani murmushi irin na boss tace “Lallai Hansai, ashe har ynxu da sauran ki, to wllh da kyar idan ba sonta yake ba me yasa bai mika ma Bibalo ta kawo kudin ba sai Jiddar” Hansai tayi tsaki tace “To Bibalo sana’a take min a bakin titi da xai ganta ya bata? Ai sai dai Jiddar dake bakin titi kullum” Zulai tace “To wllh ki farka daga wnn baccin da kike, kada ki kuskura ki bada kofar da xai shigo da wani batu bayan ihsanin da yake maku, idan kuwa kika yrda to kina ruwa, ga dai Bibalo ai ita ya kamata a so tunda da gatan ta, amma har kika yarda ya shigo maki da wani batu kan Jiddah to kashin ki ya bushe kina ji kina gani Jiddah xata xama matar babban mutum….” Shiru Hansai tayi tana kallonta ko kiftawa babu da alamar xancen Zulai ya gigitata, Zulai tace “Atoh, kada ki kuskura wllh, ihsanin ma idan son samu ne kada ki sake amsa don a bisa dukkan alamu ya ga Jiddah ne ya kyasa, to jiddah kuma a wa Allah na tuba, yarinyar da ko dangin kirki bata da, kai ina ma ta gansu, ke fa kadai ce gatan ta a duniya, ba dangin uwa balle na uba, yau da xaki koreta sai dai ta bi duniya bata da wajen xuwa….” Hansai tace “Toh wai hauka nake yi ne Zulai, bayan an amshi gaisuwa gun Iliya so kike d’an iskan ya 6a66aka ma gidan nan wuta mu shiga uku? ai jiddah yanxu bata da maraba da matar aure, Iliya ya kawo komai sadaki kawai ya rage da daurin aure, shi ma ni ce na ja lkcn ai an sa ranan kusa kusa na daga” Zulai tace “Atoh, tun wuri sanar masa ya dawo ayi ayi auren kawai, kinga wannan mutumi kam dole ya komo ma Bibalo….” Hansai ta sharce wani xufa tace “Ni dadina da ke akwai hangen nesa wllh Zulai, kinga bbu wanda ya xo ya wayar min da kai banda ke ina nan ina ta haukana, bari in sa a kira min Iliyan dama sbda kudin katifar da xan siya mata ya sa nake ta jan auren naki yrda a sa sati biyu kamar yanda ya bukata, amma tunda haka ne kuma ga wnn bawan Allah ya bamu kudade masu tsoka kema har na cire maki dubu biyu a ciki, sai ki rakani kawai gobe ko tsohuwar katifa ce in siya mata da ‘yar robobin aikin gida” Zulai tace “Shkkn kuwa” kasa karasawa cikin compound din Jiddah tayi da bokitin ruwa a kanta jin abinda su Hansai ke cewa, ta fi minti uku tsaye duk tana sauraronsu Zulai tace “Idan kin kirasa kice yace a sa bikin sati biyu kawai kin shirya a wuce wajen” Hansai tace “In sha Allahu haka xan yi” A hankali Jiddah ta karaso ciki ta juye ruwan kanta duk suka yi tsit, ta juya ta fita tsakar gidan lkci daya hawaye ya kawo idonta, ita dai bata ji xancensu na farko ba amma daga inda suke cewa xa su ce Iliya ya dawo ayi auren ta tsinci maganar su. Bayan ta fito ta so shiga gidan Iyah amma sbda irin warning din da Hansai tayi mata yasa bata shiga ba, inda xata shiga tayi kukanta me isarta take nema, a haka ta dinga jan kafa har ta isa inda pampon yake ta jingina da bangon wani gida tana share hawayen dake makale idonta, ko yaushe xai kawo mata piya piyan da yace xai kawo mata, ji tayi baxata iya jiransa ba kuma, gwara kawai ta siya da kanta duk da kudin da ya rage mata yanxu bai wuce dari biyu ba tunda Hansai ta rabata da Usman dinta ta karfi da yaji, don kuwa wanke kafa tayi ta tafi har gidansu can cikin gari ta sanar ma iyayensa su ja ma d’an su kunne ya fita harkar ‘yar ta jiddah don an sa mata rana, tun daga sannan kuma rabonta da Usman. Washegari da sassafe Hansai ta fita xuwa gidan Zulai don daga can xasu wuce kasuwan dillalai yi ma Jiddah siyayyar aure, wata tsohuwar katifa ce da ko riga babu suka siya a farashi me sauki da pillow kwaya daya, sai robobin kitchen su ma duk tsofaffi, hatta wuka basu siya sabo ba sai tsoho, suka dai kwaso tarkacen da xa a iya kai ta gidan miji da shi, suna shirin barin kasuwan Zulai tace “To baki siya xanin gado ba” Hansai tace “Ina da wani a karkashin akwati xai yi shekara goma da ajiyesa sai in bata kawai, buta kuma ta tafi da na ubanta yana can ba amfani muke da shi ba” A barrow suka kima kayan suka dau hanyar gida. Tunda Jiddah taga siyayyar da suka yi wanda ke nuna cewar an kusa aurenta da Iliya hankalinta yyi mugun tashi, Hansai kuwa tuni tayi kiran Iliya da ya sanar mata sun ma kusa shigowa kaduna, bayan ta katse kiran tana kallon Zulai da wata kawarsu Dije da ta rakasu siyayya tace “Atoh ai shkkn, yace sun wuce Abuja, kun ga wannan karan kenan da matarsa xai koma legas din” Zulai tace “Ahh shkkn, Allah dai yasa ayi bikin da mu” Dije tace “Ameen, ai Hansai ‘yar halaq ce, babu wanda yayi tunanin xata yi ma jiddah wannan abun arxikin, kowa gani yake tunda Malam Isuhu ya kwanta dama shkkn watsi xata yi da jiddah, sai gashi ta ba mara da kunya, kuma in sha Allahu baxa ki ta6e ba, kin cika yar halaq wllh” Hansai tayi murmushi tace “Toh Allah na tuba ko uban na da rai wllh ba samun hakan xata yi daga garesa ba, sai in idanuwansa xai kwakule ya siyar yyi mata kayan daki, uban me garesa banda wannan rubabben gidan, bashi da komai sai wahala wllh” Zulai ta kwashe da dariya tace “Allah dai ya ji kansa, gashi nan kin rufa masa asiri kin rufa ma ‘yar sa asiri, kin mata abun arxiki” Washegari Hansai ta azalzali Iliya da kira nan ya sanar mata nan da kwana biyu xa su je can gidan kawun nata da ake xancen auren a wajensa tare da magabatansa sai a saka sati biyun da tace, amma fa ba shi da kudin sadaki a yanxu sai dai a biyosa bashi, Hansai tayi shiru tana sauraronsa, can tayi kasa da murya tace “Iliya da kudin sadakin fa nake son yi mata dinki tunda ba lefe xaka yi mata ba kace baka da halin yi….” Ya katse ta cikin fada yace “Gashi nan da duk kudin hannuna na siyo maki masara kwano 8 da gawayi, ko in siyar in kai kudin sadakin?” Da sauri tace “Aa to ai tunda kace idan ka samu xaka bada babu wani damuwa xan ma kawun nawa bayani, Allah yayi maka albarka, ai kowa yasan kai me xuciyar yi ne Iliya, to a ina xaka ajiye Jiddar?” Yace “Ehh akwai shago daya gaban gidan kakana sai ta xauna nan kafin in sama mata haya” Tace “Atoh shkkn, ni na xata legas din xaku wuce tare ince shkkn xaka rabani da Jiddah gaba daya” Yace “Aa nan xan bar ta, mu ma gareji muke kwana a legas din” Hansai ta xaro ido tace “Atoh Allah ya rufa asiri, tunda ga gida ka samar mata a nan din shkkn, Allah ya kai mu wannan rana dai” Yace “Ameen” daga haka ta katse wayar tace “Toh ba shkkn ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button