JIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL
Abuturrab na kwance cikin resting cabin din jirgin da yayi piloting tare da Co-pilots dinsa daga lagos xuwa kano, ko minti talatin basu yi da alighting ba, idonsa a lumshe suke duk da ya rufe fuskarsa da hulan uniform dinsu na pilot dake jikinsa, tapping dinsa aka yi a kafa, ya xame hulan a hankali, Co-pilot dinsa ne tsaye kansa, pilot din yyi wani sigh yace “Done with the Secure Cockpit checklist…. Can we??” Abuturrab ya mike xaune yace “Alright…” Pilot din yace “Ain’t you changing??” Abuturrab ya kalli uniform din jikinsa yace “Not at all” Jakunkunansu suka dauka suka sauka jirgin, sai da suka gaisa da incoming crew da suka hadu da sannan suka shiga cikin airport din. Driving Abuturrab ke yi cikin motarsa da yake bari a airport, hotel din da yake sauka yawanci idan yana kano ya nufa, duk da Abbansa na da gida nan kano wanda ke a kulle babu kowa ciki baya sauka gidan don baya son xama shi kadai shi yasa ma idan kwana ya kamasa a Abuja, it’s either su kwana gidansa tare da Ahmad ko Aneesah ta xo tayasa xama, ya so tafiya kaduna yau amma bai samu flight me xuwa kaduna ba or even private jet, yana shiga hotel din ya karbi daki kamar yanda ya saba, wanka yyi ya sauya xuwa kananun kaya, yayi sllh sannan ya bude pepper soup din hanta da ya sa a kawo masa with cup of coffee, ya fara ci a hankali, ajiye spoon din hannunsa yyi tunawa da yayi bai samu Mu’axxam yayi masa magana ba a kan yarinyar nan ta Hayin rigasa, ya dafe kansa don shaff ya mance, tun a jirgi da ya tuna yake Allah Allah suyi alighting ya samesa da maganan, he can even go to d extent of taking all the marriage responsibilities in har Mu’axxam din yace bashi da hali, tsaki ya d’an yi don gobe da sassafe yake son driving xuwa kaduna baxai shiga airport din ba, a hankali ya ci gaba da shan pepper soup dinsa har ya ji ya ishesa sannan ya tashi ya shiga bandaki ya wanke bakinsa ya fito yayi kwanciyarsa. Washegari Saturday karfe goma saura Abuturrab ya shigo compound dinsu… Parking yyi kusa da motarsa da yake amfani da a kaduna, ya sauka sannan ya shiga ciki, part din Aunty ya fara nufa ya sameta parlonta tana breakfast, ganinsa tace “Daga ina haka kamar an jefoka captain?” ya xauna kasan lallausan carpet din parlon yana murmushi yace “Daga kano nake” tace “Ikon Allah welcome son…” Yace “Ina kwana Aunty?” Tace “Lafiya lau ya hanya?” Yace “Alhmdlh” mikewa tayi tace “Let me get u breakfast” Bata jira cewarsa ba ta fita, sae gata ta dawo tare da mai aiki rike da tray din breakfast din, Mai aikin ta gaishesa sannan ta ajiye, ganin kallon da yake ma tray din Aunty tayi dariya tace “Taimaka min kawai tayi ta dauko flask din ba wai ita ta hada maka ba…” Bai ce komai ba ya dau cup dake a kife ya juya yana kallon ciki keenly kamar yana neman abu, Aunty tace “To yanxu da ba Aneesah bace budurwar ka ya xaka yi da wannan kyankyanin captain, yan matan yanxu da son jiki duk ya sa sun xama kazamai” Ba tare da ya kalli Aunty ba yace “Allah ya ga xuciyana shi sa bai hadani da mara tsaftar ba” Dariya kawai Aunty tayi tace “Jiya ma Aneesar ta kirani mun gaisa ashe ta koma Abuja” Yace “Ehh ta koma…” Tace “Idan ka gama sai ka ajiyeni U-rimi don Allah, driver baya nan kuma bana son driving” Yace “Alright” Yana gama breakfast din kuwa ya mike, tuni ta dauko mayafinta da yar jaka, yace “Salem fa?” Tace “Tun yaushe Salem ya koma makaranta” Abuturrab yace “Ohh yea mun yi chatting ya gaya min, but na manta” Sai da suka fita parlon ya tuna bai je gaida Umminsa ba, ya d’an buda ido yace “Aunty bari in shiga in gaida Ummi yanxu in fito” Ta d’an 6ata rai tace “Yanxun nan fa xaka ajiyeni ka juyo Captain, cikin mintuna kadan xaka dawo ai” Bai ce mata komai ba ta fara tafiya ya bi bayanta walking slowly. Abuturrab bai dawo gidan ba sai bayan la’asar tare da ita, tana rike da ledojin atamfofi da ta sa ya siya mata a gidan da suka je, ta nufi part dinta, shi kuma ya shiga bangaren Mahaifiyarsa, kanwarsa Ramlah kadai ce parlon tana shara yace “Ummi fa?” Tace “Ta fita tare da driver yanxu” Ya shafa kansa yace “Ohk…” Juyawa yyi xai fita tace “Shine baka shigo ka gaisheta ba kuma tun safe ka dawo yaya” Ya juya ya mata wani kallo yace “Yaushe na fara wasa da ke?” Shiru tayi bata ce komai ba, yyi kwafa ya fice daga parlon. Bedroom dinsa ya shiga, sai bayan da yyi wanka ya sauya kaya sannan ya fito main parlor rike da makullin motarsa, har xai fita ya nufi kitchen jin movement a ciki, Safiyya ce a kitchen din da Ramlah sai mai aiki da alama dinner suke dafawa, yace “Is there anything to eat here?” Safiyya ta kallesa tace “Aa ba a gama ba” Juyawa yayi ya fita daga kitchen din ya bar parlon gaba daya, sai da yayi sllhn magrib sannan ya bar anguwar… Parking Abuturrab yyi yana kallon cikin karamin layin da babu haske banda na wata, yara ne bakin wani tap suna ta diban ruwa suna wasa da ruwan, tun da yamma ya so xuwa amma sbda comment din Umar a kansa ranan a hospital yasa ya ki shigowa anguwar da yamman, ya sauke glass yana ta kallon yaran, da hannu yyi ma wani yaro cikin yaran alamar ya xo, yaron ya taho da sauri, dari biyar ya dauka cikin motar ya mika ma yaron yace “Kaje can gidan da ake siyar da awara ka kira min yarinyar dake siyar da awaran” Yaron ya ruga da gudu xuwa gidan, yana isa ya kutsa kai ya shiga, Hansai na xaune tsakar gida Bibalo na haska mata fitila tana daure busasshiyar kubewa a leda, Yaron yace “Ina wuni maman Bibalo” Hansai tace “Lafiya lau, me xaka siya?” Yace “Aa wani me mota ne yace in kirawo me awara” Hansai ta kalli Jiddah dake duke bakin kwaroron wanke wanke tana yi, Hansai tace “To ai kuwa xuwa xaki yi ki ji me ke tafe da shi, tunda yasan yanayin garin kilan wani alherin ya xo mana, ko kuma Bibalo ta je, yan sa idon anguwar nan sae su iya juya mana xance yanxu yanxun nan….” Jiddah dai bata dago ba ta ci gaba da abinda take yi, Mikewa Bibalo tayi da sauri ta ajiye fitilan hannunta tace “Bari in je ni” Mayafi ta figa ta fice daga gidan tana ce ma yaron taho ka nuna min inda yake, can bakin titi yaron ya nuna mata, Abuturrab ya dinga kallonta daga cikin motar, tun daga tafiyar ya gane ba jiddah bace har kuwa ta iso bakin titi, tsaye tayi jikin motar, ya sauko yana kallonta, tayi fari da ido tana wasa da mayafin kanta tace “Sannu da xuwa….” Yace “Ina ‘yar uwar taki” ta buda ido sosai tace “Yo ae ta daina fitowa ynxu sbda bikinta sati me xuwa ne, kasan har iyayen iliya sun xo anyi komai yau…” Kallonta ya dinga yi ko kiftawa babu, tace “Idan wani abu ne gani ni ka bani in ji Baabarmu in kai mata” Ya dauke kai daga kallonta yace “Mu je xan ba Baabar taku da kaina” Da sauri ta shiga gaba yana biye da ita, sae wani rangwada take har suka iso kofar gidan, tace “Bari in je in mata magana” daga haka ta shige ciki, Hansai na ganinta tace “Me ya baki?” Bibalo tace “Yace ki je yana kofar gida” Da sauri Hansae ta figi gyale ta yafa ta fita kofar gida, dukawa tayi ta gaishesa ya sauke idonsa shi ma ya gaisheta, ta amsa cike da nutsuwa tace “Sannu da xuwa Alhaji”
07087865788✍????
???????? Jiddatul Khair*????????
By Khaleesat Haiydar????✍????
8…..
Hansai ta shiga kame kame tace “Gashi babu ma wajen xama a nan Alhaji, ko xa ka shigo daga ciki a shimfida maka tabarma” Yace “Aa nagode, hakan ya isa…” Tana murmushi tace “Allah sarki… Da yake jiddar na daurayan kwanuka shine nace ‘yar uwarta ta fito, jiki kam alhmdlh taji sauki sosai, duk ta shanye magungunan nata…” Abuturrab ya sauke idonsa kasa yace “Allah ya kara mana lafiya gaba daya” Hansai tace “Ameen, bari dai kawai in shiga in turo ta ku gaisa, ai yanxu nasan ta gama” daga haka ta shige gida ganin dai babu alamar Abuturrab xai bata komai, jiddah ta nufa da sauri, murya can kasa kasa tace “Tashi ki dau hijabinki ki saka ki fita yana nan kila ya fi gane ya baki, kada ki kuskura ku tsaya kofar gidan nan ki ja shi can karshen layi sbda yan sa ido, gashi iliya na gari, daga nan ma sai ki sanar masa bikin ki sati me xuwa ne idan Allah ya kai mu, kinga idan da akwai wani alkhairin da xai maki sai ya maki, kowa dai yasan ke marainiya ce ba uwa ba uba” Bibalo da ke tsaye kansu tana sauraron abinda suke cewa tace “To Baabarmu idan yaji xata yi aure fa kilan shkkn baxai sake dawowa ba, dama ba sbda awaran da take yi bakin titi bane yake tausaya mana yake bamu kudi?” Hansai tayi shiru, can tace “To kuma aure ae dole tayi abu saura sati daya dai har an gama komai, kawai ta gaya masa.. sannan ba ga ki ba, ai ke xaki ci gaba da yin awaran a bakin titi” Bibalo tace “Cabdijam, wllh baxan yi awara bakin titi ba kawayena da samarina na ganina, haka kawai?? sai dai ke ki dinga yin kayanki ni dai baxan yi ba, to ni ma ba sai a min auren ba kawai” Tana fadin haka ta shige daki tana gunguni, Hansai ta rike ha6a tace “Ikon Allah, yau naga jarababbiya, a maki aure? Duka nawa kike xa a maki aure, ita ma Jiddar ai don iliyan ya dade yana sonta ne kuma ya mana hidima ba kadan ba, ko so kike ya mana tijara yace sai mun biyasa? A gidan uban wa ma xan samu abun biyansa? ke kuma da nake da burin in samar maki makaranta cikin gari ki fara xuwa kya kawo xancen a maki aure, a can din sai kiga Allah ya hadaki da miji dai dai ke, nan banda yan kato da gora, da yan adaidaita sahu, ga leburori, ga yan gwangwan sai yan iskan anguwa, to waye sa’an auren ki duk cikinsu? Ai babu sa’an auren ki wllh, ke da kike matar babban mutum” Hansai ta kalli Jiddah da kanta ke kasa har lkcn tana sauraronta, ta hade rai tace “Baxa ki tashi kije ba kin bar bawan Allah tsaye a waje” Jiddah ta mike a hankali ta dauraye hannunta ta shiga daki ta dau Hijabinta ta sa, ta saka takalminta sannan ta fita Hansai ta bita da sauri murya can kasa kasa tana cewa “Ku bar kofar gidan ku je can bayan layi kada a samu me kai ma Iliya rahotu” Ita dai bata ce komai ba har ta fita, yana tsaye ya rungume hannayensa, a hankali ta karasa can jikin wani tsohon adaidaita da aka yi parking gaba da gidan nasu, ya bi ta da kallo sannan ya bi bayanta, jingina tayi da adaidaitan tana kallonsa cikin sanyin murya tace “Sakon da kace xaka kawo min fa?” Yayi shiru yana dubanta, ta fashe masa da kuka tace “Kasan baxa ka kawo min ba me yasa kace xaka kawo min?? Alkawari fa ka min” Ya rungume hannunsa yace “Ohk abinda kika ce xa ki sha??” Ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, yace “Yaushe xa a daura maku auren?” Tace “Sati me xuwa, don girman Allah gobe ka kawo min, naje na tambaya a shago ance min ba dari biyu bane, kuma ni dari biyu gareni” Bude baki yayi yana kallonta da mamaki, can yace “Yaushe kika je kika tambaya?” Cikin rawar murya tace “Jiya” Ya sauke idonsa yace “To ai ni nace xan kawo maki ko? Kuma ban manta ba” Tace “Toh baka sake xuwa ba ai tun ranan” Yace “Toh gobe xan kawo maki” Ta gyada masa kai tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, Sauke idonsa yyi kasa yace “Wa kika sani a kaduna bayan Baabar nan taku?” Ta girgixa masa kai a hankali tace “Ba kowa” Yace “Wa xai daura maki aure?” Cikin rawan murya tace “Kawu Jibril” yace “Waye shi?” Tace “Kawun Baabarmu ne shi” Shiru yyi na kusan minti daya sannan yace “Ki koma kice da Baabarku xan yi magana da ita” Juyawa tayi ta koma ciki, Hansai na xaune tsakar gida tana fifita tana jiranta, ganinta ta mike da sauri tace “Ya aka yi kika dade, nawa ya baki?” A hankali Jiddah tace “Yace xa ku yi magana da shi” Hansai ta hade rai tace “Bai baki komai ba?” Jiddah ta gyada mata kai, Hansai tace “Toh ba naje ba mun gaisa, maganar me kuma xa mu yi” Bibalo ta leko tace “Ke dai kije ki ji abinda xai ce maki kawai” Hansai ta nufi kofar gida da sauri, tana ganinsa ta sunkuyar da kai tana d’an murmushi tace “Cewa tayi kace xa mu yi magana ko?” Yace “Eh, yanxu take gaya min sati me xuwa xa ayi aurenta” Hansai tayi kasa da murya tace “Wllh kuwa, tun uban na da rai ya ci bashin da ya fi karfinmu, bamu da halin biya, to dai kusan auren biyan bashi ne, tunda mu dai bamu da kowa duniyar nan banda Allah, bamu da kowa bamu da komai sai rubabben gidan can, to ya xan yi??” Tana fadin haka ta fara matsar kwalla, kallonta kawai Abuturrab yake da mugun mamaki, can yace “Nawa ne kudin bashin?” Goge idonta ta dinga yi tana tunanin kudin da xata lafto, can dai tace “Dubu dari ne da ashirin wllh” Yace “Ina shi me kudin?” Nan fa hankalin Hansai ya tashi, cikin rawan baki tace “Ehh to ba garin yake ba, kawai sai dai a kai masa, noma kawai yake yi a nan amma ba d’an garin bane” Abuturrab yace “Ohk, shi ne xai aureta?” Tace “Ehh, Aa ba shi bane gaskiya, d’an sa xai aura ma, ehh babban d’an sa xai aura ma” Abuturrab yace “Ohk, dama akwai wani aiki ne da nake son in bata ta dinga yi, duk wata xa a dinga biyanta dubu dari biyu, kinga idan tayi aure baxai yiwu ba, naga kuma ta fi ‘yar uwarta kwazo, dama tana farawa da wata biyu sai a kawo yar uwartata, kafin nan ita ta kware sai ta dinga sa ‘yar uwar a hanya” tuni xufa ya fara keto ma Hansai tana kallonsa tace “Dubu dari biyu fa kace Alhaji?” yace “Ehh haka albashin yake, amma dai yanxu xan je in ciro kudi in bata sai ta kawo maki ki biya bashin… Xancen auren kuma sai a fasa shi” Hansai na share wani xufa da kyar tace “Toh ai shkkn Alhaji, Allah ubangiji ya kara maka girma da daukaka, yanda kake rufa mana asiri haka Allah xai rufa maka asiri kai ma” Yana kallonta yace “Ameen, amma kina ganin auren xai fasu idan aka biyasu bashin su?” Da sauri Hansai tace “Ba dole ba, dama ai sbda kudin ne suke son rabani da diyata” Yace “Toh xan je in ciro kudi yanxu…” Hansai tace “Toh turo maka ita xa ayi kuje tare?” Yace “Ehh” juyawa tayi da sauri ta koma ciki, Jiddah na daki ta hade kanta da gwiwa Hansai tace “Jiddah tashi xa ku je ya baki kudi ki kawo yanxu, duk abinda yace maki kar ki kuskura kice ba haka bane, komai yace kice masa ehh haka ne, kinji me nace??” Kallonta kawai Jiddah ke yi, Hansai ta hade rai tace “Baxa ki tashi ba an bar sa a tsaye” a hankali Jiddah ta mike ta fita dakin, yana nan tsaye ta samesa, Sai da ya kalleta sannan ya fara tafiya, bin bayansa tayi har suka isa bakin titi inda motarsa yake, Bank ya tafi a can cikin garin don cire kudi a Atm machine, ta bi sa da kallo bayan ya sauka motar, bayan wani lkci ya dawo ya shiga motar ya dau karamin leda ya xuba kudin a ciki ya ajiye, bayan few seconds yace “Tace auren biyan bashi xaki yi” Ba tare da ta kallesa ba tace “Ba haka bane” ya kalleta da sauri yace “To ya ne?” Hawaye ya kawo idonta tace “Kawai aure take son yi min da iliya sbda yana kawo mata abubuwa daga legas idan xai dawo” Abuturrab yace “Shi a ina yake xaune a kaduna?” Tana share idonta tace “Nan hayi yake shi ma” Yace “Xa ki nuna min gidansu?” Ta d’an yi shiru kafin ta gyada masa kai, tada motar yayi suka bar wajen, sai da suka shigo hayi yace “Ina ne gidan nasu?” Tace “Can gaba ne amma hanyar bbu kyau mota baxai shiga ba kuma da akwai nisa, dole sai da adaidaita” Yace “Ohk…” Ta gyada masa kai kawai, dai dai layinsu ya tsaya, ta dinga jiran ya bude mata motar ganin bai bude ba ta kallesa, yace “Yanxu idan aka fasa auren naki xaki hakura da kashe kan naki?” Shiru tayi tana kallonsa, ya d’an hade rai ganin kallon da take masa yace “Ina sauraron ki?” Sunkuyar da kanta tayi tace “Ehh” bude mata motar yayi ya mika mata ledan kudin ta amsa, xata sauka yace “Jira” Komawa tayi ta xauna tana kallonsa, yace “Kin iya amfani da waya?” Ta kallesa sannan ta girgixa masa kai alamar A’a, kunna fitilan motar yyi ya dau pen da wani karamin jotter ya rubuta numbersa ya mika mata yana dubanta yace “Idan da akwai wani abu ki nemi me waya ki kirani” Ta gyada masa kai, yace “Sauka” Ba musu ta sauka motar ta rufe masa ta fara tafiya…. Hansai na ta xaune tsakar gida tana jiran shigowar jiddah, sauro duk ya cijeta sai soshe soshe take, ganin jiddah ta shigo ta mike da sauri tana kallon ledan hannunta ta karasa kusa da ita ta amshe ta bude…. xaro ido tayi tana kallon uban kudin ciki, Jiddah dai na tsaye sai kallonta take ita ma, daki Hansai ta shige da gudu duk ta rude don yan dari biyar biyar ne kudin shi sa yayi yawa, Jiddah ta juya a hankali xata shiga dakinsu kenan aka shigo gidan babu ko sallama, Iliya ne da abokansa biyu kamar an hankadosu sai muxurai suke, ya nufi Jiddah yana huci ya fixgota ya xabga mata wani wawan mari cikin katon muryarsa yace “Uban wa ya sauke ki a mota yanxu?” Hansai na jin muryarsa tayin sauri cusa ledan kudin can karkashen jakarta tana salati ta fito da gudu, wani marin ya sake wanka mata ya hadata da bango ya lafto wani uban ashar yace “Da kudin nawa a kanki kike bin kartin alhazan nan suke yawo dake cikin gari, dama an gaya min ban yarda ba sai gashi yau na gani da idona, idan baki fada min waye shi ba al-qur’an sai na sumar da ke yau….” Yana fadin haka ya kara kai mata hauri ya shakota, ihu kawai jiddah take, Hansai da jikinta ya dau rawa tace “Ji mana Iliya, wllh wllh wani abokin uban gidan babansu ne jin xata yi aure ya tafi yi mata siyayya ya bada gudunmawarsa….” Wani wawan mari xai kai mata ta kauce da sauri ta bar wajen jikinta na rawa, kana ganinsa kasan a buge yake, Bibalo dai ta d’an windan dakinsu take leko su taki yarda ta fito bayan ta sakale dakin, Jiddah sai kichiniyar kwace kanta take amma ta kasa don ba rikon wasa yyi mata ba, Hansai ta nufi can bakin murhu jiki na rawa tace “Ka saurareni Iliya kada ka kashe min ita, wllh nace maka abokin wanda babansu yyi ma aiki ne a lkcn da yake raye, Jiddah ai ba haka take ba, jiddah kamilalla ce…” Sake Jiddah yayi ya juya yana kallon Hansai ya nufeta yana huci, wani ihu ta kwala tana cewa “Makota ku kawo mana dauki kar ya kashe mu….” Wani wawan naushi ya sauke mata a baki, tuni jiddah tayi waje a guje, daya daga abokan Iliya yace “Kai Iliya ta fice fahhh” iliya ya juya da sauri yace “Ku bi taaa” Duk suka fita da gudu, Iliya ya bi bayansu yana cewa daga nan kawai a kai min ita shagona, bikin banxa bikin hofi abinda har sadaki na biya naira duba sha uku, tinkiyar babata fa na dauke na siyar ko sani bata yi ba na biya sadakin, kawai a kai min amaryata…” Hansai dai tunda naushi ya sauka bakinta da ta fada cikin jerin bakaken tukwanen awaranta bata sake motsi ba sai ‘yan idanuwa…. Jiddah na fita dama ta bayan layi ta xaga xuwa windon Iyah, a hankali ta dinga bubbuga windon jikinta na rawa tace “Iyah ni ce ki bude” Iyah tace “Aa ba ruwana an min iyaka da ke, ni da kika sa Hansai ta kusa cinna ma gidana wuta….” Wani ihu Jiddah ta fasa ganin Salmanu daya daga abokan Iliya, ya fixgo hannunta yace “Iliya gata na gano ta” Sai ga Iliya da gudu tare da Surajo, Iyah sai xare ido take jin ihun da jiddah ke yi, a haka Iliya ya ja ta xuwa adai daitan Surajo suka sa ta tsakiya Surajo ya hau adaidaitan ya tada, Iliya ya fiddo wukar aljihunsa yana nuna mata da jajayen idanuwansa yace “Al-qur’an idan baki rufan baki ba xan da6a maki wukar nan kowa ya huta” Tsit tayi jikinta na rawa hawaye na sauka idonta, can karshen kwalta suka kai ta, wani kuturun uncompleted house da Surajo ke ginawa, sbda rashin wajen kwana yake kwana a haka, Salmanu yace “Shikenan sai ku tare nan daren yau kafin gobe da safe Hansai taje tayi mata jere a shagon naka” Iliya yayi wani dariya ya sauka daga adaidaitan yana kallon Jiddah da ko kukan ta kasa sbda fargaba da shock, ya daure fuska yana kallonta da jajayen idonsa yace “Sauka mu shiga Amaryata ta kaina” Da kyar ta sauko daga adaidaitan ya tisa keyarta har cikin gidan wanda duk dogayen ciyayi ne, Surajo yace “To ko ‘yar kifi da ruwan leda ba a siya mata ba ai” Iliya yace “Ai akwai wasu daren masu xuwa da yawa bayan wannan, idan bata ci yau ba xata ci gobe” Surajo yace “Da akwai lemo daya ma da na siyo da rana ban sha ba sai ka bata ta sha kawai” Dariya duk suka dinga kyalkyalewa da, Can jikin bango jiddah ta rakube kusa da yar katifar dake kwance a dakin da wani karamin fitila da bbu hasken kirki, ko siminti bbu a kasa, banda warin ta6a da wiwi bbu abinda dakin ke yi, ta runtse ido tana jin abubuwan kamar a mafarki, sallama su Surajo suka yi ma iliya suka fita dakin suna dariya suka yi masa sai da safe, Ya mike ya kulle kofar ya dawo ya xauna ya fiddo kwalin ta6arsa ya kunna ya fara xuka yana kallon Jiddah da ta takure ko ina na jikinta na rawa, yyi kasa da murya yace “Kiyi hakuri amaryata cikin bacin rai na bubbuge ki, raina ne ya baci ba kadan ba, kinsan idan raina ya baci bana ganin komai idona rufewa yake, har mutum ina iya kashewa, yo sau nawa ma aka yi hakan, kawai garbati ya ce min kusan kullum sai an xo an tafi dake an dawo a katuwar mota…. Shi ma shegen dake tafiya dake a motar ya ci sa’a bamu hadu ba wllh” Ita dai Jiddah bata ce komai ba jikinta sai bari yake, ya mike ya dawo kusa da ita ya xauna yana xukan hayakinsa yana murmushi ya rungumota kusa da shi, ta runtse ido xuciyarta na bugawa da sauri sauri, yace “Inji dai baki jin yunwa ko Amaryata?” Ta girgixa masa kai da sauri, ko kallonsa bata son yi kar ta saki ihun da take hadiyewa, ya wurgar da guntun taban hannunsa ya mike ya fara cire kayan jikinsa, Abuturrab ne ya fado mata, hawaye me xafi ya fara silalowa idonta, Bata san lkcn da ta fasa wani ihu a mugun tsorace ba ta rufe fuskarta da gwiwanta… Ya hade rai ya buga mata dundu a baya yace “Kee, ki kiyayeni fa, so kike ayi tunanin fyade xan maki bayan ke halaliya ta ce, dubu sha uku na biya jiya jiyan nan, har yanxu Babata bata san yanda aka yi da tinkiyarta ba, shine xaki kawo min iskanci, to idan xaki saki jiki ki saki, don muna nan da ke har sai an kira assalatu wllh….” Ta kallesa cikin dakiya amma muryarta na rawa tace “Fitsari xan yi” yyi murmushi yace “To ko ke fa, amaryata, ai gwara kawai ki saki jikin ki” Ya mike ya yace “Mu je in raka ki” Tashi yyi ya dagota xai cire Hijab din jikinta ta rike da sauri cikin rawar murya tace “Aa wllh sanyi nake ji” Bai saurareta ba ya cire Hijab din ya jefar kan gado ya nufi kofa ya bude yace “Mu je kiyi fitsarin” Ta bi sa da sauri jikinta na rawa, wani lungu ya nuna mata a jikin gidan, tun bata kai nan ba take jin zarni na tashi a wajen, yace “Kije kiyi ki dawo ki sha lemo kinji amarya” Ta gyada masa kai ta nufi wajen, komawa ciki yyi da sauri ya dau wandonsa ya laluba ciki ya fiddo wani karamin kwalba, sannan ya dau lemon coke dake ajiye a dakin ya bude, ya bude kwalban ya tsiyaya abinda ke ciki cikin lemon sannan ya rufe ya d’an jijjiga lemon ya sha kadan ya ajiye sauran, ya mayar da kwalban aljihunsa yana murmushi yace “Tass xa ki shanye lemon nan” xaunawa yyi gefen katifa yana jiranta, da sauri ya mike kamar wanda ya tuna abu ya nufi waje ya leka yace “Ke Jiddah, har yanxu baki yi fitsarin bane” A wangale ya ga d’an zinc din da aka yi kofa da shi na gidan, ya xaro ido ya fita da gudu yana kwala mata kira, gudu kawai Jiddah take wajajen da bbu kowa babu wasu gidaje sai ciyayi, sai da tayi gudu sosai taga wani me adaidaita ta tsayar da shi jikinta na rawa tace “Don girman Allah ka taimakeni wllh sato ni yayi, don Allah ka rufa min asiri ka taimakeni” Bata jira cewarsa ba ta shige adaidaitan don ya tsaya, shi ma mai adaidaitan duk a tsorace yake ya dinga gudu har suka shigo cikin mutane, har sannan Jiddah waige waige take gabanta na faduwa, sai da suka shigo hayi sosai sannan yace “Daga ina suka dauke ki?” Tace “Can cikin gari” Ya girgixa kai yace “Yanxu ina xa ki?” Shiru tayi don tasan tana komawa gida yanxu Iliya xai iya xuwa can gidan, da sauri tace “Cikin gari xan je don Allah” Dai dai kano road mai adaidaitan ya tsaya yace “To anguwan naku ba shi da sunana ne a cikin garin, ni fa nan ne iyakata?” Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta bude tafin hannunta tana kallon takardan da Abuturrab ya bata daxu, har lkcn takardan na hannunta gam, ta kalli mai adaidaitan cikin sanyin murya tace “Don Allah kana da waya?” Yace “Ehh” tace “Toh ka taimaka ka kira min number nan don Allah” ya amshi takardan ya dau wayarsa ya kwashe lambar sannan yayi dialing, Abuturrab na xaune parlon Abbansa yana masa calculating din order din da Abban nasa yyi daga waje na kayan auren Ramlah wayarsa ya fara ring, Abba ya kallesa ganin ba daukan wayar xai yi ba yace “Pick ur call” hakan yasa Abuturrab ya dau wayar yana kallon number kafin ya daga ya kai kunne, Mai adaidaitan ya mika ma Jiddah wayar ta amsa ta kai kunne, calmly Abuturrab yace “Hello” Hawaye ya silalo idonta tace “Ni ce” Kallon Abbansa dake kallonsa yyi da sauri, sai kuma ya sauke kansa kasa yace “Ohk ina ji” Ta fashe da kuka sosai tace “Iliya ne ya xo ya daukeni wai saboda ya ganni a motarka….” Abuturrab ya dago da sauri yace “Xuwa ina?” Cikin kuka tace “Wai shi ba sai anyi biki ba tunda ya bada sadaki, nufinsa tarewa xan yi” Abuturrab ya saci kallon Abbansa ya rasa abinda xai ce, Abbansa dake lura da shi ya mike ya shiga bedroom dinsa, mikewa yyi da sauri ya nufi kofa ya bude ya fita yace “Kina ina yanxu?” Ta bi inda take da kallo tace “Mai adaidaitan yace min kano road ne” Abuturrab yace “Ba sa wayar” Mika ma mai adaidaitan wayar tayi ta shiga share hawayen da ya ki tsaya mata, Mai adaidaitan yace “Ehh a dai dai wajen muke ma” bayan few seconds mai adaidaitan yace “Toh shkkn xan jira in sha Allah” Daga haka ya katse wayar, Abuturrab ya koma parlon Abbansa, Ganin bai fito ba ya karasa bakin bedroom din yayi masa sallama, Fitowa Abba yyi, Abuturrab yayi kasa da kansa yace “Abba xan d’an je in dawo ynxu, wani abokina ne ya kirani and it’s urgent” Abba yace “Alright sai ka dawo” Juyawa yayi ya fita daga parlon, ya tafi dakinsa ya dau makullin motarsa, jallabiya ne jikinsa ya fita a haka ya shiga motarsa ya bar compound din…..