NOVELSUncategorized
KWARATA 84

???? —— 82
Suwaiba najin haka ta saki wani irin fitsari tare da jan jiki ta matsa kusa da Dikko tana ƙoƙarin riƙe ƙafarshi ya kai mata wani irin halbi saida ta koma baya suuuuuu , ke ni ba’a taɓani duk duniya abinda na tsana kenan wani ya riƙemin jiki
shi yasa ko ina cikin yanayin fushi aka taɓani nake ƙara firgicewa , ku fiddomin zuciyarta nace………………. !
shi yasa ko ina cikin yanayin fushi aka taɓani nake ƙara firgicewa , ku fiddomin zuciyarta nace………………. !
Cikin kuka tace dan darajar Annabin rahma S. A. W kayi haƙuri ka ƙaramin zuwa gobe dan soyayyar da kake ma fiyayyen halitta idan har ban faɗa ba kayi min duk abinda kaga dama , sannan kuma ka tattaromin kaf yaranka duk wanda kasan ya taɓa zama ƙasanka lokacin da kayi rashin lafiya ko baya tare dakai to a nemoshi a taho dashi tunda na kasa faɗar sunansa idan naga fuska zan gane….
Miƙewa Dikko yayi baiyi magana ba ya fice daga wurin , Ashiru ya kalleta yace an daiji ɓitir shegiya munafuka Allah ya ƙara tona muku asiri gobe iwar haka lahira most go dan mai gida zai kashe ki……. Ya nuna yadda Dikko yake faɗa cewa zan kashe ki……..
Sai bayan la’asar Dikko ya dawo , gidan yau shiru ba Jiddah ba Mardiyya Nabeela ma bata nan tunda ta fita bayan na dawo daga asibiti har yanzu bata dawo ba , da sallama ya shigo ɗakina ko inda yake ban kalla ba na ansa naci gaba da kallon wayata da nake ta kiran layin Inna.
Kusa dani ya zauna ya riƙoni jikinshi yana wannan numfashin nashi mai tayar da hankali , kyarma jikina ya farayi nace sakeni , anƙi a sakekinki , cikin hayani nace da Allah ka ƙyaleni ke muguwa daɗi kikeji na taɓaki ga jikinki nan ya nuna , da hayani na ce sakar…. Mmmmmm na ƙarasa saboda haɗuwar bakunanmu wuri ɗaya.
Shiru nayi tare da ƙara riƙeshi , girgiza kaina yayi da yanayin na kalleshi , jiki a mace na saka idona a nashi naci gaba da ansar saƙonshi , saida ya gama luguiguita ni ya cire bakinshi yana cewa me ya haɗaki da ƙawayen Jiddah ? An mata bakijin magana dai ko ? Kwanciya nayi a jikinshi da yanayin kasala nace Ey banajin maganar , ke yarinya zaneki zanyi ki gama ƙaryar rashin kunyar ina dawowa anjima ya ƙarasa maganar yana tashi bayan ya saukeni daga jikinshi , nima sauka nayi daga gadon nabi bayanshi har ɗakinshi.
Juyowa yayi ya kalleni tare da cewa zaki rufe ƙofa ne ? Girgiza kai nayi alamar a, a , tou me ne ne ? Ba komai na faɗa ina ƙoƙarin zama gefen gado , ke ׳ karki zauna koma can ya nunamin gefen madubi , babu wani damuwa na koma na zauna , kayanshi ya fara cirewa yana bani labari wai Suwaiba idan ta bari ya fara ranfa da ita saiya ɓoye halittar ta , wallahi An mata da tausayin matar nan nake amma yanzu na tsaneta ko ganin ta bana san yi shegiya ƙazama…
Zama yayi saman bedsite wai inzo in cire masa takalminshi in samu lada , kallonshi nayi ban tashi ba , taso mana shi yasa matan yare suka more ma matar malam bahaushe da ni mijin bayaraba ne ba’a bari na in cire riga dakai na , za’a ciremin da soyayya ana faɗamin kalamai masu daɗi ana kulawa dani harsai naji kaina ya min girma , ya ƙarasa maganar yana zame takalmin shi ya cire safarshi miƙewa nayi ganin yana kwance belt a tsorace , a , a koma ki zauna ai ba yanzu zan dakeki ba sai anjima , yi zamanki ni wanka zanyi.
Cikin kuka nace kayi haƙuri dan Allah , saida yazo kusa dani ya sumbaci gefen fuskata ya latsa cikina saida na zabura da irin maganata yace aradu bazan haƙura ba me kuka ci ne ? Ya ƙarasa maganar yana tambayata , ni abinci naci , ai nasan abinci kika ci idan akwai saura kawomin yunwa nakeji ,
Miƙewa nayi na fita , bayan Sultana Dikko yabi da kallo a ranshi yace Allah yasa “ya “yana suyi kama da An mata , amma kar suyi rashin jinta , ubangiji ka sake azurtamu da wani rabon mai albarka ka bawa An mata lafiya ni kuma ka bani haƙuri da dangana , ina can ina yawo ni banga irin abin nan da masu ciki keyi ba , ko me tayi ta kwaɗayi data samu cikin Oho , tou amma me yasa Jiddah tace wai An mata tace baza ta aihu dani ba ? Ya taɓa saitin zuciyarshi , murmushi yayi tare da faɗa a bayyane yace ƙarya ne “Yar mata tana san Dikko kuma dole zata so ta haihu dani kodan soyayyar da muke ma junanmu , rigima kenan naga Sultana da baby da farin ciki ya shiga toilet danyin wanka.
Ɗakinshi na dawo da abincin kuma har yanzu bai fito ba , ajiyewa nayi na fice a ɗakin , gaf zan shiga ɗakina ƙanwarshi mai bi mishi ta tareni tayo zugar ƙawayenta saida kowa ya zageni fes a cikinsu sannan ƙanwar tashi ta ansa tare da fara sokamin zagi waini har na isa saboda ni ɗin banza Yaya DK ya daki Aunty Rabiya waye ni bare ubana ɗan caca karuwa da aka saka a wasan caca su waye familynki ? Karuwan banza gaba ɗaya wace ce ke bare kuma ubanki duk cikar faɗin birnin katsina ? Waye ya tsaya miki ya ɗauremiki ƙugu kike iskanci , Dikko dake fitowa yace ni nine na tsaya mata dan hayaniyar su ta fiddoshi daga ɗakinshi jallabiya ce a jikinshi har yanzu jikinshi da sauran lema kuma itama kanta batayi tunanin zata sameshi gida ba , kuma Ashiru yaa fita da motarshi shi yasa ta ɗauka baya nan yaci gaba da cewa kuma itace tasa na daketa kuma kema saina baki kashin bala’e zaki fita gidan nan , ke har kin isa kizo har gidana kiyi ma matata takakkiya ? Kin taɓa ganinta taje cikinku ne ? Matata zaki zaga……. Dan baki da kunya ? Ashe nima zaki iya zagina idan kika samu dama ko ? Ya fara fita yanayinshi yana An mata zaki ga wanda ya tsaya mata ? Tou ni nine na tsaya mata ya nuna kanshi cewa to gani kin ganni ya akayi ne….. ?
Kyarma jikinta ya farayi tace Yaya ….. Daka mata tsawa yayi kafin ta faɗi maganarta yace zanci ubanki kika sake kiran suna na , kayi haƙuri , tou daga yau naji labari ko na sake ganinki gidana saina zaneki bata haƙuri , kallona tayi tare da cewa yi haƙuri cikin ladabi , kallon Dikko nayi ya ɗagamin gira , ba komai na bata ansa , hanya ya nuna musu tare da cewa kuje , da sauri suka gangare babu wanda ya sake magana ko waiwayenmu har suka fita , zo muje ya faɗa tare da wucewa gaba nabi bayanshi.
Har ya gama cin abincin baiyi magana ba bayan ya gama ya ɗauki wayarshi ya fara dube² tare da ɓalle botir in gaban rigarshi ya shafa kanshi da yanayin damuwa kallona yayi sannan ya sake kallon wayar yace da ina da ina kikaje da bana nan ? Dam׳ naji gabana ya faɗi kafin inyi magana harya ƙufule yace bakiji ina miki magana , daburcewa nayi nace naje goruba , daga nan sai ina ya faɗa yana tsareni da ido , ƙyarma muryata ta farayi nace sai ina naje tou ? Ina tambayarki kina tambayata ? Kayi haƙuri , miƙewa yayi yace inyi haƙuri…..? Tou kinma san abinda kika yi kike cewa inyi haƙuri kenan ? Nima miƙewa nayi na fara kuka , koma ki zauna idan kika fita ɗakin nan saina kasheki…………
Karka kasheni Dikko , ke……… Rufemin baki wato saboda kin ɗaukeni mahaukaci shi yasa kikaje wurin Yazeed kai………… Saina kashe ki……….. Da gudu na fita ya biyoni yana ihu ni zaki tona ma asiri saina kashe ki…….. Na kusa shiga ɗakina naga kafin in shiga in rufe ya riƙeni da gudu na hau ƙarfen bene na sulala ƙasa suuuuuu kai…………… Saina kashe ki……… Maimakon ta fita waje a taimaketa sai tayi tunanin a dole nan ciki zata sama ma kanta mafaka wata irin kururuwa yakeyi mai tada hankali yana maimaita saina kasheki………….. Yana wata irin zabura , da gudu ta sake komawa sama ya sake binta har yanzu bai kamata ba saina kashe ki…….. Kawai yake faɗa , irin na ɗazu ta sakeyi amma sai sautsayi ya gitta……
Wani irin ihu Dikko yayi ke……. Karfa ki faɗa ki mutu , na fasa bazan kashe ki ba , An mata ya nufi inda take tafiya zuwa ƙasa dan riƙeta amma kafin ya riƙota takai ƙasa………. Kai…………… Saina kashe kaina zai faɗa ƙasa aka riƙeshi , riƙe kanshi yayi da duka hannayenshi biyu yace kai……… Wai , wai , wai Allahna wayyo………………. Saina kashe kaina………. Wasu suka riƙe Dikko dake wani irin ihu wasu suka tafi wurin Sultana da ko motsi batayi , An mata…………………… Ya faɗa tare da faɗuwa ƙasa somamme.
Nabeela Mardiyya da Jiddah da suka shigo yanzu gaba ɗayansu wurin Dikko suka nufa suna kuka , ita kuma Sultana masu aiki mata ne akanta maza na tsaye kowa yana tunanin abinda yayi zafi har Dikko ya jefota daga saman bene ya kasheta , cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya cika da “yan uwansu Dikko wannan karon har wanda suke Baba ɗaya ba’a bari ba kowa yazo tunda sharri ne ya samu dan duk wanda aka faɗa mishi cewa akeyi Dikko ya jefo matarshi daga saman bene ta mutu , abiyar zaman Momy kuwa cewa takeyi tunda ya kashe shima sai an kashe shi hukuncin wanda ya kashe shima kisa ne , yaro ne yana iskanci ba’a iya hanashi ya zama ɗan ido kar akayi masa magana ya ragu , tou wallahi yadda ya kashe ɗiyar mutane shima sai an kashe shi Allah yasa mun gani da idonmu kuma saina tsaya ma iyayen yarinyar nan shari’a daga nan har a tashi duniya sai na tsaya akan kafafuwana an kashe Dikko tunda ɗa baifi ɗa ba.
“Ya ” Yanta mata tace su ɗauko Sultana , Momy ta kalli Rabiya tace karku bari ta fita da yarinyar can tunda babu wanda yake da tabbacin mutuwarta dan ko bata mutu ba zata iya kashe ta yadda ta shirya lafiyayen sharrinta , gaba ɗaya wurin ya gauraye da hayani har bakajin maganar wani yayin da matar Dady ke cewa sai an tafi da Sultana , Rabiya tace ita a suwa ? Dan taga Dikko yana sume har ta samu bakin magana ai zai dawo , jin zance Rabiya yasa ta kira Dady ta faɗa masa Dikko ya jefo matarshi daga sama ta mutu ,
Salati Dady yayi cikin tashin hankali , babu daɗewa shima ya bayyana a gidan , ga Dikko kwance a dai² inda yaso ya riƙo Sultana aka riƙeshi ya suma , ga Sultana a ƙasa kwance kuma har yanzu ba’a taɓata ba daga yadda ta faɗa haka aka barta , Dady bai fara zuwa wurin Dikko ba wurin Sultana ya tsaya ya kalleta cikin tausayi sannan ya kalli “yan ɗayan ɗakin yace su ɗaukota su Ashiru kuma suka ɗauko Dikko suka fita daga palon aka bar Momy da ” ya “yanta mata “yan rashin kunya masu irin baƙin haƙin halinta……
Fita Momy tayi tana cewa ina za’aje mata da ɗa ? Cikin ɓacin rai Dady yace ashe kina sansa ? Tio Babana ba ɗanki bane ba nawa ne , ga “ya “yanki nan na ɗauki nawa na bar miki naki wa’anda kike so ni ina sansa kuma bana san abinda zai sameshi insha Allah bazai mutu ya barni ba saina mutu na barshi duniya daga haka bai sake magana ba aka sakasu a mota suka fice daga gidan…..
Wannan ranar ta tuno ma Momy da zuwan Suwaiba gidansu , Dikko yana da rigima haka kawai yaje ya ɗauko musu wannan “yar iskar ya tausaya mata amma ita ta saka masa da sakayya mafi muni a rayuwa ta gudu ta barshi da masifa dake neman kaishi ƙiyama babu gaira babu dalili , ya taimaketa amma ta zama silar warwarewar rayuwashi gaba ɗaya kuma ta gudu ta barshi da hauka shi ba mahaukaci ba , jiki a sanyaye ta dawo palo wuri ta samu ta zauna ta zabgaga uban tagumi tana matse hawaye.
Suwaiba kuwa bayan tafiyar Dikko kuka tasha harta gode Allah , bakin gaskiyarta ta kasa faɗin sunan wanda Dikko yake so ta faɗa masa to ya akayi ta kasa faɗa shine tambayar da take ma kanta bayan a zuciyarta tasan sunan , tana wannan tunanin ne Al ‘ Ameen ya bayyana , tana ganinshi ta fara kaine kuma saina faɗa masa , dariya Al ‘ Ameen yayi tare da cewa haba “yar gurgus na kulle zuciyarki bakinki baya iya faɗar Al ‘ Ameen , kuma idan baki sani ba nine na harbeki kika zama gurguwa , abinda ya kawoni wurinki shine fatan sauka lafiya ayi rayuwar lahira lafiya ina nan saina ga bayan mai gida saina kashe shi na kwashe kaf dukiyarshi sai nayi rayuwar duniya mai daɗi nahau manyan motoci in ƙaro mata 3 masu zafi naje duk sauran ƙasashen da bai kaini ba ,
Waye yace maka ina nan ne ? Ni na sani da kaina dan nasan dama bazaki wuce nan ba , ya baki daga nan zuwa gobe mahaukacin banza yana can yana nema na a gari kamar wani lusari baisan ina tare dashi ba , daga wurin mahaifiyarshi nake na sauke zango na a wurinki , naira miliyan biyu aka bani naje na haɗo sammu nine na bashi a banci kuma a lokacin ni ɗaya nake tare dashi a ƙasar London , kuma nine na kashe matarshi har lahira , ni nayi komai kuma nine zan kulle bakin furta zan kashe ki………………. Zan kashe ka……………… Saina kashe ku…………… Saina kashe kaina………… Haba mai gida kayi haƙuri zaka mutu saurin me kake ? Mutuwar fa yana gaf da kai da zaran na haɗa auren nan aka samu haihuwa sai mu kashe ka kaga mun hutar da kai faɗar zaka kashe kanka Al ‘ Ameen zai aika ka zuwa duniyar mutuwa , Hajiya Suwaiba na wuce sauka lafiya zuwa lahira , murmushi yayi tare da ci gaba da cewa zai dawo yana zuwa zaice saina kashe ki………. Haka zai faɗa Al ‘ Ameen baya faɗuwa dan haka sai ya kashe ki kinga na ture wata matsalar aiki ya ragemin yana faɗin haka yayi tafiyarshi yana dariya.
Fashewa da kuka ta ƙarayi cewa Allah zai tona maka asiri babu daɗewa azzalimi maci amana , murmushi Al ‘ Ameen yayi bai juyo ba ya ɗaga kafaɗunshi ????????
ya fice da sauri , kifewa Suwaiba tayi a wurin kuma sunan Al ‘ Ameen yaƙi zuwa a bakinta ,
Tunanin irin halackin da Dikko yayi mata ya dawo kanta , wurin da take taji yana juyawa yayin da zuciyarta tace ta yanka kanta ta rubuta *AL ‘ AMEEN* a jikin bango idan Dikko yazo zai gani , wayyo Allahna , ta goge hawaye tare da komawa ta kwanta a wahalce ta fara tunanin rayuwar baya……………. !!!
Kuyi haƙuri da wannan don Allah , na farko dai banda caji , na biyunsu kuma ina da hidima wanda ba lallai ne gobe zuwa jibi kuji ni ba , amma idan na samu yadda nake so zanyi ko kaɗanne fatan zaku gafarceni…….
27/11/2019 ????????
*JAMILA MUSA…* ????????