KWARTON MANYA

KWARTON MANYA

Sosai akayi masu Adda Raliya tarbar mai kyau ,anan kuma suke shaidawa ango zai zo ganin Zainabu yaji koda abun da take buƙata anjima. A haka suka bar gidan ,itako Zainabu ta saki duk ta ƙosa ango yazo ta tijara shi. Bayan mgriba ne aka shaida mata Zuwan ango. Yana zauren gidan don yy prking moton shi acan farkon layi ,don ba hanyar shigowan ta. Anan ne su Nadiya suka sa mata kaya sabo ,harda wani fesheta da turare. Humm ita dai murmushi kawai take tana tunn ta yanda zata fara.

A zauren gidan su ta ga Saif ,don shi yazo sam Habab yace ba inda zai zo, shi kawai jira yake akawota ya fara aikin sa. Kamin tajira jin mai Saif zaice kawai burin ta ta tijara Angon ,a tunanin ta shine Angon nata ,nan ba ko gaisuwa ta faɗa shi da faɗa ta ci masa mutunci tafi minti arba’in tana bala’i ko tsayawa bata yi ,shidai saif baki ya saki yana mmkin masifa irin na Zainabu .tana dira aya ne ta juya tana yin cikin gida cewa yake ” ki tsaya kiji ki saurare Ni ,amma ina tayi ciki abunta tana cewa a zuciyar ta ai na isar da abun da nakeso ,idan kuma ka aure Ni can maka kai ka sani ko me ya biyo baya”.

Kar ku manta da daga wannan page ɗin free page ya ƙare ku biya kuɗin ku Kuji yanda badaƙalar zata kaya tsakanin Zainabu da Habab????


A yau asabar rana ce da kowani ɓangaren ke cikin farin ciki kasantuwar yau ce ranan yinin biki da tarewa….hohoho Zo kuga Sobreen tayi mugun kyau kaman ka ɗauke ka gudu. Bakin ta kuwa yaƙi rufuwa ,duk da Habab yace ba wani events da xaiyi ,amma su sai da sukayi nasu. Ango yasha kyau ƙwarai ,fuskar sa sai fitar da Annuri yake na farin cikin zai fara izayar shi daga yau .

Ɓangaren Zainabu kuwa anyi ta godo da ita tayi wanka ta shirya firr taƙi har sai lokacin da Aka zo Za’a tafi da amarya ne sannan Yaya Nadiya tayi mata don dole ta samu tayi wanka ,sam ba ƙwalliya a Fuskarta ,wanda wani dandatsatstsen lace maroon tasa na cikin akwatin ta….Mayafin babba ne aka ɗaura mata’. Sosai akayi mata nasiha da faɗan akan ta natsu aure ba wasa bane ba. Idon ta ƙarr ba digon hawaye ,don da taga umma na sharar ƙwallar rabuwar su murmushi tayi a zuciyar ta tana cewa” umma ki bar kuka goben nan zaki ga na dawo”.

Komai na Sobreen da Zainabu iri ɗaya akayi ,don Abba yace bai buƙatar komai na iyaye shima uba ne a gare su ,shi zai masu komai. Part ɗaya suke ,sai dai kowa da falon ta bedroom da komai da komai. Tun da su Nadiya suka kai ma Hjy Luba Zainabu take yaɓa masu baƙar mgn ,wanda anan jikin su yy sanyi . Koda suka koma bangaren Zainabu nasiha suka ƙara mata ,kamin ace su fito a maida su gidajen su.

Sobreen taso ta shigo taga Zainabu amma kuma sai ƴan uwa ta da ƙawayen ta suka hanata ,suna ce mata ta rabu da ita ba ayau ba.

Tun Zainabu na ganin ƙarfe 8:30pm nan taga tara shiru ba ango har goma da rabi , wannan yasa miƙewa tana ficewa zuwa falon ta don yunwa takeji ,fridge ta nufa tana buɗe wa ba tsoro ,nan taga lemu kala² wani dariya tayi na shakiyanci n ta ,tana ɗaukan roba biyu haɗi d rufo fridge ɗin tana juyowa don jin motsin shigowar shi… murmushi tayi a sarari ta furta yanxu za’a fara wasan”.

Kalla n ta Habab yayi yana tuno da marin da ta sharara masa , wanda a yanxu sanye take cikin ƙananun kaya tuni ya cire na angoncin….shi kaɗai ya shigo don yace mawa su Saif baya buƙatar kowa yy rakon sa”. Wani irin farr da ido Zainabu tayi na tsiya don ta ɗauka Saif ne ƙanwar lasar da ta tijara ya kasa ce mata uhm’bare uhm’uhm”.

Ware idanun ta tayi tana sauke su akan na Haban da idanun shi ke akan ta ,fuska murtike tamkar mala’ikan zare rai. Wani irin Addu’a taja wanda nikaina bansan me take faɗi ba. Sakin lemun roban tayi a ƙasa tana faɗin na shiga uku na ,Don Allah aljan ka taimake Ni kabar Ni ,yau nake amarya mu kwana da miji na lafiya…kabar nayi zaman Aure…

kallon ta yayi yana tunanin anya wannan tana da hankali ba mahaukaciya bane? Zama yayi yana ƙara murtike fuska ,yana zama akan 2 str. Waye mijin naki Ni Habab? Kar ki ƙara tunanin zama mata a gareni ,na Aureki ne don na azabtar dake , a haka zaki zauna har muddan Rai”. La ilah haila’lhu kai su Abba suka ɗauramun ,dama kaine mijin nawa???

Shknn rayuwata tazo ƙarshe Ni Zainabu, a rasa wanda xa’a ɗauramun sai mai idon yahudawa”. Miƙewa yayi yana jin wani ɗacin mgn nata a zuciyar shi . Jah baya ta hauyi tana rintse idanun sa sai hawaye sharrrr³ don Allah ka rufe idon ka wallahi tsoron su nakeyi , don Allah bana son ganin su wayyoooo Ummana!!!!. Tayi maganan tana haɗuwa da bangon falon. Keee!! Da me ma zan fara maki?? Fara mun tsallan ƙwaɗo a haka ki shiga har bedroom ki dawo”.

Buɗe idanun ta Zainabu tayi ta mance waye lokaci ɗaya ,tana faɗin eiyeee” taɓ ɗijam Ni Zainabu ne xanyi tsallan kwaɗo. Ta ƙare maganan ba tare da ta san ya iso gaban ta ba. Jikin su na gab da haduwa dana juna…don ɗayan su na jiyo numfashin ɗan uwan shi. Manyan idanun shi ya ware akan ta ,wanda nan taga blue ash ɗin sun ƙara turuwa. Wani irin ƙara ta saki da ƙarfi tana faɗin don Allah ka matsa tsoro nakeji wayyoooo sai kawai tayi ƙasa luuuuuu idon ta na rufewaaaa!

Free page ya ƙare ,ƙi biya kudin ki na antaya ki a Paid grp…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10

Leave a Reply

Back to top button