KWARTON MANYA

KWARTON MANYA

Kinga ɗan yau sai dai ƙi kashe uwar ki bani ba”. Sakin icen Asabe tayi tana nufan inda uwar nata tayi warwasss tana ihu”. Dariya Zainabu tasa tana faɗin ” Zainabu ikon Allah ai Ni babu mai niyar cutar dani Allah bai mai da masa da Aniyar sa ba”. Ke sojan banza sojan wofi ,akan shi ne xan gudu na bar gida ,jabbara’uban Sojojin duka duniya ma ,su ɗin mene suɗin banza su da wofi”. Gida Zan koma shima dai² dashi nake wallahi. Nifa ba wai gudun shi nake ba ko tsoron shi aaa ,a bu ɗaya nake tsoro a tare dashi shine Wannan gaɓaran jikin nashi da kuma idon shi su suke firgita Ni”. Ko mawa zanyi wallahi bai Sanni bane ,don da yasan Zainabu kallo na ma baxaiyi ba ,gudun kar nayi masa illah,gida xan koma babu gidan Nadiya da xanje ,don ba shiri nake da ita ba ,kar naje ta nemi rainamun hankali”.

Asabe ne ta ɗago a zafafe tana nufo inda Zainabu take ita ta manta da babin su ma….hannun ta Zainabu ta ɗaga tana wulwulawa Haɗi da cewa ” fawa³ da ƙarfi ta ƙarke na ukun tana sauke shi a fuskar Asabe wanda nan ta tsaga wani irin ihu ,tana duƙawa . Asabe ki bar ta inshaallh zata haɗu da dai dai ita a gaba”. Ziza tayi mgnan da ƙyar”. Asabe ne ta ɗago da fuskar ta da ya kumbura goshin ta yayi tsini,kije wallahi sai kin ga waɗanin ki Abu”. Ni kika kira da Abu??”. Humm inda badon nayi maki cincin a fuska ba ,wallahi da sai kin sani yanxu ma”. Zainabu tayi maganan tana nufan katangan da ta diro tana haurewa haɗi da komawa”.

Umma ne har a lokacin a tsakar gidan sai Hansai da ta fito tana tayata aiki , da ido dai Hansai ta bita saboda tasan wacce Zainabu da tijarar ta . Umma ne ta ɗago tana cewa ” Wai Zainabu lafiya mai kika ɗaukowa kanki ne da zafi haka kike gudu??. Shiru Zainabu tayi tana tunanin kawai sai tace ” Soja take tsoro ,ina ai Zainabu kar ki bada mata mana”. Tayi maganan a zuciyar ta”. Wane kuwa Umma? Ai Zainabu bata tsoron kowa sai Allahn ta”. Humm”. Numfashi Umma ta jah tana saukewa kamin ta cigaba da aikin ta ,tana jirar isowan Malam Auwalu taji lafiya dai. Ɗaki Zainabu ta nufa ,wanda a lokacin har yamma tayi . Shiru tsawon awa tana ciki kana gari ya rufa tana fitowa haɗi da ɗaukar buta don ta ɗauro alwala. A sallahn ta ne tana addu’a ta chinci kanta da cewa ” Allah na roƙeka Allah ka rabani da mai idon yahudawan nan ko a islamiyya neman tsari ake dasu a littafan musulunci. Allah kasa bazan ƙara ganin shi ba a rayuwata”. Shafa addu’ar tayi tana miƙewa ,Umma ko har a lokacin mmki take yau Zainabu ne da Addu’?”. Hummm”. Tuwon dare taci tana komawa haɗi da zama fitar da suka saba da Umma ,amma a yau umma kaɗai ke abunta …..ana kirar isha’i ne Zainabu tayi sallar ta tana nufan gadon Umma da take kwanciya. A daren nan Zainabu ta farka babu iyaka ,saboda mafarkin Habab da tana rintse idon ta takeyi , wanda ta masa suna da mai Idon yahudawa”. Firgicin da ta dingiyi ne Umma ta rungume ta tana ta mata addu’oi ,a haka har subahi”…..sannan bacci mai nauyi yayi gaba da ita”.


Wallahi Allah na rantse!!!! Kai Hajiya Luba wannan rantsuwar fa? Da girman ki kike wannan rantsuwar ta yara ,ko yaro yakeyi ai abun ki masa faɗa ne”. Alh Ahmadu ke maganan cike da murya ta girma yana dakatar da Hjy Luba da rantse² n da takeyi”. Ai to kaji dai mai nace maka ko? Ba zan yarda Habab ya auri wata ɗiya indai ba Sobreen ba, in kuma an matsa sai dai a haɗa duka”. Ai na ɗauka Habab zai so Sobreen ko don irin zafin Son da take mashi ,idan ba’a duba matsayin Sobreen a gare Ni ba,nida Uwar Sobreen fa uwa ne ɗaya uba ɗaya”. Kamin Alh.Ahmadu yayi magana ne Muryar Habab dake zaune a saman carpet ya katse su yana basu amsan da basuyi zato ko tsammani ba”. Abba na amince xan Auri Sobreen da Zainab a haɗa duka”.
Zaka haɗa duka?? Adda Raliya tayi maganan cike da mmki”. Eh Adda Raliya”. Ashirya komai da Yakamata lefe da sauran su ,Abba Don Allah kar A saka lokaci mai tsawo”. Alhmdullh Habab Allah na gode maka ,ashe daraban zanga Habab ina raye yayi hankali da iyalin shi … mshalllaah Raliya ?? . Abba ya kira sunan ta cike da jin daɗin maganan Habab ,wanda shi kanshi na ƙasa babu abun da yake tunani sai irin izayan da zai mawa Yarinyar nan Zainabu yake ta nanata sunan a ƙwaƙwalwar shi , Bai dai ji me suke cewa ba sai tsinkayar Muryar Raliya yayi tana cewa ” inshaallh Abba a gobe xan yanki ticket na tafiya India kaman zamu fi samun kayan lefe masu kyau da ƙawa a can”. To Raliya Allah yayi maku albarka”. Amin Abba”. Ku bamu wuri xanyi magana da Hjy Luba”. A tare suka miƙe hannun ta riƙe dana Habab Suka fice dai dai Abba na kirar Ƙanin shi wanda suke kirar shi da Baba Iblo”. Kallon Sobreen Adda Raliya batayi ba ta wuce ɓangaren Habab ,duk da ranta na mata zafi akan Auren Sobreen amma ɓangare ɗaya yana mata sanyi na yarda da Amincewa Auren Zainabu da Habab yayi”. Zama yayi a Sofa itama ta zauna gyefen shi tana cigaba da Rarrashin ƙanin nata”. Sobreen ce ta kasa haƙuri ta shigo ɗakin jiki a sanyaye don tsoron Adda Raliya take ,kasancewar tasan ta da zafi bata ɗaukar wargi sam”. Kuma tana jin hayaniyar Hjy Luba akan Cewan Bata yarda Habab ya Auri wata ɗiya bayan ita Sobreen ba. Ganin ta shigo yasa Adda Raliya cike da ɗaure fuska ta mau ta miƙe tana shafa kan Habab da cewa ” Ni xan koma ,sai na dawo”. To Adda”. Y bata amsa a miskilanci”. Ficewa yayi tsawon lokaci Sobreen na a tsaye ,kamin ta tako inda yake tana zama gyefen shi ,hannun shi ta riƙe tana wasa da yatsun shi ,Hawaye na bin kuncin ta , amma kallon ta baiyi ba , bata damu ba ,don tasan shi sam bai san ya rarrashe mace ba , bai taɓa don bata tsananin ma ya iya yin hakan”. Miƙewa yayi yana nufar wani ɗan coridour da taga littafai da kayan colouring harda Arch.bord. da ido ta bisa tana hangosa daga inda take zaune”. A hankali taga ya ɗauki cryons da sauran tarkacen sa yana fara zane wanda bata san me yake yi ba.

Shiru tayi tana bin sa da ido har a lokacin idon ta bai bar tsiyar da ƙwallah ba . Ƙwaƙwalwarta ne ya fara tunano mata wasu abu ƙaɗan da suka faru shekara ba….Sunana Habab Ahmad “. Tsitt ajin akayi ciki harda Sobreen da take jin daɗin Zuwan Habab makarantar nasu wacce batayi tsammanin ganin shi ba”. Malamin nasu ne ya tambaye shi mai yake son zama in his future”. Nan Muryar sa ya amsa da cewa ” abun da iyaye na suka ɗaurani akai shi zanyi, Mahaifiyata na son na zama Soja, mahaifina Architect Kuma ko ina ina da ƙwarewa a fannin”.

Ihun ɗaliban ne yasa malamin shima murmusawa yana masa Ubarnin da ya zauna”. Tuni ƴammatan SS 2 suka fara kirar sa da Habab mai kyau”. Tun a wannan Rana ba Sobreen kaɗai ba har da sauran ƴammatan clss ɗin suka fara Son Habab a zuciyar su ,don shi mutun ne mai farin jinin ƴammata da mutane ,a kwana biyu lbrn Habab ya waɗe ilahirin makarantar Topspring Academy school. Buɗe ido Sobreen tayi a hankali tana ƙara hasko hoton abubuwan da suka faru”.

Habab me kake sha a clss uncle Antony ne fah a claass ɗin nan kasan zafin sa kuwa?? . Sai da ya afa ƙwayar hannun sa yana korawa da ruwa kamin ya juya kansa gyefe ,don baya son Sobreen tun da tanuna tana Son shi,ba ita kaɗai ba har ƴammatan ajin masu shishshige masa ,haka xai yarfa su ,wannan kaɗan nema indai bai zagi uwar su da uban su ba”. Kowa na mmikin Haba mai ya kawo shi School ɗin nan na Lagos shida take turkish na Abj. Amma shi yasan dalilin shi ,wanda ba komai bane ba fache ” bayan makarantar Topspring Academy barikin Sojoji ne ,wannan yana ɗaya daga dalilin da yasa Habab Shigowa mkrtn.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Leave a Reply

Back to top button